UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da hannun Ummi ta yafito Lubna,ta mike jikinta asanyaye ta isa gareta kusa da mu”azzam ta zaunar da ita ta hada hannuwansu tana fadin’,”Na yarda na Amince abaya nayi kuskure,na kasance Muguwar uwarmiji ga zahirah,ayayinda na kasance Mara tsausayin uwa gareka Son,ammh wannan karon zan gyara kuskure,zan zauna da lubna tamkar yata ta cikna,zan tafiyar da ita tamkar yadda zan tafiyar dakai son,ina rokon Allah ya baku zaman lafiya da zuru”a mai albarka,ita kuma zahirah ina addu”an Allah yasa akwai Sauran zama tsakaninku..”Tafada tana fashewa da kuka,daga mu”azzam din har Lubna rumgumeta sukayi suna lallashinta.
Cikin lokaci kadan Su karime suka kamallah girkin abinci suka jera bisa dining din,nan fa family din gabadaya suka hadu suna cin abinci cikinraha,sake baki kawai su Mooh sukayi sunagani tsabar soyayyar uwa da d’a,domin Ummi bata bar mu”azzam yaci abinci da hannunsa ba,ita tadinga bashi,shima da hannunsa yabata har ta koshi,sun kasa sakin hannun juna,Ummi gani take tamkar inta sakeshi zata kara rashashi ne.
Saman Ummi nan aka Sauki Mom da lubna,shikuma mooh barayin mu”azzam dayake two bedroom ne,Abbie ya shiga daya,kowa yayi wanka ya sauya kaya,Mu”azzam da kansa ya karbi wayar hajiya ya kira Shureim wanda ke tsaka da duba patient,yaji kiran hajiya yadauka cikin kulawa yana fadin”Hajjaju..”Yafada yana dariya.
Lumshe ido yayi yanajin wani Farinciki yana ratsashi najin muryan dan”uwanshi cikin kasala da Taruwar Hawaye yace”Dan”uwa..”,yafada cikin kewa,Da hanzari Shureim ya mike bakinsa na rawa yace”Dan”uwa..Na..ne..Da…Gas..ke…”yake fada bakinsa na rawa.
Dariyar Farinciki Mu”azzam ya saki kafin yace”Yes dan”uwa,kayi hanzari kataho na dawo gida,idanuwa kai kadai suka rage basu gani ba..”ihun murna Shureim yasaki yana fadin”Alhamdulillah Allah Abun godiya..,How comes dan”uwa? ina ka shigene kabarmu cikin damuwar rashinka..”Mu”azzam yace,”Is a long Story Dan’uwa,kabaro zaria yau don Allah.”,Shureim yace”Yanzu ma kuwa dan”uwa” yafada yana dariya katse wayar mu”azzam yayi yana share kwallah ya furta afili “No happy place like Home..”
Shureim yana zuwa gida yagayamata gud news,tayi murna sosai,na da nan ta shirya musu kayansu ita dashi da yara suka nufo hanya saboda yadda Shureim ya zaku yaga mu”azzam ,da yammah suka iso,Mu”azzam najin bude get ya fito waje da hanzari Shureim na hangosa bai gama daidata tsayuwar motar ba,ya fito da gudu suka rumgume juna suka kukan Farinciki,kafin sukoma dariyar Murna.
Sai da suka natsu kafin mu”azzam ya warwaremasa komai harda Auren lubna,Hakika Shureim ya tsausayama mu”azzam matuka,sai da yayi masa kwallah,hakuri yayi ta bashi yana kara mai nasihan yarda da kaddara,nan mu”azzam ke tambayanshi ina yaransa,Shureim ya fito da wayarsa yana nuna masa hoton dayayi musu last kafin zahirah tayi aure,amsa mu”azzam yayi yana kallon su Little Ummi yana hawaye,tare da jin wani bakinciki da kewa sun dabaibayeshi.
Mu”azzam da mooh da Shureim suka hade daki daya,zaratan maza,masuji da kyau da kudi,tuni mooh ya shige cikinsu ana shan hiran yaushe gamo,lokaci kadan suka saba kamar sun Shekara da haduwa dama ga Shureim iyayan tadi ansamu mooh sun tsinke da surutu,duk da mu”azzam din na saka musu baki,ammh firar tafi karfi tsakanin Shureim da mooh.
Zulaika ko sun hade da Lubna da mom da Ummi da hajiya suma suna falo suna shan hira,Ummi na bada lbrin zamanta asudan din,sunata hira da Mom tana bata wasu lbran na chan,hajiya na saka musu baki,zulaika ko da Lubna suma suna gefe sun tsinke da hira,domin Lubna akwai sabo da hira,duk da Zulaika na dari dari da ita,batasan sadda ta saki jiki da itaba suna kwararan hira,ayayin da Sultan wanda zulaika ke goyo Yake hannun Lubna tana mai wasa,Tsakani ga Allah gida yayi albarka duk barayin dakaje farincikin zaka gani tsantsan.Abbie ne ke cikin daki yana barcin gajiya baima san wainar da”ake toyawaba..
Washegari Sai ga Dr.Abduljabar yazo gidan bayan Shuriem yayimai waya yafadamai,nan fa suka hade su hudu suna shan firar bayan rabuwa,aharaban gidan suka shimfida katuwar darduma suna zaune suna hira gabansu kuwa cike da farantai wadanda ke shake da kayan marmari,suna ci suna hira,yau din kam Abbie ma cikinsu ya shige ana ta hira da wasa da dariya duk don su kara kwanatarma Da mu”azzam hankali,kuma ba laifi yafara sakin jiki,yana kokarin nuna komai ba komai bane.
Kwana hudu Shureim yayi kafin ya wuce,wannan karan dai Hajiya ta matsa dole Ummi ta kyaleta ta tafi,sakamakon iya hallaci hajiya tayi mata,dole ta barta tabi danta suka koma azaria akabarta da bakin Sudan.
Satinsu daya da zuwa mu”azzam yaje office dinsu ya cike takardan,dawowa aiki,hakika sunji dadin dawowarsa domin babu shakka,Mu”azzam zakwakuri ne,kuma jajirtacce ne abangaren aiki,domin rasashi shikadai kamar rasa ma”aikata goma ne,shiyasa ake ta murna da dawowarsa mooh ya rakasa,wanda shima yaga tsabar murna da fatan Alherin da ake zubama mu”azzam,lokaci daya Mooh yaji komai na rayuwar mu”azzam ya burgeshi ainun har yanajin zaiyi koyi da kyakyawan dabi’unsa.
Mu”azzam ya matsa su je maiduguri,saboda yaga jikin Baffa,wanda tuni dama lbrin dawowar mu”azzam din ta ishesu,har bukar da kanshi ya kirashi,suka gaisa yana mai murnan dawowa,mu”azzam yaji ba dadi,ammh shi bukar din ko ajikinsa,sai ma tambayansa dayake yaushe zaizo,nan yake fadamasa cikin Satin nan zai shigo.
Satinsu biyu cif da zuwa suka shirya zuwa maiduguri,mota biyu sukayi,mu”azzam da kanshi yayi driving dinsu zuwa maiduguri,shikuma ushe ya janyo su Ummi da lubna da Mom,sai da Yakura taga baki daga sama,fadar irin murnan dasuka shiga bata lokaci ne,haka mu”azzam ya rumgume Baffa yana tsiyayan hawaye ganin halin da Wan mahaifnsa,yake ciki wanda yake kallon a mtsayin mahaifinsa,Baffa shettima yayi murna sosai da dawowar mu”azzam haka ya zaunar dashi yanatamai Fadan yadda da kaddara da kuma hakuri da rayuwa,nan nema Ummi ke gabatar da Lubna amtsayin matar Mu”azzam ta biyu,baffa da Shettima sukayita saka albarka,domin babu yarda zasuyi da abunda Allah ya kaddara.
Daga gidan Shettima gidan bukar suka nufa,wanda shima yaji dadin ganinsu gabadaya nan aka zauna ana maida zence,ana bawa mu”azzam tare da mai Nasihan hakuri da kaddara,nan ma Ummi takara gabatar da Lubna amtsayin matar mu”azzam din,Bukar yaji dadin haka,yayi ta sakama auren albarka,mahgana kuwa sai da tayi kwallah,domin tatuna ko kwanaki dataje gidan zahirah sai da ta tambayeta ina lbrin mu”azzam tace mata haryanzu Shuru tana hawaye tace Allah ya bayyanashi,tsausayin duka rayukan yakamata,tasulale takoma daki tana share kwallah,ta sani daga mu”azzam din har Zahirah sunyi aure ne,kawai,ammh ruhinansu suna tare da juna.
Bukar ne ya Umarci mahgana tatashi taje gidan zahirah Ta karbo Su little Ummi ta kawoma babansu yaga diyansa,Ummi najin haka ta mike,tace zataje,lubna ma tace zata mom ma ba”a barta abaya ba,Mu”azzam ko na gefe kusa da mooh ko daga kai baiyi ba,yanaji yana gani suka fice daga gidan ushe zai kaisu,Bukar ko Da Abbie suka tsinke da lbaran Duniya mu”azzam ko zaune kawai yake ammh kirjinsa nauyi yakemai,ga zufa tana ketomai ta ko”ina bayaso agane halin daya cike shiyasa ya kara sanda kai ya dafe kanshi dayake saramai lokaci daya zuciyarsa na amsawa, Zahiransa ce agidan wani? yaransa ma in zai gansu sai dai adaukomai su? Hakika zuciyarsa bazata iya daukan wannan kaddarar ba.