UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dawani firgici Zahirah tadago daga jikin Ummi tana bin inda Mahgana tana nuna mata,kur tayima lubna da ido tana kallonta hawaye yana kwarara bisa fuskarta muryanta na rawa tace”Ya…yi…Au…re….? tafada bakinta da muryanta suna rawa kai mahgana ta gyadamata tana fadin”kwarai da gaske,kinga kenan dukkanku baku isa chanza kaddaran Allah ba..”
Kara kurama Lubna ido Zahirah tayi kafin ta dauke kai tana kakaro mirmishi tace”To mai zai dameni,bayan nima nayi auren ai bazanyi bakinciki ba don Ya mu”azzam yayi aure don yasamu Farinciki ba,kuje ku kaimasa ya”yansa ku fadamasa cewa Hiransa tayi matukar kewarsa kuma bazan taba daina Sonsa ba..”tafada tana gunjin kuka kafin ta ruga daki ta rufe kofa tana kuka.
Gabadaya jikinsu yayi Sanyi Lubna takara rumgume Little Ummi dake hannunta tana digan hawaye,Ummi ma dabas takoma ta zauna tana fadin”Nice sila,wlh duk laifi na ne,taya ya zanji dadin rayuwa alhalin zuciyoyi guda biyu suna azbtuwa ta dalilin son raina..’Tafada tana tsiyayar hawaye Mahgana ce tace”Ba laifin ki bane hajiya,Wlh Haka Allah ya tsara sai hakuri kawai ammh abun akwai tsausaya gaskiya..”Tafada cikin jimami.
Mom tayi tagumi tana bin moodu dake jikinta da kallo tsausayin iyayan na ratsata,Lubna ce tafara tashi ta fice dauke da little ahannunta tanajin tabbas tayi katsaladan na shigowa rayuwar Mu”azzam duba da yadda rayuwarsa ke ciikin dabaibayi,mata kina gidan mijinki ammh baki bar begen wani ba,lalle duk inda so yake yakai,Dole Ummi da mom da mahgana suka rufamata baya suka fice suna zuwa suka shiga mota ushe yaja suka fice daga gidan.
Inda suka barsu nan suka samesu acikin falon suna zaune suna fira,Ummi ce kan gaba dauke da moodu bayanta kuma lubna ce dauke da Little Ummi,Koda sukayi sallama Mu”azzam bai daga ido ya kallesu ba,sannu da zuwa Abbie yake musu kafin Ummi ta mikamasa moodu,kin amsa yayi yana fadin”fara mikasu ga mahaifinsu Tukunna Suhaima..”Yafada yana nunamata mu”azzam.
Cikin wani sanyin jiki Ummi ta isa kusa dashi ta duka ta ijiyemai moodu bisa kafafunsa,wanda ke wasansu na yara,Lubna ma ta kariso ta duka zata ijiyemai little Yayi Saurn dagowa,yadda idanunsa suka kada e,yasa hankalinsu ya tashi cikin wani yanayi Ummi tace”Son..Wht wrong with u..? bai bata amsa ba yace ma Lubna”Riketa..”kawai ya iya fada domin kansa ne ke juyamai.
Kurama yaran ido yayi yana kallonsu yadda sukayi wayau,suma kamar sunsani suka zuramai ido suna kallonsu,hawaye suka taru a idanun mu”azzam wanda suka kwaranyo har bisa fuskar yaran”hannu yasa ya dafa kan moodu yana mai addu”a kafin yakoma ga Ummi itama yamata addu”an ammh fa yakasa tsaida kwallarsa,kokarin fashewa da kuka yake na tsausayin kanshi ga yadda zucuyarsa ke suya tana fat!fat!kamar zata faso kirjinsa ta fito cikin wata irin murya yace”Daukesa Ummi kada yafadi..”yafada yana rike hannun yaron wanda yako damke kamar yasan kowanene.
hannu Ummi ta mika ta dauki moodu tana kallon Fuskar Mu”azzam din wanda yayi Saurin matswa baya kafin ya mike yana kauda kai,kuka ne ya tahomai shine dalilin daya sakashi mikewa da sauri ya fice daga falon yana hada hanya hannunsa duka biyu na bisa kansa,da kallo kowa ya bisa na tsausayinsa,ajiyar zuciya Abbie ya sauke kafin ya karbi yaran yayi musu addu”a shima sai da yayi kwallah,mooh ma sai daya daukesu yaji wani sabon tsausayin mu”azzam ya tasomai wayyo,Allah ya so,Bukar ma shuru kawai yayi baida ta cewa domin bakin alkami ya riga ya bushe,itako Ummi duk ta tsargi kanta gefe takoma tana sharban kuka Lubna ce take bata hakuri itama neman mai lallashinta take,domin tayi weak sosai game da soyayayyar mu”azzam,kuma ayanayin daya fita tana tsoron tashi ciwonshi.
Basu wani jima ba suka mike bayan Ushe ya shigo da uban siyayyar da mu”azzam ya narkama ya”yansa ciki harda zahirah bai manta ba itama ya siyomata dogayen riguna masu kyau,Abbie ya kara musu da kudi shida mooh,sallama sukayi musu,domin mu”azzam Tundazu yake kiran waya akan suzo su wuce domin yace yau zasu koma Abuja bazai iya kwanan maiduguri ba.
Atsattsaye sukayi sallama da su yakura bayan sun koma gidan baffa,shima sun cikasa da abun arziki kafin su mika hanya,karfe 7:00pm na yammah Suka dauki hanyar Abuja,wanda shikanshi baffa yayi fadan yadda zasubi dare,su tsaya su kwana mana,gobe sai su koma,ammh mu”azzam ya kafe dole sukaka bawa baffa hakuri suka kama,hanya wannan karon mooh ne yajasu domin mu”azzam baizai iya ba,ammh kuma yakasa fadi,Abbie ne ya kula da yadda yake yawan dafe kai,shine ya umarci Mu”azzam din daya bama mooh driving din.
Sunyi gudu sosai karfe 12:00Am suka isa gida,ammh azahirin gaskiya sungaji ainun shiyasa suna zuwa kowa yanemi makwanci dayake sun tsaya bisa hanya sunyi sallah,Mu”azzam dai yadda yaga rana haka yaga dare,barci ko barawo bai daukesa ba,yana kwance yana fama da kansa na jinyar zuciyarsa yanaji aransa kamar ya rasa zahirah kenan har abada.
Mahgana na shirin dawo dasu Little dasuka fara rigima sai ga Alhaji kabiru yazo daukansu da kansa domin koda yakoma gida,dayake daman yagana bata wuni agidan ba,shiyasa yasamu saken shiga dakin zahirah ya sameta kwance taci kuka ta koshe,tuni zazzabi ya rufeta,dama ga nononta sau kumbura sunyi him sai zuba suke bamasu sha ganin halin datake ciki ne yake tambayanta,bazata iya mai mgana ba,shiyasa tamasa banza falo yakoma yakira zulai yana tambayanta ita kefadamai anzo an tafi da yaran ne,to shi azatonshi ma ko an kwacesu daga hanun zahirah ne,ganin yadda taketa kuka,sai dayaje,bukar kefadamai cewa babansu ne yazo ganinsu,yanzu mahgana ke shirin maidasu wajen uwarsu,Alhaji yaji sanyi aransa na ba tunaninsa na farko bane,domin shima ya saba da yaran bazai iya rabuwa dasu ba,amsan su yayi kafin yayi musu sallama yakoma gida.
Yana kaimata su suka fara kukan nono dole ta basu,daman duk dashi ya sakamata zazzabin suna ko sha sai barci itakuwa dakyar ta fada toilet tayi wanka,saboda yadda kanta ke saramata,Alhaji dai tana tunanin Uwarsa yagana ta dawo domin tunda ya fita yacemata bari yazo bata kara ganinsa ba sallolinta ta rama,kafin tanemi paracetamol tasha ta bi lafiyan gado tana addu’a acikin ranta gefe daya na zuciyarta na bata karfin gwiwan hakuri da halin rayuwa.
Comment
Share
Vote
Janafty
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)
Mallakar:JANAF
Wattpad:Janafnancy12
Dedicated to my blood Sisters JANAF
GIFT TO:Hussain80k
Intelligent writer’s Asso✏
NOT EDITED????
NO 39
“””Koda garin Allah ya waye,Mu”azzam kasa tashi yayi Saboda yadda jikinsa yayi sanyi,ga ciwon kan dayake damunsa tunjiya,kansa yayi masa Nauyi,koda mooh ya tambayesa meke damunsa,cemasa kawai yayi kansa ke ciwo,yamai sannu.
Dannewa yake,yaki bari sugane halin dayake ciki,ko Ummi data shiga wajensa ta rude tana tambayansa maiyake damunsa,amsamata yayi da cewa bakomai,kansa kawai ke ciwo kuma yasha mgani insha Allahu,,zaiji sauki,Ummi duk tatashi hankalinta koda lubna tazo,kallo daya tayima mu”azzam tafahimci Ciwonsa yakeso ya tashi ammh bayaso ya nuna,batamai mgana ba sai da Ummi ta fice,tataka ta isa kusa dashi tana fadin”ya mu”azzam plz kabari na dubaka,Ciwonka nanemam Tashi..”