UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dedicated to my Childhood friend FADILAT FALALU MASKA…Tanque bby Sakallahu fiijannah
*NO 23*
Daida lokacin kuma zahirah ta sheme akasa hannunta bisa cikinta tana salati da karfi,Cikin wani irin Rudewa mu”azzam yayi kan Ummi yana jijjagata ammh hankalinsa na kan zahirah datake mukurkusun ciwo.
Su karime ne suka isa ga Zahirah suna riketa suna jera mata sannu,Mu”azzam rumgume Ummi yayi yana kiran sunanta ammh ina ko Numfashi batayi Uwani ne tayi Dabaran Bude Fridge ta dauko Ruwa mai sanyi ta mikama mu”azzam tana fadin”zuba mata wannan yallabai, inaga fa Zahirah Nakuda ce”Tafada hankalinta tashe,cikin wani yanayi Mu”azzam ya shafama Ummi Ruwa Afuskar hau sau biyu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana maida Numfashi daya da daya.
Idonta ta fara budewa taci karo da mu”azzam yana fadin”Plz Ummi…”Yafada kamar zaiyi kuka,Da hanzari ta dafe kanta lokacin da kalaman yarinyar ke mata gizo a kunnenta,Ture mu”azzam tayi da karfi kan tayi nasaran mikewa jirin na neman kara gada ita ya mike da Sauri zai tarota tace cikin karaji”kar ka kuskura ka tabani Ibrahim…”Tafada wasu hawaye masu dumi suna binta. kallonsa take cikin rashin hayyaci,idanunta sunchanza kala sunyi jawur kamar garwashi,lokaci guda ta maida idanunta inda zahirah ke mukurkusu,su karime na rike da ita suna mata sannu,kuka kawai takeyi tana salati.
Kallonta ta dawo kan mu”azzam wanda ke tsaye kamar wani tsohon munafuki,Mirmshi tayi mai ciwo kafin tace”Ni Suhaima,ni Suhaima,ni Mu”azzam kaci amanata ka sabama alqawari, kayi ma diyar wa”inda sukayi sanadiyar rugujewar Farinciki cikina,ka na so dole sai na hada zuru”a dasu ko..”? tafada tana kallonsa Rausayar dakai yayi ya bude baki zaiyi magana ta katseshi da cewa’Karka kuskura kayi min mgana Ibrahim kagama min komai naga sakayyar daukan cikinka danayi har na tsawon wattani tara,nazo na haifeka nasha wahalan Shayar dakai nasha wahalan Rainonka saboda kai nasha kwana da yunwa nayi fadi tashi na rayuwa don duk kai kasamu rayuwa mai inganci,yau burina ya cika kazama wani abu ibrahim ashe da abunda zaka sakamin kenan…”Tafada hawaye suna mata ambaliya.
Jikin mu”azzam na rawa ya durkushe bisa gwiwowinsa agaban Ummi idanunsa sunkada sunyi jawur shima jijiyoyinsa kansa sun mike radau kamar wanda wani cuta ta kama,gabadaya miyan bakinsa ya kafe yarasa mafita lokaci daya abubuwa sun taru sun mai yawa ya bude baki zaiyi mgana kenan karime tace”yallabai,hajiya ku taimaka akai zahirah Asibiti wlh Nakuda ce,kuma haihuwar Fari kada Asamu mtsala..”Wani sakaran kallo Ummi ta jefa karime dashi kafim ta daka musu tsawa tana fadin”Ku saketa munafukai,ko zata haihu billahil azim baza haifanmin wannan dan iskan cikin acikin gidanan ba,sai dai ta haifeshi cikin gidan Shettima..,kuficemin daga gani banzaye kawai..”Tafada cikin bacin rai tana wuci kamar mahaukaciya.
Gaban mu”azzam yafadu Ras lokaci daya yana kallon Ummi wacce tafara taku zuwa gabanshi daidai lokacin dasu karime suka fice hankalinsu atashe,jikinsu a matukar sanyaye,ga Tsausayin yar baiwar Allah zahirah,ga kuma mamakin Rashin Imanin Ummi,haba ko bata taba haihuwa ba,ita macece balle ma ta haihu tasan zafin Nakuda ammh dayake zuciyarta babu imani ko ajikinta.
Tana takowa zuwa gabansa tace cikin kakkausan murya..” IBRAHIM…” Takirasa cikin dakewa da bacin rai jin kiran nata tuni zuciyarsa ta tsinke don baitabajin muryan Ummi cikin zafi haka ba,baisamu zarafin mgana ba zahirah ta karade falon da Salati tana fadin”innalillahi..Hasbunallahu..Subhannallahu..Ya mu”azzam ka yafemin wlh mutuwa zanyi,ka fadama bahna na ya yafemin,shiko baffa ka fadamai na kasa cikamai burinshi na wanke laifinsu wajen Ummi wanda nayi iya bakin kokarina ammh abu ya ci tura,don Allah ka isar da sakona gun yakura kace itama ta yafemin Allah yayi bazamu gana ba,wayyo bayana zan mutu…..”Tafada cikin muryan kuka tana dafe bayanta,mu”azzam ya kalleta hawaye ya cikomai ido yanason zuwa gunta ammh yana tsoron Ummi wacce take kallon zahirah tana fadin”Ko zaki mutu ba ” anan ba yarinya sai kin koma gaban shettima da sakona bayan ya amsa,in ma zaki mutu ne to alokacin sai nace sai munzo…”Tafada Fuskarta babu ko digon Tsausayi.
Kan Mu”azzam ta maida idonta tana fadin”Yau zan Nuna maka kai ba kowan kowa bane mu”azzam don bakai ka haifi kanka ba,yanzu ba sai anjuma ka saketa yanzu yanzunan…”Tafada cikin bada Umarni
Arazane yadago yana kallonta kamar yadda duk azaban dake addaban zahirah sai da tadago tana kallon Ummi wacce ke tsaye ta rike kugu tana hararan Mu”azzam wanda jikinsa ke mazari ayayinda zuciyarsa ke luguden Tsoro, ya kalli Ummi yana fadi cikin Rawar murya..”Ummi don..Alllah..Ki..yi..hakuri wlh bazan iya sakin..Zahi..”Tas!Tas!ji kake karan mari ta wanke mu”azzam dashi tana huci tace”Wlh ko zaka mutu sai ka saketa ko yanzu na daga maka Nono don ubanka..”Tafada lokaci daya tana watsama mai wani banzan kallo.
Jikinsa na rawa ya rarrafa yakama kafar Ummi yana fadin”Ummi na don Allah kiyiman aikin gafara,ki tsausayama baiwar Allah nan,kibari toh in munkaita asibiti ta haihu koma miye nayi miki daga baya..”jaye kafanta Ummi tayi tana fadin”Ban yarda ba sakarta yanzu..”Tafada cikin bada Umanarni..
Sulalewa yayi ya zauna yana kallon zahirah wacce itama ke kallonsa hawaye na wankemata ido,wani sonta da tsausayinta na tsirgamai Ummi ce tadakamai tsawa da cewa”au bazaka saketa ba,sai na daga maka nonon,kenan kashirya biyana kudin Nonon daka sha kenan..” cikin Sauri Mu”azzam yace”a”a Ummi zanyi zan saketa..”Yafada yana Rintse ido kafin ya furta cikin rawan murya”Na…Sa..Ke…Ki…Sa.Ki…Da..ya..Zahirah…”yafada lokaci daya yaji wani abu ya tsayamai a makogoro yakasa wucewa.
Zahirah dake jin jiki sai da numfashinta ya dauke na wani lokaci kafin ta fashe da kuka,kuka mai tsuma rai,ga Nakuda ga sakin Aure,kai wannan bala”in dame tayi kama,girgiza kai Ummi tayi kan tace”Ai kuma baka isa ba,duka zaka cika shemata mallam,ai daga wannan na bar kara baka dama yaro..”tafada tana gyara tsayuwarta.
Jiyayi duniyar tayi masa kunci Ummi tadakamai tsawa tana fadin”Kazabi ka biyani Nonon nawa Kenan?Tafada tana kallonsa girgixa kai yayi yana kallon zahirah yakara cewa..”Na..Sa..Ke..ki..Sa.Ki…Bi..yu…”Yafada yana durkushewa shima kamar ya saka ihu zahirah kuwa cikinta ne ya harbamata ta rarrafa ta isa ga mu”azzam tana fadin”A”a yaya mu”azzam…'”Tafada kamar zata shide.
Kara dakamai tsawa Ummi tayi tana fadin”Wlh zan kira maka tsinuwa yanzu mu’azzam matukar baka karishema shegiyar yarinyarnan sakinta ba..”Tafada tana hambarinta da kafa Zahirah duk da azaban datakeji haka ta dago tana tana kallon Ummi Kafin tace”kar..Ki..yi…Ha…Ka..Um..mi…”Tafada lokaci daya tana cije baki.
Juya baya Ummi tayi tana fadin..”Allah ya…”a”a Ummi don Allah karki soma don Allah..”yafada cikin karyewan Numfashi Tace “To karisa mata cikon Ukun ta yanzu..”Tafada cikin bada Umarni.
Yana kallon idanun zahirah wanda hawaye suke ambaliya ya bude baki zaiyi mgana Zahirah ta yunkurin ta fado jikinsa tana fadin”a”a..Karka Furta don Allah,karka furta ka haramtama zama na har abada..”Tafada tana kamkamesa Ummi ta daka tsaki zatayi mgana yayi Saurin cewa”Na sake ki saki uku Zahirah ammh wlh badon bani sonki ba,sai don bin Umarnin Mahaifiyata..”yafada yana kamkameta suna kuka dukkansu mai cinrai.