UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Dawani gudu lubna ta mike ta isa garesa tana jijjigasa,lokacin da jama”an dake waje suka shiga kiran sunan Allah suna Fadin”Ya Allahu..Ya subhannallahi..”kuka lubana take cikin Tashin hankali take neman Taimako,wasu larabawa ne,suka taimakata suka sakamata shi abayan motarta Ta shiga taja da wani gudu tana tuki tana waigensa daga baya tana share kwallah,.

Wayarta ta jawo ta  latsa wasu lambobi takara akunni tana fadin”DR SULTAN am coming wit a Hartfailure Patient..”tafada lokaci daya ta waigen mu”azzam dake baya hancinsa na cigaba da zuban jini,ko alamar Numfashi babu Atare da shi.

  Daga chan bangaren Dr.Sultan ya amsa dace”Ok madam..”

  DON”T FORGET TO VOTE, COMMENT AND SHARE

        Jameelatomar

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

wannan Shafin sadaukarwane,gareki,BILLY S FARI..,Ina matukar godiya da yadda kike bibiyan Littafin Uwar mijinah!Janafy relli Appreciate

NOT EDITED????

                NO 30

   #Nadama

   Cikin Abunda baifi minti goma ba, tashigo cikin wani haraban makeken Asibiti mai dauke da hawa hawan bene na gani na fada,katon Asibitine daya kusa kama dawata anguwa saboda girmansa,specialist hopital ne mallakin gwannatin kasar ne,tana kula dashi Ainun kuma duk yawancin likitocinta baki ne,daga yan india sai yan US Ameriaca,Da sauransu kalilan ne xaka ci karo da laraba,domin kowani jinsi akwaishi acikin Asibitin.

    Cikin wani Sauri ta paka motar lokaci daya tayi waje da gudu tana kiran Nurses da gudu take tanayi tana haki kamar bata cikin hayyacinta da gudu kuwa suka fito dauke dawani, dan gado na daukan marasa lafiya,tana ganinsu takoma da baya suka biyota,ganin yadda Dr lubna taje arude yasa suke komai cikin kuzari,ita ta budemusu bayan mota suka Fito dashi,dayake akwai maza cikin azama suka dorasa akai suna gungurasa zuwa cikin Asibitin.

   Suna gabda isa emargency ne Dr Sultan ya fito,Sukaci karo da Dr Lubna tana ganinsa tace”yauwa Dr,plz help me..”Tafada tana nunamai mu”azzam da”ake gungurowa cikin jini baya ko motsi cikin tashin hankali Dr Sultan yake kara gungurasa yana fadin”Oh my god mah,dis is a Serious problem,ya Allah..”yafada cikin zafin nama yana turasa da karfi,ganin haka yasa sauran likitocin dake wajen suka bisu da gudu suna dafe kai ganin yadda mu”azzam din ke zubar da jini ta baki ta hanci da Sauri suka shiga dashi cikin emargency wanda Nurses din dake biye dasu suka ci burki suko sauran likitocin suka dumguma ciki lokaci daya kofar glass din ta kulle kanta.

   Suna shiga dashi ciki suka ciccibesa suka dora bisa Ainihin gadon dayake dakin,suka fara jona jonan Na”urori bisa jikinshi cikin hanzari kowanne yasaka hand glob,Dr lubna ma cikin zafin nama take kokarin Tsaida jinin dake zuba lokaci daya Dr Sultan ke kokarin dawo da Numfashinsa,ammh abu ya ci Tura jinin ma yaki tsayawa,kuma kokarin nemo Numfashin nasa ma yaki yuyuwa,Nu”urori sai kuka suke,ganin haka yasa Dr lubna cire safar hannunta ta fice daga wajen hankalinta atashe.

  Office dinta taje ta kifa kanta jikin Tebur haka kurum taji hawaye na bin kumatunta,bata sanshi ba,bata da wata akala dashi ammh lokaci daya zuciyarta ta Aminta dashi, taimakamasa Ashe Ashe yana cikin wani hali?halin Ciwon zuciya,Tsausayinshi takeji bata Fatan ya mutu,tafi so Asamu Numfashinsa ko zataji Kadan daga Tarihinsa,kafin kace me Dr lubna takece da kukan Tsausayin mu”azzam kamar ance mata uwarta ta mutu sai da tayi ma”ishi kafin tafada Toilet ta wanke idonta.

  Awa uku suka shafe aciki kafin su samu nasarar daidata komai Numfashinsa yadawo dakyar ammh bayan Sunyi Nasarar Tsaida jininsa dake zuba,Ganin yadda jininsa yayi kasa yana bukatar karin jini cikin Minti Talatin in ba hakaba akwai mtsala,yasa Dr Sultan Fita da Sauri ya isa ga office din Dr lubna.

  Abunda yabashi mamaki ganinta tsaye tana kaida kawo hankalinta atashe ga idanunta sun kumbura alaman Tasha kuka,kallo daya yayi mata ya Fahimci tayi kuka,tana ganin Shigowarsa tanufesa tana fadin”Dr, how is he..? Hop he survive? ajiyar zuciya ya sauke yana kafeta da manyan idanunsa yace”Alhamdulillah,evertin Is normal By Now,but jininsa yayi Low fa yana bukatar karin jini yanzu bada dadewa ba”

  Saurin yin gaba tayi tana fadin”i belong to group O BLOOD..Muje ayi Taking nawa a sakamai Dr,plz bani so mu rasa wannan patient din”Tafada cikin damuwa,ganin yadda tarude ne yasa yakasa yimata gaddama kawai sai yabita suka nufi lab din,ammh tambayoyi fal aransa,akan Dr lubna da wannan Sabon Patient din data kawo musu.

     Leda biyu aka diba nata aka sanyamai cikin lokaci kadan jinin yafara gauraya da jikinsa,wasu manyan Allurai sukamai na Samun Hutu,kafin su kaisa wani daki na mussaman,Sai dai ajira Farfadowansa,itakuma lubna an bata hutu ne saboda an dibi jinin nata da dan yawa,har leda biyu,Dr,sultan ke tare da ita,yana kula da ita,Tunda shi haka Allah yaso dashi SON WACCE BATA SONSHI.

    Ita gabadaya batama ta Dr Sultan, dakefaman kula da ita,hankalinta na ga mu”azzam lokaci daya takejin wani yanayin game da mutumin,batasan Dalili ba ammh tanajin wani abu game dashi wanda batasan dalili ba,ammh tafi dorashi amizanin Tsausayi,.

  Abbie ne yajita shuru bata dawo ba shine yakirata,cikin damuwa lubna ke fadamai Abunda kefaruwa,matukar tsausayawa Abbie ya tsausaya yayi mata fatan Samun Nasara,kuma ya jinjinamata bisa halinta na son Taimakon mutane,Sunyi sallama akan sai gobe zata dawo yanzu dare yayi bazata iya yin Driving ba,Koda Abbie yake fadama mom abunda lubna tace yana fadamusu lbrin mutumin databasu Tsaki mooh yaja,wanda ke zaune falo yana latsan waya ita kanta mom din baki ta tabe,suna jin Haushin Lubna da shegen jajaye,Abbie bai wani damu ba,don kaf hallayan lubna nashine.

      Kwana uku Mu”azzam ya shafe cikin halin Suma,kafin ya farfado,koda ya farfado da lubna yafaracin karo wacce tun bayan kawo asibitin taketa kula dashi,sosai bata da wani sukuni kullum zullumi take da tunanin Farkawansa,bayan ya farka Dr Sultan ya duddubasa yaga komai Normal sai dai zai cigaba da karban mgani kuma zasu dan rikesa na wani lokaci kafin komai ya daidaita.

   Lokacin dayaci karo da lubna,ransa yabaci yana tunanin yaushe har ya yarda ya takawosa nan,Ransa kwata kwata babu dadi,yaso tabarshi ya mutu wla chan yafiyemai nan,ko ba bakomai zai huta da rikitarikin dake cikin Duniyarnan,Koda ya farka din Dr.Lubna tayi mganar Duniya ammh ko tak mu”azzam baice mata ba,Tayi ta mai Sannu da jiki da tambayan Sunansa ammh ko kallo bata isheshi ba,baima nuna yagane dashi take ba,magugunansa kuwa sai dai Dr.Sultan yabashi ammh in itane bazai taba amsa ba,Abun na matukar bata mamaki da daure kai ammh ganin condition din dayake ciki,yasa take mai Uzuri take binsa a hankali in tayi lura da yanayin mtsalarsa kila wani abu akayimai wanda yayi sanadiyar shigansa,halin dayake ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button