UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hohoho,Kowa sai tambaya yake don Allah ina Janaf take?hmmm janaf na nan a inda kuke,bana cika posting bane cuz abubuwa sunman yawa,Masu tambayan digit dins am srry to say bawai ina nufin ni mai tsada bace,buh Nombartawace mai tsada,Janaf freeking fans zan baku nombata buh in one condition kada wani Namji ya kirani plz and plz ina daraja kaina,to kutayani darajawa,Females only don Allah,Kira mai amfani ko sako mai amfani,matukar kinsan baki dawani abun fada,plz and plz karkisoman Daukan Nombata,bana da wulakanci,kuma bani son ni a wulakantani,ku rike mutumcinku nima na rike nawa..I love u so much Masoyana Allah ya barkauna ta har abada

Here iz 09069067488

comment share and vote..

     Janafy
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

Jiya naji matukar kunya alokacin dana ci karo da wasu marubuta awasu groups din sun zauna anacin Zarafin marubuta yan”uwansu,Me kukayi kenan? kuna Tsammanin kun burgene don an zagi marubuta yan’uwanku? kokowa abun alfaharikune don azauna anayi da wata marubuciya kina saka baki kina Kara bawa readers dama rainamu? To kusani kanku ku kamawa,domin ruwan Daya hadiye bukar shizaije ya dawo ya hadiye habu,duk abun dayane Hajiyata,ke marubuciya ce itama haka so baki wuce kema yafaru dake ba,matukar munaso, Amana Adalci to muma sai munma kanmu ADALCI..,Na fada na kara fada ni JAMILAJANAFTY KO A BAKIN KURA NAKE ZAN KARE HAKKIN MARUCI,DOMIN YAU GAREKANE GOBE GA WANINKA

NOT EDITED????

           NO 32

      “”Shine wa..”Lubna ta ambata bakinta na rawa.
  
Dagowa Abbie yayi yana fadin”Shine,dan wajen Aminina marigayi Muhammed moodu,wanda mukayi karatu dashi a madina,kun manta kullum kwanan duniya sai na muku zence sa,? to yaron wajensa ne Allah na godemaka”yafada hawaye suna zubomai yana kara riko mu”azzam din.

  Kuramai do mu”azzam yayi kafin bakinsa ya bude yana Rawa yace”Abbah kh..mis….? yafada cikin Rawan murya da kuma sigar tambaya,kallonsa Abbie yayi yana fadin”kaima kasani ko,?sunbaka lbri na? nine Abbanka,Rumana, muhammed,Lubna ku taho ga dan”uwanku,ashe lubna dan”uwanki ne,kika damu ki taimakamai kai Allah nagode maka”

  yafada yana kara rumgumesa cikin wani yanayi mu”azzam ya rumgume Abbie khamis lokaci daya yanajin hawaye suna taru a idanunsa,tsawon lokaci Abbie na rumgume dashi kafin ya sakeshi ya riko hannunsa,har zuwa cikin falon ya xaunar dashi kan kujera yana fadin”ku zo ku zauna,yau ranace mai muhimmanci a rayuwarmu ku matso dan”uwanku ne..’yafada cikin murna.

   karisowa falon lubna tayi gabadaya kwanyatan tadaina aiki,mutumin data taikama,da yake ga abokin abbanta ashe? haba shiyasa takejin wani abu game dashi,takejin shi tamakar dan”uwanta da suka fito ciki daya,ashe ashe akwai wata alaka mai karfi tsakanin iyayensu basu basani ba,sai gashi dalilin taimakonsa har Abbanta yahadu da abunda tun tasowarsu bai taba fashin ambatansa ba daidai da Rana daya.

Mooh da mom suka zauna suma asanyaye suna bin mu”azzam da kallo,wanda shima yake kallonsu haryanzu mamaki bai bar Fuskarsa ba,kallonsa mu”azzam yayi kafin yace”a lbrin da Ummi na tabani ta fadamin tun bayan komawarka sudan,baka kara dawowa ba baka nemesu ba,itama kuma bata nemeka ba,Tun bayan Rasuwar Abbana,abun mamki taya kasan cewa Allah yayima mahaifina Rasuwa?

Kuri Abbie yayi masa da ido kafin ya Sauke ajiyar zuciya,kauda kai yayi hawaye suka ciko idanunsa suka kwaranyo Mooh da lubna suka kalli juna suna zaro ido,Abbie na hawaye? abunda basu taba gani ba itako mom ajiyar zuciya ta sauke domin ita datake tare da khamis tafi kowa sanin rauninsa duk rannar daya tuna Aminin nasa.

Hannu yasa ya share hawaye kafin ya dago yana kallon mu”azzam,hannunsa ya riko dama yana kusa dashi cikin dashasshiyar murya yace”Nasan Abokina Muhammed moodu ya rasu tun lokacin da bai dade da Rasuwa ba”

  Cikin mamaki Mu”azzam ya kallesa kafin yayi mgana Abbie ya rigasa da cewa”Zan fada muku komai yanzu..”

   Ajiyar zuciya Abbie ya sauke kafin ya fara magana cikin Raunin murya.

  Tabbas bayan Komawata na koma cikin damuwa halin da Aminina yake ciki,shida matarsa,ganin yadda gabadaya yan”uwansa babu wanda ya amshesa daga shi har matarsa nasa,wanda koni da sukazo dani na zammanto musu shaida sunki yarda dani,bayan komawata muna waya da moodu ammh kullum na tambayenshi ya ake cike game da zaman shi da yan”uwansa sai yacemin babu komai,in na kuma tambayi ya Suhaima nan yace min komai Normal,duk da hakan ban yarda ba domin ayanayinsa kadai nakan gane yana cikin damuwa kwatsam yakirani yana fadamin Rasuwar mahaifinsa wanda yanayin yadda naji moodu namin kuka ta waya abun yadagamin hankali,domin koda muke karatu amadina moodu mutum ne mai taurin zuciya kafin kaga abunda zai sakashi kuka abu ne maigirma,shiyasa hankalina ya tashi ainun,nayi shiri zan taho Nageria sai Ciwon Suger da Ammina ke fama dashi ya tashi har akayi Addimitting dinmu a hopt,shine ya dakatar dani daga tahowa,lokacin dataji sauki nanemi na taho moodu yahanani tahowa kan inyi zamana kawai Allah yajikan baba,Hakanan na hakura da zuwa sakamakon rokon da moodu yayimin na kada nazo,shida kanshi zaizo da ankwana biyu,bazan taba mantawa ba waya ta dashi na karshe yakirani da daddare misalin karfe uku na dare mu anan kenan,yadda yakemin mgana na fahimci tabbas akwai mtsala nan da nan na rude ina tambayanshi meke faruwa ne,nan yake fadamin duk abunda yafaru tun bayan barowata da yadda Shettima da fadi su ka dinga,muzgunama rayuwarsa data Suhaima marainiyar Allah,kafin yagama bani lbri kuka ya kwacemin na tsausayin Aminina,bai bani dabam mgana ba,yace baya da lafiya yaje yaga likita kuma an tabbatarmai da yakamu da hawan jini sakamakon yadda yake matsama kansa da damuwa,kuma yanaji ajikinsa bazai kai zuwa tsawon wani lokaci ba,ga amanar Suhaimar nan yabari gareni,Bata da kowa sai shi sai ni,kuma shi baya tunanin zaiyi tsawon rai,muna cikin mgana ne kawai wayar ta wanke,nayi ta kira ammh ban samu ba,hankalina ya tashi naso na taho tun washe gari ammh bansamu Visa ba,sai bayan Kwana goma,alokacin zuciyata tagama tsinkewa da al”amuran Moodu domin wayarsa tun ranar bata kara shiga,ba Na taho Nageria ranar wata asabar na iso maiduguri da yamma lokacin misalin 5:00pm na yamma na sauka kofar gidan Fitowa daga kekenapep,kenan muka hada ido da Shettima shida Fadi sun Fito daga gidan da alama suna wata mgana ne,Suna ganina suka wani yi tsam dasu,alaman sunyi mamakin ganina,niko cikin azama na nufesu ina mika Shettima hannu,ammh sai yaki amsa ya noke hannunsa yana bina da wani malalacin kallo ban dandaraba na sake mikamai,ammh wannan karon sai ya buge hannun nawa yana fadin”mallam daga ina? bibiyan kuma na menene,? wanda yahada to yau bashi aduniya saika kara gaba kuma ko” Shettima yafada fuskarsa ba Annuri Fadi ta amshe da fadin’ah to shi nagani yaya,moodu ne dama yazo dakai,kuma yau kwanansa tara da rasuwa,ai inaga bawani Sauran bashi ko mallam”tafada tana hararata,jin kalaman dasuka fadane yasa yar jakar dake hannuna ta subuce ta fadi,tuni hawaye suka wankemin ido,cikin tashin hankali da rawan murya nake fadin”moodu..Ya…ra..su..”nafada hawaye suna kara zubomun,babu ko tsausayin Aransu ganin halin dana shiga Shettima yace”eh aka ce,kai banzan balarabe ko Hausan bakaji ance maka abokin naka ya rasu,sai ka kama gabanka ko bakaji bane”dafe kaina nayi ina tsiyayan hawaye lokaci daya na dago yana kallonsu kafin nace”Moodu ya rasu? ina Suhaima matarsa take,ku kaini wajenta”kallon kallo aka fara tsakanin Fadi da shettima kafin fadi tace”gata goye abayanmu,kai dai maye ne,karabu damu muji da abunda ke damunmu mana,ita tun da yarasu takama gabanta dama haduwar bariki ce” tafada tana yamutsa Fuska,Gyada kai shettima yayi yana fadin”kwarai makuwa,itama takara gaba,saboda haka bamu da sauran wani abun da zaka tsaya kana titsiyemu da tambaya,ka koma inda ka fito mun gode…”Yafada yana hararata dukurkushe nayi agabansu ina hawaye nace”don Allah ku taimakeni ku kaini inga Suhaima wlh amanarta moodu yabani don Allah..”shekeke suka kalleni kan Fadi tace”mun Shiga uku yaya,zai taramana jama”a,kagafa yadda yayimana durkuso yana hawaye salon mutane su farga suce wani abu mukayi masa,ka sallamesa ko kuma sai ka kira masa karti ne,sun bacemana dashi akofar gidan”Gyada kai shettima yayi yana waige waige yake fadin”inaga haka za”ayi bari Tunda yaki tafiya..”ganin yadda yake waige waigene ya sani mikewa ina binsu da kallo ina hawaye suko ko ajinkinsu saima dauke kai da sukayi kamar basu ba,jakata na dauka na rataya ina kuka nace”Allah…ya..Ji…kan..Moodu…”Amin munji don Allah katafi mungaji da ganinka”Fadi ta fada cike da masifa,hakanan inaji inagani najuya nafara tafiya ina sharan hawaye ina waigensu,duk da lokacin yammah ne ammh babu yalwar mutane,agun sosai sai jefi jefi ne suke wucewa,ahaka ina tafe ina kuka har na karisa bakin titi na samu abun hawa,Hotel naje nakama,wanda kwana nayi ina kuka,washegari tun safe na biyo jirgi zuwa lagos,kwana biyu na kara na biyo jirgi na dawo Sudan,Wanda saboda yadda mutuwar mahaifinka ta dakeni sai da na kwanta a asibiti,sai da iyayyena suka dagemin da addu’an kana na dawo daidai,Koda zuciyata bata yarda cewa suhaima ta tafi ba,ammh banda karfin gwiwan karyatawa,tunda Basu bani  wata dama da zan gane cewa ba hakane bane,sun min koran kare,suna tunanin kila dukiyan mahaifinka zan amsa kowani abu daya danganci haka,Shekara daya nayi ina fama da Nauyin Amanar mahaifinka,ammh basan yadda zanyi na cika masa wannan amanartashi ba,bani da wanda zai bani lbri game da Mahaifiyar,iyayyena suka nema aure da Rumana,yar uwatane,Shekaran aurenmu muka haifi da namiji,wanda yaci sunan mahaifinka,Muhammed muna kiransa mooh,bayan ita sai Lubna wanda daga su bamu sake haihuwa ba iyayena kuwa duka Allah yayi musu rasuwa,dukkansu sun mutu da sanin lbrin yadda nake kwana na tashi da Tunanin girman Amanar da mahaifinka ya barmin,ga sunan ka tambayesu duk kwanan duniya,sai na tuna mahaifinka da mahaifiyarka,kukan Rashinsa kuwa basan iyakaba,kullum kuma lbrin mahaifinka har sun dade da haddaceshi agidanan,ban sani ba,ban kuma ji wani lbri game da Suhaima ba,balle naji lbrin Moodu ya rasu ya barta da cikinka,Kwatsam lubna tazomin da lbrin ta hadu dakai,kuma yadda kalura kana cikin mawuyacin hali,kuma kaki bata dama,data gayamin ni nayita bata karfin gwiwan juriya akan hakan,ashe ashe jini ke bibiyanta zata sakani farinciki da fatan Sauke Nauyin daya rataya awuyana wanda shekara da shekaru yake damuna,Allah kadai ne zai iya fisalta farincikin danake ciki,tun bayan Rasuwar moodu yauce rana ta farko danaji Bakincikin dake damuna ya gushe

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button