UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Kife kanta Ummi tayi akafadan Ummi tana kuka take fadin”Hajiya zan mutu,wlh mutuwa zanyi,taba kirjina kiji,wlh zan mutu bazan zauna acikin duniyar daba mu”azzam ba,bazan iya ba..”tafada tana dora hannun hajiya bisa kirjinta taji yadda yake harbawa da Sauri da Sauri,rumgumeta
hajiya tayi tana fadin”Bazaki mutu ba Suhaima nafi so kiyi nadamar abunda kika aikata kafin lokaci ya kure miki..”Cikin kuka Suhaima tace”Nayi whl nayi hajiya Nayi Nadamar abubuwan danayita aikatama Mu”azzam hajiya dana sani ban saka ya saki matarsa ba…”

   “”Allah ya rabumu da aikin danasani Ummi ammh bakin alkalami ya rigaya daya bushe,mu”azzam yabarmu,kuma yayi nisa da mu domin na bincika duk inda nake da tsammaninsa babu shi babu dalilinsa..”yafada yana dafe kansa,Shureim kenan wanda shigowarsa kenan,daga hajiya har Ummi an rasa mai lallashin wani Ummi fadi take”Ni dazai dawo wlh zani har maiduguri na roki Shettima gafara Zahirah ma tadawo dakinta,indai zai fasa barina yadawo mu zauna tare ban saba da kowa ba sai shi Shureim shine uwata shine ubana,,shine da”na shine madadin yan”uwa na,wlh rashin mu”azzam tamkar rabani da duk wani jin dadin rayuwata ne..”tafada tana kamkame hajiya,shureim daya jingina da bango fadi yake”Ai shikenan Ummi,komai fa ya kwabe,..”yafada shima kamar yayi kukan.

  Dr.Abduljabar ya shigo shikanshi halin da wannan Family din dasuka zama tamkar yan”uwansa suka shiga ya tabasa,dakyar ya lallaba Ummi yayi mata alluran barci bayan ta rike masa hannu tana fadin”Dr nasan kasan inda mu”azzam yake,kacemai yadawo wlh na tuba nabi Allah,kace mai eh ya dawo zanje na dawo masa matarsa indai hakan shine zaisa ya zauna dani ,wlh kaji na rantse ko yanzu sai naje maiduguri,kai likita ko a kasa ne ma indai Mu”azzam zai dawo gareni zan tafi zani wlh ku tsausayamin ku memomin da’na”Take fada lokacin da alluran tafara aiki ajikinta ta sulale bisa gadon tana Fadin..”Da’na…!…”Da gudu hajiya ta fice tana gujin kuka shureim ko baya ya juya yana shesshekan kuka,Shikanshi Dr.Abduljabar hawayen ya share ta kasan medicated glass din dake idonsa yana gyarama Ummi kwanciyarta,kafin ya kariso kusa da Shuriem yana bubbuga bayansa alaman lallashi,juyowa kawai yayi yafada jikin Dr.Abdujabar yana fadin”I feel Alone Dr.Ya zanyi shikadai ne dan”uwa na,kalli halin da Ummi ke ciki,kalli halin da Hajiya ke ciki i swear to god Mu”azzam shine ginshikin farincikinmu rashashi kuma tamkar rasa walwarmu ce ta har abada…”yafada yana mai sakin kuka.

  Lallashinsa ya shiga yi yana fadin”Kabar kuka zai dawo very soon…Inaji ajikina shima duk inda yake yana cikin halin dakuke ciki,insha Allahu Soon brr zai dawo gida da zarar zuciyarsa tayi sanyi.”Shureim ya dago yana kallonsa idanunsa jawur yace”Babbar illar Dr.Shine bazai kula da kansa ba,zama zaiyi cikin lalura karshe zuciyarsa ta buga ya mutu,inda,baya da kowa,mukuma yabar zukatanmu cikin zullumi da saka rai na har abada..”yafada yana buga kansa da garu saboda yadda zuciyarsa ke amsawa,dakyar Dr.Ya lallashesa suka fito daga dakin yakaisa office dinsa yana basa baki har ya samu natsuwa,koda ya fito ya iske hajiya zaune fuskarta ta kumbura saboda kuka,ga zulaika ma nata fama da yara, itama ta sha kuka,hajiya na ganinsa tace yazo ya tafi da zulaika gida tasamu tayi wanka taci abinci taba yaran nan,ita tana nan,Yayi na”am da batunta ya umarci zulaika data tashi su tafi harda karime hajiya tace su wuce wanda lokacin dare yayi,itakuma hajiya dole dama abarta ta kwana da ummi saboda yanayin yadda take farkawa,shi Ushe tundazu yakoma gida cikin alhini.

Koda Sukadawo gidan ba wanda ya runtsa su lami duk suna falo xaune jugum jugum,inda suka saba sauka nan zulaika tafada tayi wanka tayima yaranta kafin tayi  sallolin da’ake binta ko abinci dasu lami suka kawo mata kadan taci shureim kuwa shashen mu”azzam yashige yana ta kuka dakyar zulaika ta lallabasa tayimai wanka ta shiryasa,dakyar ya yarda yasha tea tabashi paracetamol yakoma ya kwanta domin ciwon kai ne da zazzabi suka rufesa,gefe itama ta kwanta rumgume da yaran tana share kwallah tsausayin mutanen da suka kasance jarumai ammh yau Ranuninsu ya bayyana.


   Wahegari Tun safe mu”azzzam ya fita neman ma kansa mtsaya koda yaje Airport na birnin ikko jirgi daya ne zai tashi da karfe 9:00am na safe kuma zai yada zangon A EGYPT,Cikin ransa yayi kasake yana ayyana Zuwansa garin da baitaba zuwa ba, kawai wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi Kayi rayuwa achan mana,ka manta Abbanka yaje chan,Umminka tayi rayuwa achan Tabbas nima Zan maimata Tarihi zai maimata kansa,Zan isa garin na SUDAN nima in taba rayuwata achan,koba komai garin da Ummi na da Abbana suka fara haduwa ne.

Tuna haka yasashi saurin yanka ma kansa tikiti da sauran chuku chuku abunga ga masu dashi nan da nan komai ya kammallah ko hotel din daya kama bai koma ba,daman daga shi sai yar jakarsa ya fito zama kawai yayi yana jiran tashinsu zuciyarsa ta matsu ya bar kasar Nageria kasar da babu komai cikinta sai kunci.

  9:00am din kuwa jirgin ya tashi ya lula dashi cikin sararin samaniya cikin wani yanayi Mu”azzam ke maimata inda zashi da karfi.. ” SUDAN

Godiya ta mussaman ga masoyana masu bibiyana,Nagode muku sosai ga wadanda suka kirani sukamin sannu da jiki epecially thanks to u my Sisi of life Aisha Alto,da ke my kakus mum khday,my esha,Aisha bello ina godiya,sai my juwairiyyah Rogo,dake my Queen Eshart,and u my Shatutu,ina matukar godiya da kulawanku,Tanque so much my Habibaties

DON’T”FORGET TO COMMENT AND SHARE AND VOTE ME ON WATTPAD JANAFNANCY12,masu bibiyar wanchan account din toh na chanza account mai son kamani ta chan ga user name dina dana chanza..one luv janaf fans

     JameelatOmar
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

   
Wannan shafin ta gaisuwan,Sada ZUMUNTA NE,na marubuta yan”uwanah..✍????

FEEDHOM❤,Khadijat Beebeenmasoya(Uwata),Aysha sada machika,Hafsat Hafnan(Sahibata????),Aisha Alto(my sisi of life),Hauwa s zaria maman uswan(Mommata),Khadijat Candy(Mamata),Billy Abdul(yayata),Sa”adatu Alkali D/Tsafe(Bestyta)????,Ramlart R manga(Real maidambu),Sis Narja”art(Antyna),Beeba muhammed(Bebatina),AminaOmar Fana(Aufana),Fatima Adamu(Mumfdly),Mum kausar(Dotana),Halima Abdullahi(kanwata),Sainah Ummu meenal(Antyna),Mom Afra(Boss me),Ameena Abba(Anty meena),My meeragee,Meemartjj(kanwata),Lasminzy,Fatima Sardauna(Mrs Sardauna),Hauwa”u M U(Smasher),Sa”adatu bintu Abdullahi,Bby maryam,Ummy yusra,miss zahra(Kawata),Teemaswra,Jamila k/Mashi(My Namecy) Sadiya Sidi said(my Sharifiya),Miss Xark(Kishiyata)????,Asmee sani,Chubado muhd(Uwar dakina),hapsy kawar arziki,jabaka writer,kamal no love Sardaunah(gaye nah)????,maman hanan(Deen),maman weedad,Maryam obam,Nusiba uk(Kawata)Raheenat m Abbakar(Yar garinmu),Sameena Aliyu(My samee)Zainab Dahiru wowo,And u makociyar kwarai Fadilat talba,Safiyyah Aliyu wakili,Ummu Abideen, Sis mugirat musa..,Wayyo ni dadi kasheni wlh Kuna da yawa,Dukkanku nayi zaman Amana daku ina rokon Allah aduk inda kuka sanya kafa Allah ya cigaba da dafa muku Amin,ina matukar sonku mazga mazga????Santala santala????Kai dukanku nace muku Bhahoot bhahoot????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button