UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Moodu kuwa shima an shiryasa cikin shigan wani riga da wando yan kanti black and white,wandon baki rigar fara,ansaka Tambarin ARMY da babban baki ajiki,yaci ko zanzaro abunshi,shima kan nan ya sha gyara,kafarsa shima sanye da takalmi sawu ciki bakake na fatar damusa,hannunsa harda wani bakin Royal Din agogo mai tsada da yarari,kai Abun fa sai wanda ya gani,in kaga little da moodu saboda sha”awa sai kaji kamar ka sacesu balle zahirah wacce Teema makeup tazo ta fitomata da aininhin Sirrin kyanta sai wanda ya ganta,duk da basuyi anko ba,Asma”u tayi shigar less ne itama Ammh nata riga da Sikat ne dinki halfjamfa ce ta dauketa matuka Sikat din pencil ne yakamata sosai ya fitomata da Suranta da Allah ya badata,Less din nata milk colour ne,shima yana da wasu Stone ajiki suna kyalli suna daukan ido gwanin ban sha”awa,head din kanta brow colour ne,haka Takalmin kafarta itama Halfcover ne,mai kyau dashi tare da pos din dake hannunta harda ita akama kwalliya abunka ga farar mace sai ta haska cikin kayan da kwalliyan gabadaya,su Alee ma sun sha gayunsu cikin Riga da wando abun sai wanda yagani,Su Ashe kuwa anci doguwar riga cikin wani boyel less,an saka gwaggwaro an bazo gashi ta baya,tace bamai barinta abaya dole ta hallarcin wannan wajen,hakama mahgana da Sauran yan”uwa da abokan arzuka suma sun chakare sunce baza”a barsu abaya ba Suma..
Suna isowa suka shiga har cikin gida Suna fadin afito musu da amarya Su wuce da ita,ga ango chan na jiranta amota,Dr.Abduljabar kenan da Shureim suke ke wannan mganar,kin ko basu amarya Ashe kuwa tayi tace sai Sun gama diban mutane kana,dolensu suka fara daukan mutane suna kaisu kayatattacen Hall din daza”ayi Lonching din wanda kenan cikin GRA din,Su Asma”u ne karshen Tafiya ita da zahirah domin ko su Little Ummi da moodu Ashe tatafi dasu,Lokacin da aka sanya Zahirah cikin motan dayake ciki sai da yakusa zaucewa da ganin kyan da zahirah tayi,Shima din yana sanye da Shadda Milk colour aikin jikinta kuma brown colour ne,sai hular kansa ma haka,hatta Rufaffan Takalmin kafanshi ma hakane,sai agogon hannunsa ma na wani fatane Shima brown colour ne,Kallonta kawai yakeyi,itakuma tana mai Fari da ido,hanunta ya riko yana matswa lokaci daya,yana kurama Kunshinta ido yadda ya tsaru kuma ya dace da hannun nata,dayake Shureim da Dr.Abduljabar na gaban motan baya da halin mgana,Asma”u kuwa motar Mooh ta shiga don yana ganinta yajata yace tazo ta shiga motanshi Tunda Tasu zahirah tacika ba waje,to ya zataki balaraba daga sama,ai sai tatafi tana yanga ta fad motar yaja suka bi bayan Su mu”azzam.
Koda sukaje wajen sun iske su Little bakin hall din don dama dasu zasu shiga,mu”azzam na fitowa ya damke hannun zahirah su moodu kuwa suka ruga wajen iyayansu Zahirah ta rikema little hannu ayayinda Mu”azzam ya rikema moodu ammh dayan hannun nasu suna damke juna su Asma”u da mooh suka biyo baya kana,Su Shureim da Dr Abduljabar suka takamusu baya har zuwa cikin hall
Suna Shiga wajen yadau sowa da ihu da tafi lokaci daya wata waka tana tashi ahankali na U ARE MY LIFE..”Sukuma suna taku cikin isa da Shauki hannunsu rike da juna,gefe daya kuma,suna damke da yan”diyansu duk wanda yagansu indan akace ya”yansu ne, sai sunyi mamaki matuka,Abun ya burge kowa fa,sun isa wajen dazasu zauna suka zauna suka sanya ya”yan nasu atsakiya kowanne ya rike hannu daya cikin burgewa,nan da nan waje yadau Sowa,kafin mc ya fito yafara gabatar da Abunda ya tara mutane,nan da nan aka zagaye kowani tebur da abinci bayan anci ansha aka sanya kida mata Suka shiga fili Sunata rawa cikin harda Ashe da mahgana,Su Shureim da Dr Abduljabar suma sun shiga fili sun chase sosai mu”azzam dai ko da akace su taso ki yaki,yakuma hana zahirah tasowa Asma”u ne tazo ta dauki su little ta shiga fili tadan taka rawa mooh ya fito yana mata barin yan dubu na liki,su Shureim namai tsiya suna bazasu basu ba,Saboda shi balarabe ne,dariya kawai yake musu baya mgana saboda murna,sai wajen la”asar aka tashi bayan anyi hotuna da Sauransu,kafin kowa ya watse amaida amarya akafara Shirin Tafiya Abuja da ita don mu”azzam yace yau zasu wuce babu tsayawa,suna dawowa aka shiryamata kayanta da nata dana yaran sai akwatunanta aka fita dasu aka sanya amota,Wanka aka sakata ta sakeyi ta sanya wata atamfa da Farin hijabi kafin akaita wajen bahna dinta,albarka kadai yaketa sakamata domin yace in da zata ba bakonta bane kuma ita ba yarinya bace yanzu ta san Abunda ya kamaceta,Hardashi mu”azzam ya aika yazo ya hadasu yayi musu nasiha,daganan gidan Famfari suka nufa da ita wajen baffa da Yakura suma sukayi musu nasiha tareda fatan alheri,Wannan karon tafiyan babu yakura saboda ba mai kula da da Shettima shiyasa ta zauna Ashe ce da mahgana da wacce Ashe ke bima wa,Wacce suke cema yafindo,Sai mami mahaifiyar Asma”u,Wacce dama da direbanta Tazo shi ya dauketa,Shureim Shiya dauki amarya da yan”uwanta ayayinda Dr.Abduljabar ya dauki Mooh da Asma”u da mu”azzam wadanda Su little ke hannunsa,sun makalemai Ushe,kuma motar daya tuko ta dauko kayan abinci ne na gara,da kayan toye toye na al”ada,shikuma direban Shureim kayan sawan zahirah ya dauko da akwatunanta da kayan bukatuwanta danata dana yara,Sai mami ita kadai ita da direbanta karfe 5:30pm na yammah Suka bar garin suka dau hanyar maiduguri zuwa Abuja..
Basu isa Abuja ba,sai after 9 na dare kana motocin suka shiga maitama,abakin get din suka tsaya suka fara malamala hon da gudu sani mai gadi yazo ya budemusu motocin suka fara Sulalawa zuwa cikin gidan,Ummi da hajiya da mom sune ke falon sanda motocin suka shigo gidan,Lubna da zulaika ko ciki,suna hira.
Dama Tun tasowarsu Mu”azzam yakira Ummi ya fadamata gasu bisa,hanya shiyasa duk wani abu daza”ayi na tararsu an kammallahshi kama daga kan girke girke zuwa kan kayan lashe baki,suna jin Diran mota suka mike,Ummi dake sanye da wani Ubansu less,Doguwar riga less din daga kallon Farko zaka gane bakaramin dukiya aka mikaba kafin a daukosa ba,Kunnanta da hannuwanta Zinarene, ke kyal kyali yana haskawa,da hanzari suka fice Ummi ce kan gaba,ita ta bude motar da zahirah take ta fito da ita babu kunya Ummi ta rike hanci ta rangada kuda akunnan zahirah aifa sai waje yadau sowa,mahgana da Ashe ma suka soma guda,harda juyawa da rawa,Mu”azzam dayaji Ummi na guda sai dayayi mamaki,dama haka Ummi take,ita ta riko zahirah da kanta harzuwa cikin gida,itakuma hajiya da mom suma ma sauran jama”a sannu da zuwa,haka aka sassauke kaya su karime na jida suna kaiwa cikin gida,gabadaya suka dumguma zuwa falon hardasu mu”azzam din,Wanda yayansa ke makale dashi sunki yarda da kowa sai shi,jin guda daga falo shi ya fito da zulaika da lubna daga saman Ummi itama Lubnan tayi shigarta ta alfarma cikin Shaddart Navy blue,riga da zani tayi kyau sosai abunka da farar mace,da hanzari suka sauko suma masu sannu da zuwa,ita ta kariso ga Ummi tana riko zahirah tana fadin”oyoyo Antyna barka da zuwa…”Zahirah bata amsa ba domin tana cikin mayafi ne,daganan dakinta nada wanda ta barshi aka nufa da ita da kafar dama Ummi ta umarce zahirah ta shiga saiga Ummi har kan makeken gadon zahirah tayima mata masauki tana sakin guda da kanta,su ashe na tayata,lubna ce ta zauna agefenta tana rike da hannuwanta nan da nan Ummi ta fice tabada umarnin kawo kololin abinci kafin kice kwabo ancika gabansu da Nau”ikan Abunci kala kala da drinks suma su mu”azzam an kai musu shashensu Abun sai wanda yagani,Lubna bata nuna kishi ba ko kadan ita ta samo pilet ta zuboma Zahirah sinasir da miyar alayyahu,tazo har kan gado tayaye mayafin nata ta mikamata abincin,zahirah batayi musu ba,ta karba da mirmishi tana fadin”Ta gode..”