UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Cikin sanyin jiki da Nadama mai karfi Moodu yabi bayan Shettima domin Daman yasan za”a Rina..Yana shiga ba abunda yafi firgitasa sai ganin da yayi ma mahaifinsu wato zannah moodu kwance baya da lafiya Shettima na kokarin Tadashi zai bashi magani moodu na kokarin karisawa shettima yadakamai tsawa kan basa bukatarsa yakoma inda ya fito..Jin haka yasa zannah moodu bude ido yana bin Shettima da kallo kan yace cikin ciwo”Shettima kai da wanene'”Tsuramishi Ido Shettima yayi kan yakada kai yace”bakowa Baffa”Jin haka yasa moodu saurin karisawa gaban zannah yayi kneel down yace”nine Baffa..Nine Moodun ka nine nadawo”Jin haka yasa zannah kokarin tashi yana washe baki cikin farinciki yake furta”Moodu kai ne da gaske”shima moodun cikin murna yakama zannah yana jaddadamai dacewa shine,nan da nan zannah yahau hawaye yana fadin”Allah sarki Ummu kursum yau gaki baki da Rai ga moodunki yadawo cikin koshin lafiya”jin haka yasa Moodu ya firgicewa yakalli shettima cikin Rudewa yace”,in…In..Inna ta rasu? yafada kamar yana kwaikwayon mgana, juyamaSa baya shettima yayi kan yafara da cewa.

      
   Inna Tarasu da sunanka abakinta moodu,Tunda katafi daidai da rana daya inna bata taba fashin ambatonka ba,tunbayan Tafiyanka da shekara uku muka daina jin labarinka mallamin naku na mkrantar wanda da taimakonsa ka tafi ance yakoma garinsu da zama wato ghana saboda damuwa nida Baffa har ghana mukaje ammh sai muka tarar Da Allah yamai rasuwa kuma kasani shikadai ne yasan inda kake har ake samun labarinka agunshi..Wannan lbrin shi yadada tayarmana da hankali  tunda inna taji lbri shikenan bata kara lafiya ba tun baffa na bata hakuri kan zaka dawo insha Allahu har shima yagaza  saboda shuru  baka ba lbarinka gashi muna cikin halin rayuwa balle aje chan abincika mana kai,inna sai da ta shekara tana jinya hawan jini ya kwantar da ita kafin Allah ya mata rasuwa..Tabar duniya da begen ganinka ..Hakika munji mutuwan inna mussamman Baffa da fadi ,wacce tarame ta lalace tafita hayyacinta ashe mutuwan inna tadaki baffa duka duka kwana bakwai da rasuwarta shima yafita sai daukosa akayi yafadi abubuwa sukamana yawa kiwon damuke komai yafara karewa halin rayuwa yafara tsannata agaremu

    awannan Halin ne nayi Aure itakuwa Fadi tana gidan mijinta Allah bai taba bata haihuwa ba..Gwanin irin shekarun da kadiba baka dawo ba  yasa muka fara cire rai da kai ammh baffa kullum zencenka yake Mukuma mu ganin kana chan lafiyanka kalau kadai samu Abun duniya ne ka manta damu mukuma muna iya bakin kokari akanshi ammh baya gani ganin mun damu shiyasa baffa yarage ambatonka ammh mu munsani aransa bazai taba mantawa dakai ba..Shekarun baffa biyu kenan cikin halin ciwo Agidan munshafe shafinka munbarka amtsayin matacce ne Ashe kana  nan da Ranka moodu cikin koshin lafiya da wadatan arziki ka manta da tushenka da Asalinka ballatana iyayanka

Shettima yakarishe hawaye suna kwaranya bisa kuncinsa harda shessheka Baffa ma dake kwance kukan yake..Moodu dayayi zaman yan bori akasa yadora hannu akai yasaki wani irin kuka mai ban tsausayi yana girgixa kaI..Hawaye shettima ya share kan ya waigo yace “Ka fice kakoma inda ka fito moodu munsaba rayuwar baka yanzu ma zamu kareshe rayuwar mu baka..Bamu bukatar ka moodu kafice mana daga gida”Yafada cikin tsawa yana nuna masa kofa.

Khamis Da suhaima dake tsaye gefe tsausayi ya cikasu suka kalli juna lokaci daya Da suhaima wacce tsoro ya shigeta duk da ba jin me ake cewa tayi ba..Ganin haka yasa khamis karisa ya dafa shettima yana fadin”Kar kayi haka dan”uwa ka saurareshi kaji dalilinsa mana”Khamis yafada cikin hausan sa daya koya gun moodu wacce bata fita da kyau..Dagowa shettima yayi yana kallon khamis sai alokacin ma ya gansa ya budi baki zaiyi mgana idonsa ya sauka kan Suhaima wacce taketa wiki wiki da ido..Cikin dakewa Shettima yace'”Moodu wayan nan Fa daga ina'”Yafada yana mai wani kallo..”Moodu yadago kansa idanunsa sunkoma jawur yakalli baffa dake kwance yana kallonsa kafin ya juya ya kalli shettima daya tsareshi da ido yace cikin shakakkiyan murya”Khamis abokina ne tare mukayi karatunmu dashi amadina..”sai yayi shuru Nuna Suhaima Shettima yayi kafin yace”Ita wannan fa”Kallonta Moodu yaga yadda ta tsorata taja baya idonta ya ciko dakwallah..Dauke kai yayi kafin yace” MATATACE….! dai dai lokacin Da”akA bude labule Fadi ta bayyana cikin dakin tana kuka tace”Matarka moodu..Au harma Aure kayi achan kafin kadawo ko..Mu muna nan muna rayuwa cikin kunci saboda rashinka..To wlh baka isa ba sai dai kabarmana gidan mun barma duniya kai hade da wa”inda suka maka walicci auren”Tafada tana fashewa da kuka.

Comment
Share
Vote

#intelligent writer’s#
#Uwar mijina..!!#
#JANAFI#

 INTELLIGENT WRITERS ASSO

    ???? UWAR MIJINAH..????
          (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)

      ALKALAMIN:JANAF????
      WATTPAD:JANAFNANCY

Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF

NO.4

Kasani cewa himma da hakuri da dogaro ga Allah,Sune ginshikin samun Nasara A rayuwa..Assalamu Alaikum janaf

NOT EDITED

“”””””Moodu bai damu da yarda suke cemai yafice yabasu guri ba..,Illa fara labarta musu lbrin Abunda yafaru Tunbayan Barinsa gida da Aurensa da Suhaima har zuwa yau dinan yakareshe da cewa”Ku yarda dani Wlh ko da kwana daya bantaba mancewa daku ba kuna raina..Aurena da Suhaima kuma haka Allah ya kaddaramin bani da yarda zanyi,kuyiwa girman Allah kuyafeman dan”uwanku”Yafada lokaci daya shima ya kice da kuka.

Ammh ina Shettima da Fadi basu tsaya sauraransa ba illa ma suna kara Umartansa daya bar musu gida basu bukatarsa ahalin yanzu.

    “”moodu kukan yake kuka maicin rai da shesshekan zuciya Shettima kuwa Da fadi mganganu suketa jefan dan”uwansu dashi kamar basusan daga inda yafito suna kuma cewa yafita yabarmusu gida..

  Tuni Suhaima ta rude duk da batajin yaren dasuke fadi ammh ganin yadda moodu ke kuka kuma shikanshi khamis din talura da yadda hankalinsa ke tashe cikin harshen larabci take tambayanshi meke faruwa? kan yasamu zarafin bata amsa Fadi ta bankamata harara lokaci daya dacewa”Shegiya mara Asali”Wanda sai da moodu ya tsaigata da kukan dayake yadago yana kallonta..Khamis kuwa yaji kalman ammah bai fahimci ma”anarta ba tukun tunda hausan daya iya gurin moodu bata da wani yawa.

  Suhaima bata saba ganin tashin hankali ba balle dataga yadda fadi ke hararanta sai ta rude tanufi moodu cikin tashin hankali tana jansa tana mgana cikin harshen larabci wai yatashi yatafi..Shi yakara bakantama Shettima da fadi rai suka umarci moodu yayi gaggawan barin musu gida basu bukatarsa..Khamis yana ta kokarin basu hakuri ammh sunki sauraransa..Yakura kuwa na kofar dakin tana sharan hawaye domin suhaima ce da moodu ke bata tsausayi.

  Zannah moodu ne ya tsawatar yana daga kwance cikin wani hali da karfi hali yace”Haba shettima Dan”uwanku ne fa moodu wanda kuka fito ciki daya…Nasani moodu bazai barmu haka kurum ba ku yarda da dalilinsa kubarsa yazauna cikin yan”uwansa na rokeku”Yafada tari ya sarkeshi moodu ne yayi saurin isa kusa dashi ya tarairayosa ya aza kansa bisa cinyarsa shettima ya dauko ruwa yana basa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button