UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yaji dadin wajen sai gashi har dare ya raba baisani ba,sai daya duba agogon ahannunsa yaga har 12 ta wuce kafin ya yunkura ya tashi,da kafansa yasake komawa cikin Hotel din,sallolinsa dasuka kufcemai ya fara ramawa,kafin ya jawo kan wayar dake cikin Dakin Hotel ya daddanna wasu lambobi magana yayi kan abunda yake da bukatar akawo mai,babu dadewa ko akayi Nooking din kofar ya bude ya amshi babban Farantin da”aka shakosu da kayan marmarin ma”ana Fruit domin sukadai yake iya ci yadan ji dadi bisa bakinsa,ammh bayansu tunda yabaro Nigeria bai kara saka wani abinci abakinsa ba.

  Mu”azzam yasamu wajen zuwa domin yanzu kullum da gari waye zuwa yayi sallar azahar yake fitowa yazo gunan yazauna yana,kallon shige da ficen mutane,kuma baitaba cin komai agunka ba,sukansu ma”aikatar gun sun ganesa shiyasa ko yazo basu bi takansa saboda susan ko sunje baya bukatar akawomai wani abu,kuma kullum da kaya daya yake yawo kamar wani mahaukaci in ka gansa bazaka iya shaida dan wani jinsi bane saboda yadda Gashi da kasumba suka cikamai Fuska babu kyan gani.

    Tadade tana zuwa wajen,kuma inbazata manta ba,kullum wajajen wannan lokacin take ganinsa yana zuwa yazauna shikadai yana kallon waje daya,kuma bayama kowa mgana kuma baitaba shan wani abu ba,wani lokacin sai dai ta ganshi yana sharan kwallah,kimanin Sati daya kenan take lura da Mutumin tun bata maida kai hardai tafara Fuskanta wasu abubuwa agame da shi,na yadda yake mu”amalansa awajen tafara dora ayan Tambaya akansa amtsayinta na babbar likitan zuciya ta fahimci yana fama da wata damuwace wacce take saka shi kebewa daga mu’amala da mutane,haka kurum takejin zata taimakeshi tayi alqawarin in tazo gobe zatamai mgana taji kodaga ina yake,kuma mike damunshi..? kuma shi dan wani kasa ne? me kuma ya kawoshi nan din?


Kimanin Sati hudu kenan Da Tafiyan mu’azzam ammh har zuwa wannan lokacin babu amo ba lbri,Ummi kuwa babu yarda take domin babu abunda ya chanza zani gabadaya ta rame ta lalace kamar ba ita ba,ga yawan kuka ga damuwa,kullum Dr.Abduljabar cikin zuwa dubata yake yana auna jninta tare da kawo mata magunguna,Ummi sai ta wuni ta kwana batama kowa mgana sai dai ta kalleka hawaye yana zuba daga idonta inko ta bude baki zatayi mgana to mganar kenan”Ina Da”na ko kaga Da’na.?Shiyasa rashin mganar bata ma Dr.Abduljabar yace shine mafi a”ala saboda in tana yawan irin haka sai kwakwalwarta tasamu mtsala,hajiya ke tare da ita haryanzu tana taimakamata nasihohi da ban baki kan Ummi ta dau kaddara da hakuri tacigaba da addu”a insha Allahu Mu”azzam zai dawo gareta,jin hajiya kawai take ammh ita tanaji ajikinta ta kusa mutuwa tabar duniyan gabadaya,domin bazata iya jure zama haka babu mu”azzam dinta ba.

  Shureim na zuwa duk weeked wani lokacin yazo shida zulaika ko kuma yazo shida yaransa,wani zubin kuma shikadai,wannan zuwa ne,yaje maiduguri ya duba jikin Shettima wanda halin dayake ciki sai da yasa Shureim ya zubar da kwallah,baffa na kuka yana bama Shureim sako,kan ya rokan masa Suhaima data yafemasa dayake yanzu ansamu yana mgana saboda andage da magani,Dakuma arokan masa mu”azzam shima ya yafemai saboda duk shine silan komai,shi kuka shureim kuka ,yakura kuka,wani abun tashin hankali kuma bukar yazo ya sameshi agidan nan yake bashi goro da minti  dauren Auren zahirah sati mai zuwa.

Iya Rikicewa Shureim ya rikice,Duk da yasan cewa dole daman zahirah zatayi aure,to ammh su little Ummi ba da Moodu yaza”ayi dasu,kamar bukar yasan abunda ke ranshi yace”Kada yadamu zata cigaba da shayar da yaran har zuwa ta yayesu kafin suzo su karbi yaransu shi mijin nata ya amince da hakan,shikuma mu”azzam Allah ya bayyanasa”Sadda kai kawai Shureim yayi yana goge kwallah,Yakura ma daki ta shige tana ta kuka,daya nemi ganawa da zahirah kiri kiri bukar ya hana yace”bata da masaniyar duk abunda ke faruwa hatta da ko auren da za”a daura mata,saboda haka bayason yaje ya tadama yarsa da hankali yayi hakuri kawai sun gode Allah bar zumunci”Babu yarda Shureim ya iya banda hakuri domin kome yafaru baiga laifinsa ba,duk Ummi ce taja wannan abun da bata saka mu”azzam ya saki zahirah ba,da duk haka bata faru ba,Sakon dayazo dashi na madaran yaran da kudi yabawa bukar,sai kayan abincin dayazoma su yakura dashi suma ya saukemusu kafin yayi musu sallama yamika hanya,yana mai tsausayama mu”azzam domin ya hadu da jarabta kala kala.

  Agaban Ummi shureim ke maidama hajiya yadda sukayi da bukar,hajiya na hawaye take Furta” Allah Sarki mu”azzam Allah yazama gatanka a duk inda kake..”tafada tana share kwallah kan tacigaba da cewa”Shikuma bukar inda yayi hakuri ko shekara yaran sunyi kafin yayi Tunanin aurar da ita,ammh wannan danyen Hukuncin daya yanke sai naga kamar yayi tsauri,tunda ko baimata aure ba,yasan cewa bazata koma ma mu”azzam ba..”Hajiya tafada cikin tsausayi Ummi dake zaune kawai gani sukai tatashi tana kuka ta haura sama,da kallo suka bita,domin yanzu gabadaya sun ma daina bata laifi Tsausayinta suke ji yadda rayuwa ta maidata,kai bama Ummi ba hatta fulawowin gidan susan cewa babu majinginar gidan,babu bangon gidan domin Namiji shine gida,Ko ma”aikatn gidan suma sun san sun rasa bango buhun sigari kowa ya lasheka sai yalashi siga,Shureim bai tsaya ba washegari nayi ya koma zaria saboda aiki.


SUDAN

   Kamar koyaushe tana gama duba patient dinta ta fito daga cikin asibitin motarta ta hau wata kirar 4matic,ta nufi wajen domin ta wasa wukan yau sai tayimai mgana,haka kurum take jin,tana son jin wani abu game dashi,ko kwanaki da taso mai mgana tafiyace ta kamata zuwa india shiyasa bata koma wajen ba,sai jiya daddare ta dawo shine yau bayan fitowanta daga asibiti ta nufo wajen kai tsaye.

   Illai kuwa tana paka motarta idonta yakai mata kanshi yana zaune,inda yasaba zama,da kuma kayan data saba ganinsa,cikin kuzarinta ta fito daga motar bayan ta sanyata ciki key,ta fara takawa, zuwa garesa kai tsaye ta nufi inda yake,har ta tsaya agabansa baisan da tsayuwar mutum ba,saboda yadda yayi zurfi cikin Tunaninsa tadade tana nazarinsa kafin tayi karfin halin cewa

   “Hy…”Tafada tana mika masa hannu,dagowa yayi cikin mamaki da alja”abi yana kallonta kyakyawan macece fara ce tas mai daukeda da doguwar Fuska hancinta har baka yake,ga dan karamin bakinta wanda yasha jan jan baki,Tana sanye da wata doguwar rigar abaya baka sai mayafinsa wanda ta yane kanta dashi,Fuskarta sanye cikin wani siririn farin glass,sai kafarta dayake sanye da wani takalmi baki mai tsini,sai hannunta na dauke dawata jaka baka da makullim motarta.

Cikin dakika kadan ya karemata kallo,kauda kai yayi bai maida mata da martanin mganarta ba,sai ma yayi kamar ba dashi take ba itakuwa jikintane yayi sanyi lokacin data ci karo da Fuskarsa saida ta tsorata harta dan ja da baya,ammh ganin yadda yawani dauke kai yasata kara matsowa takara cemai hy da yaran hindu,nan ma yayi mata banza,takoma larabci,nan ma yayi mata banza,takoma French nan ma yayi mata banza,kai duk yaren duniyan nan tayi mishi yaki tankata,ganin haka ne yasa cikin tamtama tace”Assalamu Alaika…”Tafada tana shakkar shi din musulmi ne

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button