UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

ajiyar zuciya ya Sauke kafin ya koma ya zauna Jingina kansa yayi da cussion din kujeran kafin ya lumshe ido,ganin haka yasata fadawa kichen,Katon tire ta samu ta zubomai fankasau din datayi da safe da miyar ganda,sai lemon kwali,da Ruwan Faro,takawomai Center table din dake tsakar falon ta ja zuwa gabanshi ta ijiye Tana fadin”ga abinci da Ruwa yaya..”bai dago ba,kuma baiyi mata mgana ba,ganin haka yasa takoma kujeran dake kallon nasa ta zauna ta rafka tagumi tana kallonsa,Sai da yagaji da kansa ya dago ya gyara zama ya tsiyaya ruwan ya sha,abincin ma kadan yaci,kuma tundaga sannan bai Kara yimata mgana ba,daga karshe wayarsa ya fito dashi yakira Shureim suna mgana,bayan sun gama dashi ya kira mooh daga Sudan sukayi mgana kafin Suyi sallama.
Mahgana ce ta fara dawowa,Tayi murna da ganin mu”azzam har hakan yakasa boyuwa aranta,ta furtamai tana mai barka da arziki,ya amsamata Shima cikin sakin Fuska da girmamawa,Dawowartane yasa Zahirah komawa daki tayi wanka,tazo ta amshi su little daga hannusa Domin Sun tashi tun dazu,taje tayi musu wanka ta sauya musu kaya,sai gabda mangariba,Kana bukar ya dawo Shima yayi mamakin ganin mu”azzam din ammh sai ya shanye mamakinsa sukayi musabaha bayan sun gaisa,nan yake fadamai Tun safe yazo gidan babu kowa sai Zahirah,Jinjina kai bukar yayi ko Afuska bai nunama Mu”azzam din komai ba,shima baimai wata mgana data dankanci zahirahn ba,dama shikanshi bukar yasan Fade kawai take,ammh ai dukkansu bamai iya gujema dan”uwansa.
Tare sukatafi mallaci Sukayi sallar mangarib da Bukar,suna dawowa Mu”azzam yayi musu sallama ya tafi gidan Baffa shettima,ammh kafin ya tafi sai da ya amshi wayar zahirah ya sakamata sabon layinsa,bayan ya cikata da kudi,suka rabu cikin kewa da son juna,tayi tayi da safe ya dawo kan ya wuce,ammh yaki yacemata bazai dawo ba,saboda kada su shiga hakkin Allah,haramun ne mace na idda ta dinga kebewa dawani namiji,ko yanzu ma dayazo don takamane,shiyasa dole ta hakura ammh Zahirah Harda dan hawayenta tace agaida mata da Ummi da lubna yace zasuji.
Baffa da yakura suka ga mu”azzam da daddare,nan yake shaida musu Tun safe yazo,yana gidansu zahirah,dariya kawai baffa da yakura sukayi basu ce komai ba,Nan gidan ya kwana sai washegari tun safe suka dau hanya,bayan ya cikasu da kudi,dayake tun bayan dawowarsa ya dauki nauyin wani likita dayake zuwa gida duk sati yana duba Baffan,babu laifi jikin da sauki Tunda yanzu ana mai gashin kashi,yanzu yana iya motsa hannuwansa da kafafunsa kuma bakinsa ya bude,jiki dai yayi kyau domin mu”azzam ya saki kudi sosai game da ciwon baffa,bangaren kudi da abinci basu da wata mtsala sukan Domin mu”azzam baya barinsu haka,koda bayanan Shureim yamaye gurbinsa,balle yanzu daya dawo bai gaza ba ko kadan.
Koda yakoma gida Baifadama Ummi komai ba,ammh afuskarshi ta fahimci ya samu kwanciyar hankali,bata tambayeshi ba,shima bai cemata komai ba sakon gaisuwan da zahirah tabashi yafada,dakuma sakon su yakura na agaishesu sosai,washegari kuwa yakoma wajen aiki domin kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa ta gushe,yana kiran zahirah ammh sai bayan kwana bibbiyu saboda yaji lafiyarta data yaransa,basa wani dogom hira sai ya yanke,domin bayaso ya zura jiki,domin Shine zai sha wuya.
Kwana ashirin da biyar da Sakin zahirah ammh Shuru bata ga period dinta ba,hankalinta yatashi sosai tana fargaban kada ace ta samu cikin Alhaji da shikenan an gama da ita,tashiga tashin hankali da zullumi sosai saboda tasa abun aranta,Jinin farko baizo mata ba Sai da ta kwana talatin Cif cif kafin ta gansa da yammah,ai data da gansa batasan sadda ta daka tsalle daga bandaki ba tana ihun murna,har sai da mahgana ta shigo tana tambayan lafiya,rumgumeta tayi tana fadin”period dina ne yazo,wayyo na godema Allah”
Rumgumeta mahgana tayi tana fadin”murna banaki bane kedai hardamu Allah mun godemaka da baki samu ciki ba..”Dariya zahirah Tayi kafin mahgana ta fice ta barta da hanzari ta rarumi wayarta ta Kira yaya mu”azzam,shiko lokacin yana falo suna hira da Ummi,lubna na gefe kiran na zahirah ya shigo wayarsa yadaga tunkafin yayi magana ta daka tsalle tana fadin”Albishirinka yaya mu”azzam…”tafada cikin murna gyara zama yayi yana fadin”Makullin mota yar yayi,fadamin naji meya faru ne..,?”dariya tayi kafin tace”Yanzu naga Period dina yazo..”Ware ido yayi kafin yadanyi ihu yana fadin”Yes…Alhamdulillah nagodemaka Allah na sonah..”yafada yana bayyanar da murnansa,ganin yadda Lubna da Ummi suka zuramai ido ya sa ya mike yakama hanyar shashensa yana fadin”ammh Shine kike wannan tsalle,bani so karki ji ciwo kiman Asara..”yafada yana mata dariya.
Bata fuska tayi kamar yana ganinta tace”to kar nayi murna zan dawo wajen my miji,ok wato abunda nayi rashin hankali ne ko”?Saurin cewa yayi”Waneni da cewa gimbiya guda bata da hankali,tabdijam ai ba wanda yakai ki hankali,kinma Fini inaga..”yafada yana danne dariyansa don kartaji jin abunda yace ne,yasa ta tsintsire da dariya harda rike ciki,kansa ya hau shafawa yana fadin”muguwa kawai…”Yafada cikin kasala,gwalo tamai tanamai dariya kafin ta yanke kiran tana cigaba da murnanta saboda ganin zuwan jinin domin ko bakomai ta hango kamshin komawa gidan yaya mu”azzam dinta.
Tana yanke kiran,ya shiga cikin bedroom din ya fada bisa gado yanajin wata kasala na rufeshi,Runtse ido yayi yana shafa habansa,haka kurum in ya tuna da hiransu sai mirmishi ya kwacemai shi kadai ransa fes,domin yanzu Tuni ciwo yakama gabansa Tunda ya samu kwanciyar hankali,Abunda yakema ciwo yadawo mallakinsa,da wannan Tunanin daganan barci ya kwasheshi,ko awajen aikinsu anga cigaba domin walwalrsa ta dawo kamar da,yakoma aiki tukuri,brr mu”azzam ya dawo da Kasaitansa,da izzansa da komai nasa saboda rayuwarsa tafara daidaita,Lubna kuma tana iya bakin kokarinta wajen bashi dukkan kulawa koda bazai godemata,ita ta yarda ta amince haka kaddaranta yake,ita yanzu fatanta zahirah ta dawo kila abubuwa zasuyi sauki.
Zahirah takira Asma”u tana shaida mata dukkan Abunda ya faru,saboda tsausayin Zahirah da Farinciki sai da tayimata kwallah,tabata hakuri tace taso zuwa lokacin da suka kammallah Jarabawa bata samu dama ba,gashi yanzu tana Sokoto Usman dan Fodiyo Universty Tana karanta Medicine,ammh tayi mata alqawarin in lokacin maida auran yayi don Allah ta shaidamata zatazo,sun sha hira sosai kafin suyi sallama,duk da yanzu Asma”u ta lura kawarta ta takara gogewa aharkan rayuwa,duk yar kunyanan da Rashin sakin jiki duk ta ragesu,taji dadin hakan sosai kuma ta kudiri niyyar kara taimakon Zahirahn akaro na biyu.
“”Rayuwa tana tafiya tare da Ababen mamaki,Kowani bawa yana kwana yana tashi da buri ne,aransa Kwanci tashi kuma batabar komai ba,gashi har Yau ne zahirah take kammallah iddanta bayan tayi jini uku,Alhamdulillah duka zukata na cike da Farincikin barin ma Zahirah da mu”azzam ji suke kamar sunyi aikin hajji Saboda yadda suka samu natsuwar zuciya.
Mu”azzam yaso amaida musu Auren a washegari Ammh bukar yabashi hakuri,da cewa yabari sai sati ya zagayo jumma”a bayan an sauko daga sallar jumma”an sai amaida auren,duk da Ransa baiso ba yaji dadin haka saboda yasamu damar gudanar da duk wani Shirye shiryensa,domin Duk abunda basuyi ba a auren farko to wannan karan za”ayi bidi”a sosai domin wanchan karan ba”ayi murna sosai ba.