UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Jin Tayimai sallama yasa,yadago yana kallonta cikin mamaki sanin muhimmanci sallama yasa ya bude baki kamar mai koyon mgana ya amsa mata chan kasan makoshi,wanda ita kadai ne data ke kusa dashi taji abunda yace”Amin wa”alaikis salam..”yace kafin ya kauda kai.

  Mirmishi tayi kan tace”Wow..u are a muslim..?Tafada da sigar tambaya,ko kallonta baiyi ba, cikin jin dadi ta zauna kujeran dake fuskartanshi tana fadin”My Name is DR LUBNA KHAMIS, “Tafada tana kallonsa kafin ta zuramai ido tana fadin”U…”?Tafada tana zakudamai kafada,sunan data fadane yasa ya kalleta kamar zaiyi mgana kawai sai ya kauda kai ya mike yafara tafiya batare da ya ko kalli barayin data ke ba.

DON”T FORGET  TO COMMENT VOTE AND SHARE

    IT ME JAMEELAOMAR
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

 
I Dash d whole page for u Hussain80k,..Allah kadai ne zai iya biyanka Alherinka gareni..Daga yau ina me Sanar da kai UWAR MIJINA…,sadaukarwane gareka  tundaga yanzu,har  zuwa  karshensa,Bari nayi maka irin taku ta indiyawa,Bhahoot Bhahoot..????????????????

My BLOOD,Aisha Umar..Kitaho ki taka wannan Salon na yau naki ne,kip Following hajiyata I love u so much dear Didi????

NOT EDITED????

             NO 29

     Cikin mamaki itama tatashi tana bin bayan shi tana mai mgana cikin harshen Turanci,ammh yayi mata banza,sai ma tafiyarsa dayake kamar ma baisan da halitta wata tana binsa ba,abunda yafi daure mata kai shine yana tafiya yana dafe kai alamar dai tabbas ahashashenta yakusa zama gaskiya kenan.

  Gajiya tayi da binsa ta tsaya cak tana binsa da kallo,agaban idonta ya shige hotel ko waigowa baiyi ba,abun ya shiga bata mamaki tafara tambayanta Who iz he? bata da wannan amsan,cikin mutuwan jiki takoma wajen motarta tayimata key ta shiga tajata tafice daga wajen ranta baya mata dadi,ammh tasaka aranta komai ye game da wannan mutumin sai ta sanshi,tana ji ajikinta wani gagarumin abu ne ke damunsa kuma ayadda ta lura kamar yana fama da mtsalan Rashin lafiya ne,ciwon ne dai haryanzu bata tantance wanne ne ba daga ciki.

    Tana wannan Tunanin ta iso ga wani babban gida Mai bisa ma”ana Upstair ne gidan,kuma da dutse akayi shi,gidane nagani na fada wanda tsayawa misalinshi sai na gama wannan page din bangama ba,hon tayi wani balarabe yazo ya budemata get din yana gaisheta cikin harshen larabci.
  

Jikinta asanyaye tayi parking motarta cikin parking space,ta fito hannuta rike da jakarta tana tafiya cikin rashin kuzari,mahaifinta dake chan sama zaune cikin wasu kujerun alfarma ,dattajine wanda akallah zai ba shekaru 65 da biyar baya ammh hutu da kuma kudi su suka boye shekarunsa,ammh Fuskarsa tana cike da farin gashi, ya kuramata ido cikin Siririn Farin gilashin dake sanye cikin idanunsa,yana hango tsantsan damuwa atare da ita,ganin haka ne yasashi mikewa ya tattara takardun gabansa ya bude wata kofa wacce zata sadashi da cikin gida.

  Da sallama ta shiga falon kafin ta wurga jakarta kan kujera tafada tana runtse ido,Muhammed dake zaune kan daya daga cikin kujerun falon yana latsa waya ya waigo yana kallonta kan ya tabe baki yana fadin”Ke wai meyasa baki da Natsuwa ne? kullum kina girma ammh kina cin kasa..”yafada cikin harshen larabci,dagowa tayi tana bankamai harara kafin tace”Eh din ina ruwanka da rashin Natsuwata..”tafada itama cikin harshen larabci.

  Ransa ne yabaci tuni ya mike yana wuci ya nufota ganin haka yasa ta mike da gudu zata gudu,sai ji tayi taci karo da mutum tana dagowa Tace”ABBIE..”Da karfi kan ta makalkalesa tana fadin”Abbie kaga Mooh ko..”Riketa Abbie yayi yana kallon Namijin yace”Ai kai ne babban banza,kaida yakamata ka ijiye iyali ammah baka da aiki sai hayaniya da kanwarka..”yafada shima cikin harshen larabci.

  Tura baki yayi yana fadin”To ammh Abbie ku bakwa ganin yadda yarinyarnan Tabi ta rainani ne.”Kai ka raina kanka..”Abbie ya bashi amsa yana jan hannun  lubna suka karisa kan kujera  falon yana fadin”Dr meya faru ne,naga kin dawo ranki bace..”gyara zama tayi tana ruko hannunsa take fadin”Abbie ina mutuminnan dana baka lbrin shi jiya..”?tafada tana kallonsa gyadamata kai yayi yana fadin”eh naji meyafaru dashi..?

  Gyara zama tayi tashiga rattafamai abunda yafaru takara da cewa”Allah Abbie Yana bani tsausayi sai danaji Shima musulmi ne irinmu sai naji inason jin wani abu game dashi,ammh yaki bani dama”Tafada cikin Nuna alamun damuwa.

  “Ke lubna bazaki kiyayi kanki da jajaye ba ko,watarana sai kin sai da kanki da kanki..”wata farar mata doguwa ta fada wacce ta fito hannunta dauke da wasu mulmulayen kulolin abinci tana jerawa bisa wani katon tebur din cin abinci mai kama da na liyafan Larabawa,Tabe baki mooh yayi yana fadin”Barta mom Allah yabata sa”a yarinyar nan shigen rawan kai da shisshigi, ina ruwanki da wani,mutum ki barsa mana ammh saboda bala”in ta sai ta yi makanta jajaye”Yafada cikin nuna abun ya isheshi Tura baki Lubna tayi tana fadin’Allah mom don baki gansa bane,Sai yabaki tsausayi..infact ma ni abunda yasa nakeson Taimakamai kamar yanada problem da irin aikina ne dat why”Harara ya bankamata kan yace’ehye yanzu zaki ce yana da alaka da aikin ki mudai kada ki kwasomana wata Annoba gida am telling u…”

“Gaskiya kam..”mom tafada mirmishi dattijon yayi yana riko hannunta yace”Don”t mind them by dota,ki taimkama mai indai ya baki dama,ni na Amince ko nan gidan ne,ki kawosa muji miye lbrinsa,in munda hanyar taimakonsa Fine,in kuma bamu dashi da baza mu rasa yadda zamuyi ba..”yafada yana kallonta da ihun murna tafada jikinsa tana dariya take Fadin”Shukuran Laka ya Abbie…’taketa fada tana ma mooh gwalo wanda yacika yayi tsab kamar zai fashe tabe baki mom tayi tayi ficewarta afalon inda sabo sun saba da halin Lubna da Abbieta wajen shigen jajaye su kowa nasu ne.

Gwarin gwiwan da Abbie yabama lubna shiya karamata karfin gwiwa cigaba da bibiyar mu”azzam sai dai kash inta isa wajen banda sallamanta Dayake amswa baya kara ko kallonta balle tasan ran zai mata mgana,kuma kullum cikin Hotel din take ganin yana shiga kenan shi bako ne zuwa yayi? daya ga alamar tafara takuramai sai ya chanza wajen zama,ammh duk da haka sai ta nemoshi,shiyasa yanzu ya daina zuwa ma kwata kwata ya gwammace yayi zamansa adaki,saboda bayason kowa ya rabeshi shine dalilinsa na barowansa gida,abunda ya lura dashi yarinya so take ta shiga rayuwarshi da karfi da yaji,shikuma abunda bazai yarda dashi ba kenan,babu wata mace datake burgesa afadin Duniyar bayan Hiransa shiyasa ko alama baijin zai ba wata Fuska harta shigo rayuwarsa.


   MAID

    Rana bata karya sai dai uwardiya taji kunya ayau ne bayan ansauko daga sallae jumma”a dubban mutane suka shaida Daurin Auren ZAHIRAH ABUBAKAR BAHGANA DA ANGONTA ALH KABIRU BAKANO* Akan Sadaki aure Naira dubu dari lakadan ba ajalan ba.

  Bakin bukar yaki rufuwa shida angon wanda yasha babba riga da hula shima bakinan yaki Rufuwa,mutane dadama sunga wautar Bukar da irin wannan gaggawan dayayi na aurar da diyarsa tana shayarwa ai da komai miye daya bari ta yaye,ko kuma suyi shekara lokacin sunyi kwari ammh yaki dole shi sai an daura aure,in madaga baya zata tare to babu damuwa,hatta yan”uwanshi sun nuna rashin amincewarsu sunce abari zahirah ta yaye yaranta tukunna ammh sai bukar ya kawo musu Alh kabiru har gida yazo yana rokonsu dasu  taimaka adauran Auren haka tunda addini bai haramta ba,shi ma uba yake ga yaranta wlh matukar ubansu zai barmai su zai rikesu har illa masha Allah,to ganin girmansa tunda ba yaro bane yasa suka amince aka daura aure daga baya zata tare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button