UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Mganar da zannah yayi shiya dakatar da Shettima da Fadi basu da yarda zasuyi ammh fadi ita tunda tadora ido kan Suhaima taji ta tsaneta saboda itafa harga Allah kanwar mijinta tayima alqawarin yayan nata( Kiji karfin hali)da sun hada ido sai ta bankamata harara.

   Tuni labarin dawowar Moodu tacika gari yan”uwa da abbakan arziki sai tururuwan zuwa ganinsa ake..Anata lbrin yazo da mata balarabiya kowa sai zuwa ganinsa ake shida suhaima masu zuwa don Allah da masu zuwa don gulma..Tuni labari ya yahadu agari ashe moodu ba bacewa yayi ba yana chan yana hutawanshi harda ma balarabiya yazo..Chaichai..Abu yacika gari..kowa da Abunda yake fadi.

   Wuni sukayi da baki shiyasa basu kara wani tattaunawa ba,dare nayi kunyar shettima yasa yabar Suhaima gun yakura shikuma yatafi yakama ma khamis otel yakwana yaso yadawo ammh damuwar dayake ciki tahanasq dawowa kuka reras yayita ma khamis yana bashi hakuri..Koda gari ya waye suka dawo ko mgana shettima baimai ba saboda yatafi ya kwana da khamis..Itakuwa suhaima taga rayuwa domin bayan Tafiyan moodu haka Fadi ta sakata gaba da zagi da cin mutumci duk da batajin metake cewa ammh tasan cewa komeye bamai Dadi bane.

   Sai da yakura tamata mgana itama din bata ragama mata sai da dai tabar gidan aka samu sa”ida..Duk da yakura batajin larabci da hannu taita bawa suhaima hakuri wacce ta kwana kuka sai yanzu taji nadamar yarda da Auren moodu har ta yarda ta biyoshi nigeria ammh ta yanke shawarar khamis zata bi takoma kasarta ta haihu..Yakura ita taita dawainiya Da suhaima taneman mata makwanci takawomata abinci duk da bata mgana sai dai ta kalleta kawai tamata murmishi alamun tagode sosai.


Satin su daya dawowa ammh shikanshi moodun zaman hakuri yake yi da yan”uwan nashi mussaman Fadi wacce bata da hakuri ko kadan gata masifaffa ko agidan Aurenta darajan zannah take ci,Suhaima cikin satin datayi ta fuskanci wani Abu haushi sauyin rayuwa tayi kuka kamar idonta zai fadi saboda takuran fadi..Wacce ke wuni agidan sai dare take komawa,shikanshi moodu baisamu ya kebe da ita saboda shima bai zauna ba suna ta cukun cukun chanjin kudinsa zuwa na nageria,sai da komai ya kamkama ya ciro kudin duka yazo ya zubesu gaban Baffa da Shettima da Fadi ammh sai me sai suka juya baya kan basu bukatar komai da dabayanan wake basu kiri kiri suka ki yarda Yakai Baffa Asibiti Abun Takaichi kuma Shettima ke biyema Fadi yana yarda da shirmenta.

  Lokacin Da khamis yayi shirin komawa Nanfa Suhaima tasaka Danja ita gida zata koma kuka take kamar zata shide,Dakyar khamis ya lallabata ta yarda zata zauna ammh da sharadin zai dawo yadauketa,khamis yayi tabawa moodu baki ganin yadda duk ya shiga tashin hankali kafin tafiyarsa sunyi mganan Da Baffa kuma ya Fahimce sa Shettima kamar wanka akama Asiri.

Sunrabu cikin kewa da kaunar juna..Akan sai wani lokaci,wanda lokacin da har yanzu baiyi ba kenan Domunn  Rabuwar moodu Da khamis Ta har Abada kenan.

  
Saboda gudun mgana yasa Moodu ya yanki barayi nan cikin gidansu yaja sasa nashi shida Suhaima wanda sai da yaja cucekuce kamar basusan inda yafito yarasa wannan Tsana da yan”uwansa suka masa ba,Suhaima tashiga halin Rayuwa gun Yakura ne kadai take samun Dama Dama ammh Fadi tayi mata mugun Tsana wanda ko a idanunta bai boyu ba

  Cikin lokacin moodu yanemi lecturer a Universty of maiduguri kuma suka daukesa ba laifi yasamu Abun Duniya wanda sai dai ya ijiye ko yakaimasu Shettima ba amsa zasuyi ba..Shiko baffa Jiki yayi Nauyi ko mgana bai iyayi..Tun Abun nabawa moodu mamaki haryazo yafara Damunshi Uwa uba ga amanar marainiyar Allah wacce Tarame ta lalace saboda zullumi Tuni Shima yafara ramewa Damuwa suka taru suka sanyamai hawan jini wanda ba wanda yasani sau shi Sai Allah sai Amininsa khamis.

   Ana haka kwatsam Aka wayi gari Da Rasuwar Zannah bukar,wanda mutuwar data girgiza jama”a Dadama,ciki harda moodu wanda sai da kwanta asibiti babban Tashin hankali Shine wajen karban gaisuwan haka Fadi ke kuka tana birgima tana fadar Sunanshi dana matarsa akan susuka kashe musu uba..Abun nan yayi Sanadiyar haifar dawani Nauyi akirjin moodu wanda bai wuce ba har Ranar dayakoma ga Allah

  mutuwar Zannah itace mafarin komai Domin lokacin kuncin Rayuwa tabude musu Suhaima wacce kullum kuka take tamadaina zencen komawa gida domin ganin Shikan Shi zannah baida kwanciyar hankali,Suhaima macece dabata manta alheri komai kankantarsa balle wanda yabatamata lokaci Daya taji ta tsani Fadi Da Shettima wanda bata fatan ko mutuwa tayi su sallaci gawanta..Dafari bata fahimtar bakaken kalaman Da Fadi ke jifanta dashi ammh yau da gobe yasa tafara Fahimtar wasu daga cikin Hausa hartakecin wani Abu daga ciki.

  Tunda Sukayi Aure Sau biyu Tak moodu ya kusanceta..Saboda shikanshi baida kwanciyar Hankali Koyarwan ma dayake don yazama Daolene Kwatsam Shettima yatada ballin Tunda Baffa yarasu to moodu yazo yabar musu gida da karuwa donsu haryanzu basu yarda Aure sukayi ba dauka Sukeyi Abokiyar Shashancinsa ne….

Wannan Shine mafarin komai Daren Da moodu yaji haka bai kwana Duniya ba zuciyarsa ta buga Allah yayi masa Cikawa..Mutuwar data girgiza xuciyoyi uku alokaci daya Shettima,Fadi,da Suhaima wanda ko amafarki basu zata ba. Mutuwar da haryanzu suke kokamata wanda basuda Ranar Dainata ba..Suhaima Sai Da Tayi awa uku asume har Saidai aka kai moodu zuwa gidansa na gaskiya ta farfado..Allahu Akbar duk mai imani yaga Suhaima sai ya zubar mata da kwallah domin Ayanzu bata da wanda zata kallah tace natane..Lokaci daya taji Duk Duniya bazata ta taba yafema Shettima Da Fadi ba don Sune silar mutuwar bango kuma ginshikinta.

S Fadi sun koka na Rashin Dan”uwamsu ammh kash hakan baisa sun Saduda ba anayin bakwai Suka tattara komai na moodu suka rike Suhaaima ko Tsinke basu bata da sunan bata da gadon dan”uwansu..Rayuwa tayima Suhaima kunci babu mai Tsausayamata Sai Yakura,Fadi kuwa kullum tazo zagi da cin mutumci babu wanda batasha tadinga jifanta da mugayen kalamai nacewa ita karuwace koda yake itama ta hanyar da”a ka haifeta kenan..Suhaima tayi kuka kamar idanunta zasu rufe gashi bata da nombar Khamis balle takira bata da kowa sai Allah.

    Tunbayan Rasuwar moodu Suhaima ta fahimci tanada jaririn ciki wanda bayyanansa gareta wani Taimako ne da budi daga Allah moodu yatafi Moodu yadawo..Suhaima tayi farinciki matuka lokaci daya tadorama cikin wani soyayyah wacce bata da karshe..Takudiri niyyar boye cikin domin kauda idonsu Shettima da Fadi,Haka ko akayi daman bafitowa takeyi ba komai adaki take,sai yakura ne ke shigowa dubata tana kaimata abinci Shima aboye,Sai dacikinta yakai wata shidda dayake tana da girman ciki yakura tafara ankarewa dashi lokacin Da Suhaima tafahimci yakura tafahimci Halin datake ciki.

   Ta tsorata harsaida Tsoron ya bayyana Afuskarta ta rike hannu yakura hawaye suna kwaranyomata tace”Kiganni ko duk boyensa danake sai da ya fito kirufamin asiri kada sufadi su Sani wlh zasu iya rabani da shi.kuma yanzu duk duniya shine kadai Sanyi idaniyata”Tafada da hausanta wacce ke chakule da larabci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button