UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wajen awa biyu likitoci suka kwashe da Mu”azzam kafin su fito cikinsu harda Dr.Abduljabar,office kawai yace Shureim ya biyosa,ummi na ganin haka tayi zuruf tabi bayansa kamar wacce akace dama bazata ji ba,suna zuwa office din Shureim ya zauna yana fadin”Dr,ya jikin Dan”uwa na hop dai ba abunda nake zargi bane..ko?”

Yafada yana kallonsa,jinjina kai Dr Abduljabar yayi kafin yace"Nayi matukar mamakin yadda Ciwon zuciya yakama brr,mu"azzam lokaci daya,wani irin tashin hankali ne ya gani ko ya faru dashi,wanda yayi sanadiyar taba masa zuciya haka..? dafe kai Shureim yayi yana fadin"hasbunallahi wa"ni imal wakil..."Ummi kuwa dake gefe ta dora hannu kai tana fadin"menaji kuna cewa,Son din nawa ne yakamu da ciwon zuciya,na shiga uku ni Suhaima tsakani na da Shettima Allah ya isa bazan taba yafemai ba..' Tafada tana kuka ko kallonta Shureim baiyi ba Saboda yadda ta bashi Haushi,kina neman kashe danki da kanki ammh kina sakarci kin kasa ganewa.

  Dr.Abduljabar ne ma ya shiga bata baki,shureim ne ya katseshi da cewa"Dr wht iz d solution now..? Dr Abduljabar yace"Munyi nasaran dawo da Numfashinsa,ammh yanzu yana bukatar jini gaskiya,kuma dole ne aguji tuna mai da abunda zai dinga tadamai da hankali,kuma don Allah abunda yake bukata ko yake son gani to ya kasance yana kusa dashi,gudun tashin ciwonsa.."Rausayar dakai Shureim yayi kafin yace"Abunda zai gani ya kwantar mai da hankali har ya sashi Natsuwa Ummi tayi sanadiyar da yayi mai Nisa na har abada.."yafada kai tsaye yana kuma kallon Ummi,wacce tayi Tsuru tana kallonsa,shiko ko ajikinsa illa mikewa da yayi yabama Dr hannu sukayi musabaha tare da fadamasa suje a dibi jininsa domin shi yana iya bama kowa.

Leda biyu na jini aka diba na shureim aka sakama Mu”azzam wanda ke daki na mussamam babu mai shiga sai likotoci,ko Ummi duk kwakwanta anki barinta shiga sai dai ta lekasa ta jikin glasa din daya ma dakin kwanya,har dare suna Asibitin bai farfado ba,daman Dr Abduljabar yace ana sa ran farfadowansa yau zuwa gobe insha Allahu.

Sai lokacin yaduba wayarsa misseds clls ruturutu,na zulaika dana hajiya yasani dole hankalinsu ya tashi har dare bai dawo ba,haraban asibitin yafita yaje cikin msallacin asibitin yayi sallolin dake kansa,kafin ya samu Natsuwar kiran hajiya,wacce yana labartamata abunda ke faruwa tana zaune ne,sai da tazamo kasa saboda tashin hankali cikin wani yanayi ta Furta”Innalillahi wa’inna Alaihirraju”un…,Ashe suhaima bata da hankali bansani ba,ashe Suhaima haka take bansani ba,ashe bata da wayau bansani ba,sakarya kawai mara tunani,taje ta kashe danta akan gabanta na banza,shettima ko yana asara kadan ne,ita sai tafi kowa kuka da shiga damuwa”Hajiya tafada kamar tama zahirah da mu”azzam din kwallah

Shureim yace”wlh hajiya sai ma kinga yadda dan”uwa yadawo kamar wanda ya shekara yana ciwo..”yafada kamar yayi kuka,hajiya tace”Allah sarki bawan Allah,ya hadu da jarabawar Uwa,Allah ya tashi kafadunsa..,”Shureim ya karba da Amin..Kafin hajiya tace”in ita Suhaimar..? yace”Tana cikin Asibiti tana ta ma mutane koke koke..”Tsaki hajiya taja kan tace”mtseww…Koke koken banzanta,ubanwa zata ma kuka bayan duk abubda ya faru itace sila,sakarya mara wayau,kai gobe ma Kabiru zai kawoni dole nazo nacimata mutumci,kuma saita bar asibitin nan,kada ma ya farka yacikaro da ita zuciyarsa tabuga ya mutu gabadaya..”Shureim dai hakuri yake ba hajiya ammh ta inda take fita dabam ta inda take shiga dabam,sallama sukayi hajiya nakara jadaddamai gobe tana tafe.

Dakyar shureim ya lallaba ummi,suka koma gida don wajen basu bukatar mai jinya suke kula da komai balle shi da ko ganinsa ba”ayi balle tace saboda shi zata zauna,koda suka koma gida yadda Ummi taga rana haka taga dare tayi kuka kamar ranta zai fita,shettima ko da fadi sunsha Tsinuwa harda na bala”i,koda gari ya waye tukan Ma shureim ya tashi tasaka Ushe yakaita chan Asibitin tana ko zuwa aka hanata shiga har kuka tayima Dr Abduljabar kan yabari tashiga,taganshi ammh yahana saboda dokace sai in ya farka,nan ta zauna tana lekensa tana share hawaye.

Karfe goma tayima hajiya baraka acikin asibitin dayake dama tasan Asibitin kai tsaye tazo,Shureim shiyazo yayi mata jagora zuwa wajen da"a ka ijiye mu"azzam,wanda shima bai dade da zuwa ba,Ummi tana ganin hajiya ta fashe da kuka tatashi zata rumgumeta hajiya takauce tana fadin"Karki sake ki tabani,kuka kikeyisuhaima,ai nadauka yadda zuciyarki takekashe da rashin imani bazaki taba kuka  saboda halin da kika jefa danki da kanki ba.."Sororo Ummi tayi tana kallon Hajiya kan tace cikin kuka "Ni kuma yaya..? tafada tana nuna kanta.

Gyada mata kai hajiya tayi kan tace”Kwarai da gaske,ai bandauka haka kika zama mara imani ba da tsausayi,ace ki saka danki ya saki matarsa da tsohon ciki,kuma ki koreta a daren,haba rashin imanin naki Suhaima ya wucema yadda nake tsammani wallh..”Tafada ranta bace,dukewa kawai Ummi tayi tana kuka hajiya ko ta cigaba da cewa”bansan cewa haka sakarcin naki yayi yawa ba sai yau,ke aka cuta daga karshe suke da riba,domin kin saka ya saketa,takoma gida,sun karbi diyansu sun rike sunbarki da halinki,kuma ciki jikinta inta haifeshi,nasu ne ke kuma kinga kin,rasa farincikin danki gashi kwance rai a hannu Allah ,ke baga da”n ba kuma ke baga suruka ba,kuma ke baga jokokinki ba,duk kinyi batan batatatan,kin zabi ki durkushe rayuwarki da hannunki suhaima,wlh Tir girmanki da wayonki bai tsinana miki komai sai ci baya..”Hajiya tafada kwallah na ziraromata.

Ummi kuwa akasa ta zauna tana rusan kuka tana fadin”Na shiga uku ni yaya,taya zaki dinga ganin laifi na,wlh har abada bazan yi nadaman abunda na aikata ba” Tafada tana kuka t Hajiya tace’,Baki shiga uku ba tukunnah,Sai in dan naki ya mutu gabadaya kinga nan saiki lalace gabadaya,kuma nadama bayanzu nake sonkiyi ba Suhaima,sai lokacin Nadamar naki yazo lokacin nake so yi Nadama,”Tafada cikin bacin rai.

 Suna cikin haka ne ,sai ga Dr,Abduljabar ya fito daga dakin da mu"azzam yake yana fadin"Alhamdullilah brr,ya farfado yana ta kiran wasu sunaye bansan wa yake Nufi ba,zaku iya shiga ammh banda dogon hayaniya plz"yafada kamar yana rokonsu,jinjina masa kai Shureim yayi yana fadin"Babu damuwa Dr.Mungode.."Ko gama rufe baki basuyi ba,Ummi tadanna dakin da gudu batare data tsaya jin bayanin likita ba,kallonta kawai sukayi suna kada kai.

Yana zaune akan gadon marasa lafiya,an gama masa karin jinin,tunjiya yanzu ruwa ake karamai saboda rashin babu komai acikinsa,jikinsa babu riga sai dogon bakin wando,fuskarsa ta zurma ya rame sai hancinsa daya fito zuruf dashi kansa na sunkuye Ummi ta fado dakin tana fadin..”my son..”jin muryan Ummi yasashi dagowa yana kallonta,itama shi take kallon tana hawaye ta karisa kusa dashi ta riko hannunsa tana fadin”haba my son,meyasa zakayi haka? don kasaki zahirah shikenan sai akace karshen rayuwarka ne yazo,meyasa nima bazaka min adalci ba ehe mu”azzam…”tafada hawaye na gangaromata.

Runtse ido yayi kafin ya bude ya saka duka hannuwansa ya tallafeta,kafin yasaka yatsunshi yana sharemata hawaye dakyar ya iya fadin”kiyi hakuri Ummi ba laifi na bane..”Abunda kawai ya iya cemata kenan ya sadda kai bisa kafadanta yanajin yadda kirjinsa ke suya,hajiya da shureim dake tsaye suka kariso hajiya na fadin”an ce bayason hayaniya Suhaima wata kuma mganar banzar kike fadamai,tunda dai nasan ba wacce zata kwantar mai da hankali bace”

jin muryansu hajiya yasashi dagowa ganin Shureim yasa shi fadin”Dan”uwa..”yafada yana mika masa hannu,kamawa yayi yana zama agefensa yana masa yajiki,hajiya ma ta gaishesa tana tambayansa ya jiki ya amsa da cewa”Jiki da Sauki hajiyarmu ,yaushe kika zo..’? tabe baki hajiya tayi tana fadin”ban dade da zuwa,nazo ne da takaicin abunda shashashar uwarka ta saka ka aikata..”Tafada tana hararan Ummi.

Mirmishi yayi mai ciwo baice komai ba,baki Ummi tatura batayi mgana ba hajiya tace”ai zuwa maiduguri yakamaki Dole kije kiyo masa bikon matarsa in kina son ganin danki cikin koshin lafiya”Daga mu”azzam har Ummi da kallo sukabi hajiya kafin Ummi taji sai yanzu taji dadin saki ukun data saka yayi mata da yanzu hajiya tasata tayi abunda batayi niyya ba.

Ganin sunyi shuru ne yasa Hajiya fadin’ko bazaki bane…? Mu”azzam ne yayi mgana cikin sanyi da takaichi yace”Hajiya ai zahirah ta haramta gareni..”Yafada cikin wani yanayi yanajin taruwan kwallah a idanunsa, Hajiya taji gabanta yafadi tace”Bangane ta haramta gareka ba,ba saki daya kayi mata ba?..’girgiza kai mu”azzam yayi kafin ya Furta chan kasan makoshi”saki uku ne hajiya..”yafada yana dora kansa akafadan shureim saboda yadda yakejin wani hajijiya na yawo dashi.

Salati hajiya da Shureim,suka saki suna sallallami hajiya kasa mgana ma tayi ,sai kawai ta fashe da kuka tana fadin”wlh Suhaima hakkin danki bazai barki ba,sai ya bibiyeki,da hakkin yar marainiyar Allah wlh sai kin karbi sakamako gurin Allah..”tafada tana share hawaye,Ummi kuwa dukar dakai tayi ko ajikinta murna ma take daya kasance haka,hajiya babu yarda zatayi da ita yanzu.

Cikin Kasala da ciwo mu”azzam yace”Ta haihu jiya,babanta yakirani yake fadamin ranar da ciwon nan zai kwantar dani..”yafada yana yi baya ya kwanta saboda kwallar data cikamai ido gyaramai filon Shureim yayi yana mai sannu,washe baki hajiya tayi ga hawaye tace”Allahu akbar kaji ikon rabba ko,me aka samu.?.”yana daga kwance yace”twins ne mace da Namiji yace..”guda hajiya tasaki tana kallon Ummi tace”Allah na gode maka,duk wanda yakeja da ikon Allah,karshenta rai ya kashe mutum..”tafada kanta tsaye shureim ma baki ya washe yana fadin”congrat dan”uwa..Allah ya rayamana yaranmu ka kamoni fa”yafada yana dafa hannunsa mirmishi kawai mu”azzam yamai baiyi mgana ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button