UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

After 1 week

Acikin satin dayan,nan Mu”azzam ya gwamgwaji amarcin sa son ransa,kwana uku kawai yayi ya dagamata kafa,tadan kara warkewa,ai shikenan yasamu nayi sai ya dinga tsorata ta dacewa in bata bari anyi ba,shikenan gun bazai warke ba,zai sake rubewa,dama ga karime tamata fadan banda gujema miji dayimai gaddama,Tuni zahirah ta zama yar gari,domin sai Asatin takoma mkranta,wanda har Asma”u sai da tabiyo sahu,Allah yasa uban gayyahn bayanan ankira sa a office ya tafi,ganin yadda zahirah ta chanza cikin kwanaki sai da tayi mamaki ammh sai ta barshi a ciwon datayi ne,batawani dade ba tatafi daman Direba,yakawota,da ya dawo tafadamai zuwan Asma”un kara kwabanta yayi data rike sirrinta karta je tana bankalawa,jinsa kawai takeyi batasan me ya mu”axxam ya maidata ba.

Ko malam haruna hutu yallabai ya bashi na sati daya kafin nan yagama angwancewansa,Ummi kuwa Tuni sun manta da ita,tun tana kiransa awaya kan taji shuru yace zai zo bai zo ba,kullum karya yake yankamata kan aiki ne yayi mai yawa a office bai samun zama in yafita tun safe sai dare yake dawowa alhalin sai yayi kwana uku bai leka ko waje ba,da zahirah taga zakewarsa nayin yawa ta tuna mai da Ummi,daure fuska yayi yana tambayanta Ummi ke aurenta ko shi,ta bashi amsa dashi yace to tabi Umarninsa kawai duk abunda yace tayi to tayi amfanin dashi,aiko tundaga ranar ta tattara Ummi ta watsar ta cigaba da ba Mijinta hadin kai suna marzan juna son ransu kamar zasu cinye kansu saboda soyayyah,tuni mu”azzam yagama koyama zahirah salo salon na tafiyar da da Namiji kuma ta haddaceshi shiyasa kullum take kara rikitashi,ga Su karime su abun yayi musu dadi,suma suna bata gudummuwa ta Fanni kayan Fruit haka zasu yayyakamata sukawo mata taci,duk don jin dadin ogansu.

koda takoma mkranta babu Abunda ya chanza,zani don yanzu da kanshi yake zuwa daukanta bai yarda ma yakara tura ushe ba,sai sun dawo gida,ya gama Rumgumen rungume,nasa,in anci sa”a ya tsaya nan ranar kuwa da yakejin tsiya a tsumduma kogin ma”aurata,kafin kace me dukkansu sunyi kiba sun chanza kowanne kwanciyar hankali na ratsashi kamar basu da wani damuwa.

Sati biyu cif cif da tafiyan Ummi Ranar tadawo kwatsam,wanda ko Mu’azzam din baisani ba,don shi yakai zahirah mkranta,daganan Ushe ya wuce dashi gun aiki,rabonshi da waya da Ummi kwana uku,kenan Tun ranar data kirasa kan yaturomata Ushe yazo yatafi da ita ya lankayamata karyan Basu samun,zama shida Ushen tabari weeked,shiko bayason Ummi tadawo ne ta katsemai jin dadi harga Allah,ashe tace kaci kaniyarka Deraban Hajiya yadawo da ita har gida,Su kansu su karime sunji ba dadi dawowar hajiya don sunsan shikenan Rayuwar zahirah data yallabai ta shiga takura.

Happy sallah to all Muslim ummah,Da fatan anyi sallah lafiya,to Allah maimaitama Amin

One luv janaf fans.❤

Ana tare.????
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

  *Alkalamin:JANAF*
  *Wattpad:Janafnancy*

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Kuyi hakuri,inata samun complain dinku kan wasu groups yanzu nadaina Musu posting to am srry to say nima yanzu bani nake posting ba,sakamakon wayata tacika hartafara gogemin abubuwana masu Muhimmanci,kuyi hakuri nasan duk inda masoyan Janaf suke UWAR MIJINA Zai iskeku duk inda kuke,nagode Son Kauna wanda baya karewa????????

Hussaini 80k wannan page din nakane,kayi yarda kakeso dashi..Alkhairinka gareni ya wuce baki ya furta,Allah yabiyaka da Sakamako mai kyau,Janaf tana matukar girmamaka

      *NO 19*

Koda Ummi tadawo kamar wacce akama mutuwa fuskarta babu fara”a ko kadan saboda achan zaria sun sha daga da hajiya kan mu”azzam saboda tace zata fara nema masa aure,aiko hajiya tahau tsiya tana fadin”Auren me kuma suhaima? banda wanda yayi,ina ganin kamar kinyi hankali ashe lambo kikayi’,nan fa tashiga mata fada kaca kaca tayi mata kuma tace ta neman mai aure Tagani, tabarima ya Sauke Nauyin dake kansa na Auren dayayi na farkon Tukun kafin tafara Tunanin Auro masa wata.

Ummi bata iya musama hajiya shiyasa,ga haushin Abunda mu”azzam yayi mata,baita taba fifita aikinsa akanta ba, ada komai yake datace tana son abu yake yankesa yayi mata,ammh sai gashi common ya aiko adauketa ya gagara sai Da Shureim yatashi direbanshi ya kawota,abun yamata ciwo matuka kuma da Haushin abun tadawo tayi alqawarin yau ba sai gobe ba sai ta tsare mu”azzam taji dalilin wannan sabon halin daya fito dashi.

Koda aka tashi su Zahirah yau ago da kansa baije dauko ta ba,sai ya tura Ushe ya daukota,itama ganin Ushe sai tashaka,wai don me Mu”azzam bai zo daukanta ba,kuma alhalin da zasu rabu da safe baice mata bazai samu zuwa ba,ranta abace suka dawo gida,cikin takunta na sanyi tayi sallama falon Kafadanta rataye da jakan mkrantarta,bata lura da Ummi dake zaune,kan kujera ba,tasaka kai zata wuce dakinta sai ji tayi an dakamata tsawa dacewa”Ke..Ke…Ke…”Ummi tafada tana mikewa saboda mamaki.

Saurin cin burki zahirah tayi lokaci daya gabanta na amsaa,Ummi fa takejin muryanta innalillahi wa”inna alaihirraju”un tafada kafin ta waigo jikinta na rawa,sakin baki Ummi tayi tana kallon yarinyar daga Sama har kasa,saboda mamakin yadda dan Tafiyan datayi yarinyar ta chanzamata,da hannu ta ya fito ta tana fadin”Zo nan maras kunya,zanyi mganinki yanzu basai anjuma ba”Tafada tana gyara tsayuwarta.

Jikin zahirah na rawa tafara takawa ga Ummi tana kamkame jikinta ta iso gabda ita ta tsaya tana fadin”Don Allah Ummi kiyi hakur…Gam kake ji Ummi tasaka bayan hannunta ta make mata baki tana fadin”Hakurin Ubanki..”Nace hakurin Ubanki,wato kinfa ra wayewa saboda kin shiga mkranta,in Ubanki ubarkane zaune,ko Uwarki Fadi data mutu zaki wuce baki gaishesu ba?”Tafada tana dakamata tsawa,tuni hawaye suka fara zuboma zahirah ta saka hannu tadafe inda Ummi tadaketa sai ga jini tuni bakin ko ya kumbura,zubewa tayi akasa tana fadin cikin kuka”A.a ki..Yi..Ha..Kuri..”Tafada tana kame bakinta kada takara shan Duka,hararanta Ummi tayi tana fadin”Bazan hakura ba,nace bazan hakura,shegiya mai kama da mayu,kin bi kin takura rayuwata,wlh ko kaunar ganinki banayi ammh dayake ke mayyace kinki ki tafi ki barmin gidan dana ko na shakata”Ummi tafada ranta na suya da kafa ta haureta bayan ta zubamata dumdu abaya tace”Bacemin dagani munafuka mai kama da shegiyar uwarta”Da Sauri Zahirah ta mike jikinta na rawa tana kuka ta shige daki Ummi ta rakata da tsaki “Mtseww…Daga dawowata nafara cin karo da bakin ciki kai Allah ya isa fadi da shettima wlh bazan taba yafe muku ba”tafada lokaci daya tana goge hawayen daya digomata,fasa komawa tayi ma ta zauna,sai kawai tahaura sama itama tana kukan,su karime dake labe sukace”Kai hajiya wlh dakin hutama kanki da wannan bakin rikon,ko kema zaki samu kiyi kwanciyar hankali,haba abu kamar cin kwan makauniya,karime tafada cike da takaichi,su lami ma haka sukaita fadan albarkacin bakinsu.

Koda zahirah ta shiga daki kukanta tasha ma”ishi kafin tashare hawayenta tunda babu mai lallashinta,kayan mkrantar ta cire ta sanya na gida tiolet tafada tayi alwala tazo tayi sallar daganan kwanciya tayi tana sakan zucci kafin barci yayi awon gaba da ita.

Bata farka ba sai la”asar sallah kawai tayi ta sanya hijabi ta kwaso littafinta tafito zuwa haraban gidan zuwa wajen karatu,ko abincin ranarta bataci ba saboda bacin rai,shikanshi malamin yaga chanji don yau karatun nasu ma baiyi tsawo ba suka tashi saboda ya lura da yanayinta,suna tashi takoma daki kosu karime basuji duriyanta ba kwata kwata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button