UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mikewa tayi afirgice Hannunta bisa kirjinta tace”Ya..ya..Mu..az…zam..”Tafada kamar bata yadda da Shidin take gani ba,saboda yadda ya ramemata a ido,sai dai yakara fari da tsawo,kallonta yake yana cije lips dinsa,lokaci daya yafara takowa zuwa gabanta Fuskarsa babu fara”a ko kadan Ja da baya Zahirah ta hauyi tana kallon yadda mu”azzam yawani hade rai Sai da yakaita bango kafin taja ta tsaya kuramata ido yayi yana kallonta,Itama Shi take kallo ammh jikinta na rawa,Hannunsa yasa ya dafa bangon wajen yana kara kusantota har jikinsu na gogan juna,Fuskarsa ya ja zuwa gareta Saurin Runtse ido tayi saboda yadda taji gabanta na fadi Fat…Fat..Fat.

Jira take taji saukan mari,ammh sai mai sai taji Shuru Bude ido tayi tana kallonsa yadda ya kuramata ido lokaci daya idonsa yajanza kala,,tuni jikinta Yayi sanyi takuramai ido hawaye suna taruwa a idanunta,Bai mata mgana ba,sai kallonta kawai yake yana cije baki,Hawayen da zahirah ke Rikewa su suka zubomata,hannunsa na rawa ya saka ya dalle mata baki yana fadin”wannan bakin ne yace bazai koma gida na ba,shine yace baya bukatata alhalin ni ina chan,kullum ina fama da cuta,ko tari nayi sai jini ya zubo,why My hirah,kina so zuciyata ta bugane..”yafada Idanunsa sunyi Raurau,Kuka kawai Zahirah ta fashe dashi tama kasa mgana,kallonta yayi kafin yace”Ni banyi kuka ba,sai kece zaki wani Fashemin da kuka,Allah kimin Shuru ko na matse miki baki yanzu nan.”Jin haka yasata karama Volume din kukanta,baiyi wata wata ba,ya rumgumota kam ajikinsa,lokaci daya suka saki ajiyar zuciya,Kamkameta yayi yana Shinshinar wuyanta Cikin wani kasala yace”I miss u ..”yafada yana dora kansa bisa kanta wasu zafafan hawaye na ziraromai

Jin hawayensa na diga abayanta ya sata kara kara kamkamesa tana fadin cikin kuka”Mi…ss..U…Tooooo…”tafada tana kara tusa kanta akirjinsa,kamkam suka damke juna tamkar wani zai rabasu,Dukkansu hawayen Farinciki suke na murna sake ganin juna arayuwa,Sun manta da kowa da komai,kawai duniyar ne ke juyawa dasu Saboda farinciki Suna cikin halin Rumgume da juna,Sukaji kukan Little wacce tatako ita zatayi Tafiya sai tafadi ta buga kanta,tako kwala ihu,moodu najin kukanta Shima ya tako sai Shima ya kifa,kukansu ya ruda iyayyan nasu suka saki juna da Sauri kowanne na rige rigen zuwa garesu.

Comment
Share
Vote

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED????

         NO 43

   “””Shiya samu Nasaran Daukan little Ummi ita kuma ta dauki moodu,atare suka rumgumesu suna lallashinsu lokaci daya suna kallon juna,mirmishi zahirah Ta sakarma mu”azzam shiko ya ballamata harara kamar zai daketa,Kauda kai tayi tana yar dariya kafin ta koma kan kujera ta zauna tana Cigaba da lallashin moodu,ganin sunyi ki yin Shuru yasa mu”azzam takawa zuwa inda Zahirah take yana kallonta yace,”Malama ki bude riga ki basu abincnsu yunwa sukeji..”yafada Yana wani cin mgani.

  Dagowa tayi tana kallonsa kafin itama tace”yanzu fa suka gama sha,babu yunwar dasuke ji Faduwar dasukayi ne Rigimarsu tatashi..”Kuramata ido yayi kafin yawani zaro ido yana fadin”ke ina wasa dake ne? yarinyarnan fa wlh kin fara rainani zaki basu kokuwa sai na danneki na basu dakaina..”yafada Yana danne dariyansa,Tura baki tayi tana fadin”to..To agabanka ne zan bude riga,sai dai ka fita waje,ko ka juya baya..”Tafada tana kifkifta ido.

  Dariya Taso kwacemai bai san Sadda ya rike baki yana fadin”kaji min yarinya da sanabe,yo Allah na tuba Shi abunda bakison naganin inace ba agabana ya ida girma ba,kinga wlh ki bashi nono yasha ko na saba miki”yafada adole Shi miji kuma babba????Zahirah tayi nakwa nakwa da Fuska kafin ta zage zif din Rigarta tabaya ta ciro nononta guda daya kamar tayi kuka ta turama Moodu abaki tana fadin”Ai daman kadaina sona,kuma ma haushi na kakeji tunda yanzu kasamu wacce tafini balarabiya niko baka dani..”Tafada hawaye na digomata bisa Fuskarta.

  Kuramata ido yayi yana kallon yadda take goge kwallah tana bama Moodu nono,Zama yayi akusa da ita yana kallonta yakasa cemata komai ba,illah kuramata ido dayayi yana kallonta ransa na kuna,Tana gama ba moodu ya mikamata little Shikuma ya rike moodu,sai da tabasu suka koshi kana tamaida rigarta harta gama,tana share kwallah kuma taki kallonsa,suna jikinsa yaran Sukayi barci Shimfidesu yayi kan 3siter,din kujeran dake kallonsu ya mike yazo gabanta ya tsaya yana kallonta kafin yasa baki ya kirata cikin wata irin murya.

    “ZAHIRAH….”Yafada Numfashinsa na sama da kasa,jin muryan dayasa yakirata yasata dago kai Tana kallonsa,Idonsa sun kala sunyi jawur ya nuna kansa yana fadin”Tunda kikabar rayuwata,Na tagyara rayuwata ta durkushe,na rasa walwalata,dariyata,Annurina,komai nawa ciki harda aikina,saboda ke na bar mahaifiyata da kasata baki daya,na bar dukiyata da yan”uwa natafi inda bani da kowa nayi rayuwa duk don saboda ke!Saboda ke naki zama lafiya kullum cikin allurai nake da shan magunguna,Saboda ke nakasa kallon Lubna Amtsayim mace awajena,Saboda ke banta kallonta da Sunan soyayyah ba,Saboda ke nadaina barci Saboda son da nake miki naki zama lafiya,adalilin sonki na saka rayuka dadama cikin kunci Saboda ke nashiga gararin rayuwa,Saboda ke na aikata komai,wlh Tallahi,..inda bana sonki Bazaki Auri wani yaketa inda naketaba,kuma nasake marmarin Kusantoki gareni domin sake komawa gonar dawani yayi nomarsa aciki ba,Dabana sonki bazaki taba gani na anan ba….”

   Ya fada yana juyamata baya daidai lokacin da wasu zafafan kwallah suka zubomai,Jikin zahirah daya gama yin sanyi ta dukar dakai tana kuka,ta mike tana danne bakinta da hannunta kafin ta durkusa bisa gwiyoyinta kafin Tace”Don Allah ya mu”azzam kayi hakuri nasan nayi kuskuran fadan cewa baka sona,wlh bada gangan bane,nikaina Banson dalilin dayasa nakejin wani zafi ba duk sanda na tuna kana da mata ba..”Tafada ciikin kuka kafin tacigaba da fadin”Wlh duk karyace nake fada,tunda muka rabu,bantaba jin nadaina sonka ko na minti daya ba,na yarda na amince don kai kadai akayi ne,zan koma gidanka akaro na biyu na bautamaka na kuma sakaka farinciki har karshen rayuwata…”Tafada kuka yaci karfinta.

  Saurin juyowa yayi yana rikota Lokaci daya ya sakata ajikinsa yana fadin”kibar kuka don Allah my hirah,kukanki daidai yake da barazanar daukewar Numfashina.,na hakura dama ni baki batamin ba am sryy kinji na sakaki kuka..”yafada yana dagota lokaci daya yana sharemata kwallah,Lafewa kawai takarayi tana sakin ajiyar zuciya,sun dade ahaka,Zahirah ce ta tuna da cewa idda takeyi Shiyasa tayi zumbur ta kwace jikinta tana kallonsa shima kallonta yake kafin yace”meya faru?

  baya taja kafin tace”Idda nakeyi fa,Haramun ne Kama junan da mukeyi..,”Tafada tana sadda kai ,Tamke Fuska Mu”azzam yayi kafin yace”Jini nawa kika gani..?dagowa tayi tana kallonsa kan tace”Ko daya baizo ba tukunnah..”zaro ido mu”azzam yayi kafin yace”wht?na shiga uku, kardai knje kin sakin mai jiki ya dura miki ciki..”jin haka yasa gaban zahirah faduwa,dagowa tayi lokaci daya idonta ya ciko da kwallah,girgiza kai tayi kafin tace”a”a insha Allahu ma ba haka bane..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button