UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Shureim da Dr,Abduljabar sukace hakan nada kyau,nan da suka hada musu wata kasaitattaciyar dinner wacce za”a gudanar ranar Asabar da daddare,kuma zasuyi lunching achan bayan an daura aure,itako Ummi da lubna kasaitattaciyar walima suka shirya Suma Ranar asabar din,da safe,Abun ba ba”a cewa komai,domin mooh ma zaizo da shida mom daga Sudan Abbie dai bazai samu daman zuwa ba yace,Hajiya ma da zulaika sun shiryama Abun sosai don wannan karan Ummi ta wasa wukarta zata shiga ta fita domin bayyana murnarta,kayan auren kuwa ita da lubna suka tafi Dubai suka kwana biyu Suka hado Saitin akwatuna guda ashirin da biyu shake da kaya,Sha biyu na Zahirah Sha biyu na Lubna ne,mu”azzam fa yayi barin naira,ita Ummi ita kuma ta hadama Su little nasu akwatin shake da kayan alfarma domin suma ba”ayi musu na suna ba,Itama Zahirah Mu”azzam ya turamata da kudi Dubu dari biyu yace tayi hidimar gabanta,to suma su mahgana dasu ashe sunce baza”a barsu abaya suma sun shirya wata hadaddiyan Sister day dinsu ranar Alhamis,gyara kuwa Zahirah ta zare ba kama hannun yaro,tasha tayi wanka tayi Tsugunne,Ashe da mahgana basu barta ba,sun dage wajen gyarata ciki da bai,Itama kuma tana taimakon kanta da shan kayan Fruit babu wasa domin so take ta zautar da yayan nata abun ba Sauki fa,takowani bangare shirye shirye kawai keta kamkama tako”ina Saboda Abun ya karato.

    Ranar laraba,Ummi da hajiya da zulaika da lubna suka kai kayan Akwatina Maiduguri,sunga kara da karramawa da Mutumci wajen yan”uwan Bukar,an manta komai an zama yan”uwa sai wasa ake ana dariya,kayan sunyi domin an bata dukiya,sosai Kamar ba bazawara ba,Domin Shifa mu”azzam yace Shi budurwa zai Aura,basu kwana ba suka juyo gida suma da kayan arziki sosai na kayan toye toye da lashe lashe..Abun sai wanda yagani.

    Gabadaya gidan Mu”azzam ya gayyaci kamfani nan na MAKARI tazo ta sauya komai na gidan,hatta su kayan Na”ura saida aka chanza,dakin Zahirah ma komai sabo aka chanzamata tundaga bedroom har zuwa falonta,itako Lubna dakin kusa da zahirah itama aka Zubamata kayan alfarma iri daya dana zahirah sai dai bambamcin colour,Ita zahirah Black and ash ne,sai lubna black and red ne,Ranar alhamis da safe mooh da Mom Suka iso gida ya kaure da murna domin su hajiya tun ranar talata suke,Ummi ta fahimci haryanzu Mu”azzam bai kusanci Lubna ba,yasata itama ta shiga gyarata,domin har ga Allah bazata fifita zahirah akanta ba,itama gyarata tashiga yi domin kallon yarta ta cikinta take mata,su karime ko suma shagalinsu kawai suke da murna zahirah zata dawo akaro na biyu kowani ma”akacin 10th mu”azzam yaba kowannesu domin ya siya Abunda yakeso na biki,suka amsa suna murna tare dasa albarka,su uche ma ba”a barsu abaya ba,suma sunata shirinsu domin kowa fa ya shaida da yallabai yana cikin Farinciki.

Ana gobe Daurin Auren Abokan suka kammallah,Shureim da Dr,Abduljabar,da Mooh da ango mai gayyah mai aiki mu”azzam sun rigaya da sungama tsara komai,Wannan karon Tafiyan mota zasuyi,da yammah suka tashi mota hudu daya Ushe ke tukata empty benz din mu”azzam ne,sai 4matic motar Shureim,sai Corollah sai wata bakar jeep,da direban Shureim din shima ke tukata empty babu kowa aciki suka dauki hanyan maiduguri,basu isa ba sai dare wani kayatattacen Hotel suka kama suka sauka sukayi wanka suka huta kafin su isa gidan baffa shettima suka gaishesa basu samu Yakura ba tana gidansu zahirah,koda suka isa chan sun iske haraban gidan cike da al”ummah an gama Sister day din ba dadewa suka iso,Zahirah na dakinta cikin Shigar dogowar rigar abaya baka an mara rollin da bakin gyalen abayan,An mata make up tayi matukar kyau kamar ba ita ba, hannunta da kafanta yaji kunshi ja da baki yayi kyau sosai,Sai kawarta Asma”u datazo tun jiya daga mkranta wanda Mami ma ta iso yau domin ita ta kirata ta fadamata ba,sai ko gashi tazo domin tace ai zahirah yace awajenta,koda mu”azzam yanemi ganin zahirah Ashe ta hanata Ita da kanta tafita dauke da su little dakai musu tacema mu”azzam yayi hakuri sai gobe bayan Daure Aure zai ga zahirah babu yadda ya iya sai hakuri buh ammh an batamai bajet dinsa wlh,yaso yasa zahirah a ido saboda yadda tunaninta yahanasa sukuni cikin kwanakin nan data kashesa da wani salo in suna waya,wanda karatun Asma”u ne domin kwata kwata yar kunyar nan babu ita wajen zahirah domin yaga alamar wannan dawowar zata ida zauta shi ne gabadaya.

Asma’u ce tayi hidima dasu wajen abinci da abun sha,tana ma mu”azzam tsiya Shureim na tayata shida Dr,Abduljabar mooh ne yace yana bayan dan”uwansa,yana karemai ammh idonsa na kan Asma”un tunda ta shigo falon saboda yadda tatafi dashi,ko”ina tabi yana binta da kallo,tana lura dashi duk sai ta tsargu domin ba karya gayen itama ya tafi da ita basarwa kawai takeyi,goma daidai suka yi sallama Suka koma masauki, bayan Mu”azzam yabata an maidama zahirah su little Ummi yaran da sukafara tafiya da kafafunsu gwanin ban”sha’awa suma sun dau wanka cikin kayan kanti duk inda suka wulga sai an kara waigowa saboda Sha”awa.,.

RANAR DAURIN AURE

   Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Gashi tarihi yakara maimata kansa,amsallacin kusa da gidan baffa aka kara maida auren zahirah dana mu”azzam bayan asallaci sallar jumma”a dubban mutane suka shaida Daurin Auren nasu kan sadaki naira dubu dari,lakadan ba ajalan ba,Allahu akabar baffa da kanshi yakara yima dansa mu”azzam walicci akaro na biyu ,Awheelchair aka daukosa yazo wajen yakara nemamasa Auren zahirah akaro na biyu,Shikuma wan bukar ya basu shima akaro na biyu,ana gama tabbatar da Daurin Auren Baffa ya shiga share kwallah,wanchan karon bayan daurin Auren yayi kuka mai cike da fargaban,ammh na yau kukane mai cike da farinciki da Annuwasha tare Murna ya cika burinsa ko yau ya bar duniya.

Shiko mu”azzam Rumgume Shureim yayi yana hawayen Farinciki domin ada ya fidda rai da samun zahirah akaro na biyu sai gashi Allah ya sake bashi ita,bayan yakusa fidda rai,Allah sarki Alhaji kabiru yazo Daurin Auren na zahirah,kuma har gaisawa yayi da mu”azzam yana tayasa murna,Domin Bukar da kansa yakirasa yafadamasa maida auren zahirah dazaya gudana,Alhaji kabiru yaji takaichin rashin dacen da bai yi ba na samun Zuru”a daga zahirah ba ammh yabarma,Allah komai,yana tunanin kila baida rabon haihuwa ne aduniya,yagana Kuwa tuni alkadarinta ya fara karyewa domin yanzu Alhaji baya wasa da ibada,inna ma daga chan ta dage dayimai addu”a kuma ta sanya anamai,cikin lokaci yafara dawowa hayyacinsa itakuma yagana bata gane bane,domin baya nunamata komai,ko umarnin data saba bashi baya mata musu binta yake,ahaka lokaci kadai yake jira tagane bata da wayau domin kamar an farkar dashi daga barcin daya kwasheshi.

Comment,share,and vote

    “Janafty”
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED????

           NO 44

     “””Daganan wajen Daurin Auren bayan sungama gaggaisawa da mutane,suka dumguma zuwa gidansu zahirah domin daukansu zuwa wajen Lonching din,koda suka zo,tuni amarya ta cakare cikin wani dakakken Codde less,Light brown Colour,ammata dinki ciki da alaku,riga da zani,sai head dintama milk colur haka pos din dake hannunta,da mayafinta takalmin kafanta ma milk colour ne,halfcover ne mai wasu Stones ta sama,su little Ummi kuwa wata gown aka samata fara Kal da ita mai wani baza daga kasa,angyaramata gashinta an rabashu gida biyu,ansa wasu band masu kyau an daure,kafarta itama sanye da wani bakin takalmi itama din cover ne wanda ya hadu har yagaji da haduwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button