UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Yagana dake Cikin bedroom dinta ita da kawarta Zinatu tayi wuf tatashi jin guda ya mamaye gidan,dafe kirji tayi tana kwalalo ido take fadin”Zinatu ya tabbata ga amarya an kawo,wlh ji nake kamar naje na burmata wuka agaban iyayan nata..”

Tsaki zinatu taja tana fadin”mtsewww…Sai kije ki bankamata ana miki fadan kikiyayi kiwon awaki kina zencen kyallah ta haihu,miye na damuwa keda kikasan nan da Sati daya zata koma inda ta fito..”

Comment share and vote

       Jamilajanafty
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED????

            NO 33

   “Kallonta yagana tayi kan tace”Allah Qawata..”wani killer smile Zinatu tayi kafin tace”indai da mallam da boko sai fita ta barmiki gidanki da mijinki nasha ruwan walh Qawata..”

  Tafada cikin gadara da wani yatsina hannu yagana ta bata suka kashe tafadin”Shegiya qawata ko shedan na tsoron hada hanya dake'”dariya tana fadin”don uban mutun shidin shedan na hada hanya dashi,ne yo duk karatun dayane,Karatun dare dukkanmu mukayi Shiyasa har tafaru ta kare bamu Fahimci komai ba”dariya suka sheke dashi suka kara tafawa daidai lokacin dasukaji shigowarsu falon yan”uwan Alhaji da sukazo daga kano suna musu lale marhaba.

   Cikin mutumci da kararramawa yan”uwan kabiru suka amshesu akasa suka zaunar da zahirah,wata diyar goggon kabirun wacce,ake kira da uwani tayi karaf ta karbe Little Ummi dake hannun Hajiya tana fadin”Allahu akbar kaga inda akeyi don Allah,irin haihuwa jikar akbarka,Allah yasa wata shekara ki haifoma yan hudu ne ma ba yan biyu ba”tafada tana shilla little ummi wacce ke bangala dariya,nan wata ma ta karbi moodu suna tayabawa suna saka albarka.

  Hajiya ne tayi gyara murya tana fadin”To masha Allahu yaudai ga amaryanku mun kawo muku,munji dadin yadda kuka karbemu ga zahirah nan ta shigo cikinku fatan zaku riketa tamkar yarku ta cikinku domin yanzu taku ce sai,kuma kunyi hakuri dan tana da danyen jego”Uwani ce ta karbe da cewa'”Mu karba wlh Allah yabada zaman lafiya mai dorewa da hakuri da juna,yara kuma muna so inda karima akawo wlh kawu bai ki ba,shida ya kwashi Shekaru kullum ya shigo gida sai haushi wata karya kullum jiya iyau babu cigaba”tafada tana hararan dakin yagana wacce ke ciki sunajin duk maganganun da uwani ke watsawa.

Cikin Zafin rai,yagana ta mike zinatu ta rikota kallonta tayi tana huci tace”sakeni na fita naci mai cin uwar wanchan ballagazan karuwar kauyen”Tafada tana huci,sakinta Zinatu tayi tana fadin”easy madam,barta keda kikeda takamar nasu hannu yo wani burga za”ayi miki barta tayi lokacinta ne,gobe bazata yi ba ko,?”tafada tana kallonta ajiyar zuciya yagana ta sauke kafin takoma gefe ta zauna tana huci zinatu na mata dariyan shakiyanci.

  Yakura ne takatse su da yadda suke zubama zahirah kirari da kuma yabo,gefe daya kuma suna yadama yagana habaici,da fadin”amm,ina shashen uwargidan mu kaita mu damkamata amana bisa al”ada dare nayi..”Uwani ta mike tana fadin”ku taso ku biyoni kunsan matar gidan sai mai gidan”tafada cikin gatse taso zahirah sukayi suka bi Uwani inda Ta wuce kai tsaye cikin wani bedroom tana tura kofan lokaci daya da sallama.

Su Ashe na ganin haka suka hada baki suna sakin guda,masu yawo da kamshi Turare suna ta fama dashi,Suna shigowa yagana da zinatu suka kallesu shekesheke cike da mamaki har suka zazzauna bisa kafet din dake tsakar dakin,Uwani tace tana nuna yagana”ga uwar gida karfen gida,uwar gida ga amarya hasken gidan ta shigo an kawo miki amanar nan ne ta iyaye dasuke badawa tun al”adunmu na da..”

  Da gayyah tafadi maganar bayan ta wani juyamata ido,wani wulakattacen kallo yagana kebin uwanin dashi kafin tace”yo ai na aza uwani yar kanzaki ke zaki karbi amanar don naga kiris yarage ki kaso aurenki kuzo ki auri kawun naki muyi zaman kishi,dake”tafada kai tsaye lokaci daya tana balla masu Hajiya da sukayi tsuru tsuru harara

Baki Uwanu ta rike kan tace”Wane ni da kaddarar dole,ai Uwani tayi zaman kishi dake yagana watan tonon asirinki ne yazo,ai amaryar dai ita ta dace dake,domin daga kamun ludayin mutum ake gani beran masar ne,ba mutum takamar wani Namiji  mage ba”Tafada tana tura dankwalinta gaba.
 

zuciya ta ciko Yagana zatayi mgana Zinatu ta rigata da cewa”kai kai Qawata wannan wani turare ake busamana,kada ace dai Turaran mallakane ake turaremu dashi”Tafada tana toshe hanci yamutsa Fuska yagana tayi tana fadin”wa yasani Tunda dangin ASiri ne,in Atsaye suke to ni yagana A tafe na kwana,zencen amana plz and plz kutashi ku barmin daki,amana ban karba ba,bakuma zan karba kabiru ne tazo taji abunda nakeji inace jijiyace takawota tazo taja ta barta domin mallakin yagana ce ita kadai..”Tafada cikin izgili.

  Cikin mamaki suke binta da kallo barinma hajiya wacce ke bin yagana da kallon mamaki,itako zahirah tana cikin mayafi tana kuka,batasan sadda taji kukan ya tsaigaita ba,tadago kanta ta cikin shara sharan lifayanta tana karema yagana kallo wacce ke jifansu da mugun kallo,Ashe ne ta miki tana fadin”ikon Allah haba baiwar Allah ammh kodon ganin idonmu kya rage wani abun ko? muma saboda al”ada ne kada muki kawota kice ba”a darajaki ba,ammh kam amanarta ai mijintane kadai zamu damkamawa,keda ita kuwa kowa ya iya allonsa ya wanke,yadda za”a kirasa mijinki haka za”a kirashi mijinta,kinga duk abun daya ne”tafada tana ballamata harara kan tace”kutashi mu sada ta da dakinta dare nayi kar mu shiga lokacin ango.

Dariya suka sheke dashi atare kafin zinatu ta mike tana fadin”ke kuma asuwa,gayyah Arna a idi,jibi bakinki don Allah…”Tafada tana nunata kafin sukara tsintsirewa da dariya,Ashe kuwa ta waigo tace”Ni a ubanki da uwarki,Tambadaddiya mara kamun kai,yo gwanda kowa da kowan wanke ko banza ita kawar taki Allah ya rufamata Aure ya lullubeta kefa,banda yawan kan ta zubar ba abunda kekiyi Kasuwa duka ta kulle an rasa inda za”a sai yawon bin gidajen kawaye Ana neman kashe musu aure,kibari kiyi auren sai ki samu bakin mgana” Tafada tana huci tare da rike kugu.

  Ganin haka yasa yakura mikewa da zahirah wacce abunda ke faruwa ya daskarar da ita,yakura tacema hajiya”hajiya ku tashi mutafi.Ke kuma Allah baki hakuri mun fita hakkinki..”Tafada tana rumgume zahirah jikinta,kama hanyar Fita sukayi zinatu ta mike don mganar da Ashe ta fadamata ya dafata tayi tsalle tasha gabanta tana fadin”Ke Kuchakar cikin gida kalleni nan,ki gani nafi karfinki da dukama danginki,Koda BARIKI TA FITO(mry obam) ta ganni da bariki na wlh,nafiki tashanci,har ni zaki nunama Burauba,Haihuwar lagos girman kaduna,ba kadan iskacin da bansani ba,yo Allah na tuba wani darene,jemage bai gani,yarinyace yadda kukawota haka zakuzo ku dauketa domin Qawatace kadai take da alhakin mallakan Alhaji ita kadai bayan ita babu wacce ta isa kowacece itakuwa koda kan buzun mallam take kwana kuwa”Tafada tana tunkude Ashe,akwai Ashe ta yarfe hannunta bayan ta tsaya da kafanta mahgana tadinga jan hannun Ashe tana fadin”A’i rabasu don Allah ki wuce muje..”ammh ina sai da Ashe tace”ahhayyye nanaye..ke barikin waje ce,niko kilacin cikin gidane,nasan duk wani nau”i na iskanci da tambalewa da na rayuwar yau da kullum domin nine in nayi gohi za”a cini batare da bacin rai ba,kuma ga tarin lada????????????????wata fa,Sai ta fita ta nema in akayi rashin sa”a bayan anci shegiya a zubamata na jaki,kinga ko kotanan ta miki zarrah,yo dakike fadin Alhaji,yo ai mganar banza kike Alhaji yagaji da zama da juya shima yana bukar ganin wahalarsa aduniya ya auro jinin haihuwa,kuma insha Allah shekara mai zuwa sai munzo sunan yan hudu bama yan biyu ba,Sai da bakinciki ya kashe mutum,kuma da iznin lahi Sharri sai yakoma ma maishi”Tafada tana hararansu tare da buga musu tsaki duk da mahgana nata janta,su hajiya tuni sukayi waje don wannan kalaman na Ashe ya girmi kunnansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button