UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Ko kallonta baiyi ba,illa juyamata baya dayayi yana fadin”It ok,ni lafiyata kalau,karki fadama Ummi komai na rokeki..”yafada cikin sanyin jikin,Daganan ya runtse ido kamar yayi barci saboda bayason Damuwa,dole yasa Lubna taja jikinta tafice daga dakin Jikinta duk asanyaye.

     Sai zuwa yammah ya samu ya fito adaddafe,yana kokarin nuna yaji Sauki,nan ko ko dan tafiya yayi sai yaji jiri ya kwashesa,ga tsananin ciwon kai dayake addabansa,Su Ummi a idonsu yana nuna musu yaji sauki,itako lubna tariga ta sani Ciwonsane ke son tashi,kuma yaki yarda adubasa,ammh yana zaune da ciwo.

    Kwana uku yayi yana fama da ciwo babu wanda ya sani,kuma awashegarin ne,su Abbie zasu koma chan Sudan din,saboda daga chan ma”aikatan Su mooh din ana bukatarsa cikin gaggawa,adaren dazasu tafine,Abbie ya tarasu yana musu nasiha shida lubna,yafadama Ummi ga lubna nan za”a barta wajen mijinta,mganar aikinta kuwa Abbie yace ga takardunta nan In mijinta ya amince sai ya nema mata wani aiki anan,domin yanzu tana karshinshin kulawansu ne ga amanarta ne yana fatan Allah ya zaunar dasu lafiya.

  Shiko Mu”azzam,Abbie yayitamai fadan tare da umartansa daya maida hankalinsa wajensa,aikinsa yakuma kula da kansa da lafiyansa,tunda yasan halin dayake ciki,ya amsama Abbie dayaji kuma insha Allahu,zai maida kai wajen aikinshi,kuma yayimai alqawarin maida hankalinsa ga aikinsa,kuma amanar lubna ya karba Allah yabashi ikon Sauke Nauyin dake kansa.

Washegari suka rakasu Airport,jirgin ya kwashesu zuwa sudan,wanda lubna tayi kuka,sosai ta rumgume mom tana hawaye,hakuri mom tayi ta bata,domin itama kukan takeyi,shikanshi Abbie sai da yayi kwallah,Dakyar dai suka rabu cikin kewa da sabo.

BAYAN SATI DAYA

   Acikin Satin Mu”azzam yakoma bakin aiki ba zama,kodon yaragema kansa damuwar datake addabansa,ba laifi yaji sauki,tunda ya daukanma kansa alqawarin zaiyi tawakalli yamaida al”umuransa wajen Allah,aikin daya koma sai yarage masa yawan Tunani,satin dayakoma yacikaro da wata shari”a mai sarkakiya Wata matace ke karan yayan mijinta,ya cinyemata dukiyanta dana ya”yanta wanda mahafinsu ya mutu ya barmusu,to shikuma shiga kotu na farko yazo da Shaidun komai,marigayin kafin ya rasu sunyi wata yarjejiniya har ya mallakamai duka dukiyan,to ya fadi yarjejeniyar yakama kame kame,wai yayima marigayin al”qawarin bamai ji,to Shari”ar ta rikice ainun tana bukatar dogon bincike Shiyasa ya maida hankalinsa waje guda,bai samun lokacin kansa ma balle yayi Tunani duk da Hirah na nan acikin Ransa bazata ta taba fita ba,in yafita tun safe sai dare yake dawowa,wani lokacin ma sai Ummi tatashi gaba yake cin abinci,itako lubna tana gefe domin tsakaminta dashi gaisuwa bayan nan babu abunda ke hadata dashi,abun na damunta ko tanemi tayimai mgana ya tankata ko zataji dadi,baya sakarmata fuska,wani lokacin daki take shigewa tayita kuka ita kadai,tana tuna da ace ita keda iko da kanta,wlh da tuni ta yakice soyayyar mu”azzam aranta.

Ummi kuwa tana lura da takun sakan dake Tsakamin ma”aurantan biyu tadai yi musu bakam ne,kuma bakomai bane dalili sai Yanzu kwata kwata batason Tursasa mu”azzam yin wani abu matukar bashi yayi ra”ayi ba,Lubna na bata tsausayi ainun ammh bata da yarda zatayi domin abaya tayi amfani da karfin biyayyah dayake mata ne,ta sakashi aikata abunda yazo yana damunsu dukansu,shiyasa bata kaunar sakashi wani abu wanda bai yi niyyar ba,tana gani Tun bayan Tafiyar iyayan Lubna asama suke kwana tare da ita kuma itakanta yarinyar ramewa kawai take atsaye.


   Yau takama Monday ne,Tunsafe mu”azzam ya fita bai dawo ba sai dare,yana dawowa ya tarar da Lubna zaune afalo cikin doguwar riga kanta babu dankwali ta bazo gashinta harzuwa gadon bayanta,Sannu da zuwa tayimai ta mike da niyyar amsar jakarsa ammh sai ya dagamata hannu kawai ya wuce dakinsa bai ko kalli barayin datake ba,da kallo Lubna tabishi idanunta sunciko da kwallah.

Komawa tayi ta zaune tana kokarin maida kwallar data ke kokarin saukomata,remot ta dauka ta sauya tasha zuwa MBC3 ,Ummi ce ta sauko daga sama cikin riga da zani na wani leshi mai kyau da tsari tun daga nesa ta hango Lubna nan Ranta duk babu dadi ko bata tambaya ba,tasan bai wuce ita da mu”azzam ne.

   Karisowa falon tayi tana kallonta,Da Sauri lubna tace”Sannu da Fitowa Ummi..”
 

   “Yauwa Dota,kina nan ashe.? Ummi ta tambayeta tana kallonta dariyan yake lubna tayi kafin tace”Eh Ummi ina kallo ne” To yayi kyau”Ummi ta bata amsa kafin lokaci daya tace”Armm Son ko yashigo..? kallonta Lubna tayi kafin tace”eh ya shigo Ummi yanzu bada dadewa ba..”

   Ummi ta mike tana fadin”Ok bari na dubasa don naga kwanan nan yana wasa da cin abinci..”da kallo tabi Ummi tana fadin”Gaskiya kam..”Tafada ranta na kuna,lokaci daya tana kure Ummi da kallo harta Shige shashen mu”azzam din,kafin ta maido da kanta bisa babban talabijin dake Falon,Ammh kuma idonta ne kadai ke kai,hankalinta baya tare da ita yanaga begen wanda bazata samu ba Wato Mu”azzam.

  Da Sallama Ummi ta shiga bayan Ta tura kofar,baya falo sai ta danganta da bedroom din ta tura tashiga tana mai sallama,yana zaune bisa gado,ya tasa system dinshi gabansa gefe daya kuma wasu takardu ne,birjit agabansa,yana ta aiki bisa system din,gefe daya kuma yana ta duba takardun dake gabansa

  Cikin kasala yadago kansa lokaci daya yana amsama Ummi sallamanta,karisowa tayi ta zauna kusa dashi gefen gadon tana fadin”Son..”Zubamata ido yayi yana fadin”Ummi..”Yafada yana sosa kansa,dafa kafadansa tayi tana fadin”Son kana zurfafama kanka aiki da yawa gaskiya,kasan kuma baka da ishasshiyar lafiya ko? kuma gashi yanzu bakasan cin abinci sam..”Tafada tana shafa kansa har zuwa fuskarsa.

  Lumshe ido yayi kafin ya bude ture System Din dake gabansa yayi kafin ya matso kusa da Ummi yana riko hannunta yana fadin”Ummi,case dinnan yana bukatar bincike da natsuwa kuma karki manta aiki nan shine Farinciki na da takama na,Akwai mutane dadama dasuke so su taka mtayina ammh Allah bai basu dama ba,to meyasa ni nasamu dama bazan yi amfani da damana ba,ko so kike na bari lokaci ya kuremin..”yafada yana lamgwabemata kai.

  Mirmishi tayi tana shafa kansa tace”Daz my Swt son..Shiyasa nake alfahari dakai,ko a ina Son dina yafita dabam da Sauran maza,ayita aiki amaida hankali,Allah yayi maka jagora..”Tafada tana buga bayansa,kwantar da kansa yayi akan kafadanta yana fadin”Mganar abinci kuma,inaci in naje office Ummi na,kuma u already know banacin abinci mai Nauyi in zan kwanta sai Ruwan liptop..”Gyada kai Ummi tayi tana fadin”hakane,ammh nidai bamison kana wasa da cin abinci son,baka ga yadda ka rame bane,ko bakaso kamaida jikinka ne”tafada tana mai dariya,shima dariyan yake yana rumgmota.

  Sun dade ahaka tana rumgume dashi tana shafa bayansa kafin tadagosa tana fadin”Son tashi muyi mgana..”,,tafada da alamar mganar mai muhimmanci ne,gyara zama yayi yana fadin”,Toh Ummi nah..”Riko hannunsa tayi tana fadin”game da yarinyarnan ne Son..’Tafada tana kallonsa
 

  Yamutsa fuska yayi kafin yace”Wata yarinya kenan Ummi”?yafada da tsigar tambaya,rausayar dakai tayi tana fadin”Lubna mana..”Kuri yayima Ummi da ido kafin yace”Meya faru da ita..? matse hannunsa Ummi tayi tana fadin”babu abunda ya faru da ita yanzu,ammh in kacigaba da banzarta da ita,wani abu zai iya samunta nan gaba,Son ada naso bazan kara tursasaka kayi wani abu wanda bakayi niyya ba,ammh yazama dole duba da ga yarinyar da hallarcinta gareka,uwa uba ga girman hakkinta dake wuyanka Bani son Allah yakamaka da danne Hakkin aure..”Tunda Ummi tafara magana Mu”azzam ke kallonta yakasa cewa komai sai da tagama takallesa taga yana kallon hannuwanta dake cikin nasa,ganin haka yasata cewa” Kaji Son,bani so Tursasaka ne,but yazama dole..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button