ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Amiru ya lumshe ido, ya ce,
“Uncle Junaid, bani da bakin da zan gode maka……. bani da abin da zan biyaka wannan alfarmar da ka yi min…..” Uncle ya yi murmushi ya katseshi yace,
“Kana dashi Amiru!.
Mairo ta sha bani labarin soyayyar da kanwarka Amina take yi mata, wannan wadda suka zo mai kama da kai. Ta shaida min cewa maigidanta ya rasu. Ka bani Amina in aura Amiru, don wanzar da dauwamammen zumunci a tsakanin mu”.
Cikin al’ajabi Amiru ya ce,
“Amina is special a gare ni ko a cikin kannena goma sha biyu, lallai Amina is among the luckiest….
Na taba gayawa Habibu zan roke ka ka bar mini Mairo, ni kuma in baka kannena hudu ba lefe ba sadaki. Na fada ne kawai a fatar baki, ashe Mala’iku sun amsa. Uncle Allah ya kara GIRMA!”.

Suka hade hannunsu suka cure kamar ba za su saki ba cike da wata shahararriyar kauna daga Allah, Baffa ya ja su doguwar addu’a suka shafa. Baffa ya ce, su barshi da Mairo, su ci gaba da shirye-shiryen su, yana so zai yi mata ba-zata ne. Suka yi murmushi. ***

Kwana ta yi tana gwada lambar Uncle Junaid ba ta samu ba. Ta shiga damuwa sosai. Tsoron ta kada Allah yasa fushi ya yi saboda ganinta da ya yi tare da tsohon mijinta.
Abu kamar wasa Uncle har kwana uku babu wayarshi babu kafarsa cikin gidanta, don haka ta yi tattaki har office amma ba ta same shi ba. Shima Amiru ko sallama bai zo ya yi mata ba, ya kwashe ‘ya’yansa ya tafi Abuja dasu ba ta kara jin duriyarsu ba.
Da albishir mai dadi ya tari Alh. Abdurrahaman da Hajiya Aisha, ya kuma gaya musu bukatar V.C na auren Amina. Daddy da Hajiya suka yi ta hamdala tare da kara yawaita sadaka. Ko da Amir ya tuntubi Amina ya yi mamakin amincewar ta nan take. Bai san ita tunda ta dora ido a kan Junaidun ba ta kara gane kanta ba.

Ya yiwa gidan Habibu tsinke a daren bakinshi ya kasa rufo, zumudin ya gaza boyuwa. Habibu ya dafa kafadarshi ya ce
“Angon Harrit ya aka yi?”
Ya harare shi ya ture hannunsa daga kafadunshi, ya ce,
“Kai komi mai muhimmanci sai kasa iskanci da shakiyanci a cikinsa, to bani goro in baka albishir”. Ya ce,

“To bari ina zuwa”.

Ya fito jim kadan bayan shigarsa da kwalin ‘Aspen’ da ‘Lighter’, ya zari daya ya kunna ya manna mishi a baki. Da sauri ya ture ya bige hannunsa, tabar ta fadi, ya bi ya take da takalminsa, cikin takaici ya ce,
“Wai don Allah Yaya Habibu, yaushe za ka girma ne?”
Ya yi dariya ya ce,
“Sai ranar da son Mairo ya daina kai ka hanyar lahira, ya daina kwantar da kai a asibiti, wato ranar da ka zama namijin duniya”.
Dina ta yi dariya ta ce,
“Rabu da shi Amiru, muna nan muna jiran nashi turn din, idan ya gano wata ‘yar kwailar. Irin su Habib ba ciwo suke a kan soyayya ba, rijiya suke fadawa dungurungum su kashe kansu in sun rasa samun wadda suke so….”.
Ya ce,
“Amma kin yanke ni ke da sirikinki bashi kuka ci, akwai ranar da zaku biya shi”. Amiru ya ce,
“Na ma fasa baka albishir din, tunda da Taba za ka hadani, ka jawo min fushin Mairo, ban ji ba ban gani ba……”.
Ya kamo hannunshi ya fizge, yana dariya ya ce, “Haba dear…. tuni na ji albishir din, ai Baffa ya gaya min komi yanzun nan, kun yiwa V.C Junaidu fin karfi kun toshe masa baki da Amina”. Ya yi dariya ya ce,
“V.C mutum ne mai saukin kai, yadda na zaceshi ba haka yake ba, ya ji tausayinmu ya tallafi rayuwarmu shima Allah ya tallafesa. Bani da abin da zan biya shi wannan sadaukarwa da ya yi min koda na bashi my favourite sister. Wanda na san zai karba ne ba don so ba, sai don kulluwar zumunci a tsakaninmu”.


Tana shirin fita office wayar Baffa ta shigo, da hanzari ta amsa cike da girmamawa. Bayan sun gaisa ya ce,
“Kina gida ne yanzu?” Ta ce,
“A’a, ina shirin fita ne zan ba da lacca 8-10”. Ya ce, “To in kin fito ki zo ina son ganin ki”. Ta ce, “Babu damuwa Baffa sai na iso”. Suka aje wayar a lokaci daya.

Karfe goma na safe ta fito daga ‘twin-theater’ cikin rakiyar zugar dalibanta, wadanda suka riko mata jakar hannunta da takardunta har zuwa inda ta adana Terrain din ta, ta karbi kayan hannunsu suka yi sallama suka koma, ita kuma ta zaburo mota sai Yakasai gidan Alh. Abbas.
Bayan sun gaisa da Habiba da Hajara da su Rahama, ta samu Baffa a falonsa, ya nuna mata waje ta zauna, ta zamo daga kujera ta dira gwiwoyinta a kasa ta gaida shi. Ya amsa yana duban ta sosai, ganin yadda ta ramar da kanta cikin ‘yan kwanaki kalilan saboda damuwa. Bai nuna mata komi game da zuwan Junaid da Amir ba, tambaya ta farko da ya watso mata ita ce.

“Mairo maza biyu za ki aura ne???”

Ta cira kai da sauri ta dubi Baffanta, ya girgiza kai ya ce, “Yo maza biyu mana?
Kin amshi maganar Junaidu, an gama komi sai shafa fatiha kadai ya rage, sai kuma ki turo min Alh. Abdurrahaman da kansa ya zo bikon ki? Sannan shima Amiru ya zo, dukkanninsu da rokon a maida aure.
To dukkansu akwai mutunci da ganin girman juna tsakanina dasu. Don haka bana bayan kowa, zabi yana gare ki, kamar yadda shari’a ta baki dama. Ina so ki gaya min wanda kika fitar ni kuma ranar da na sanya ba zan daga ba zan daura aure”.
Kanta a sunkuye ba ta yi magana ba, har sai da Baffa ya gama yana sauraron ta. Ganin ta ki yin magana ya ce,
“Kefa nake saurare Mairo”.
Daga can kasan makoshinta ta ce,
“Baffa ni bani da zabi a cikinsu, kamar yadda ka ce sharia ta bani damar in zaba, ni kuma na baka wannan damar, ka daura da duk wanda ka ga ya dace. Duka ina son su ina kaunar su, don haka ba zan iya zaben daya a cikin su ba”.
Baffa ya girgiza kai yana murmushi. Autar Inna Hure, bai san sanda zata daina yarinta ba!.

Ya ce,
“To shi kenan, tunda haka kika ce, na kuma gode da wannan GIRMA da kika bani, ya nuna min cewa kin amince ba zan yi miki zaben tumun dare ba.
Da fatan duk wanda na zaba miki a cikinsu za ki yi min biyayya shima ki yi masa, ba tare da an tsaya yin wasu tone-tone da kwakulo laifin da ya riga ya shige ba, za ki zauna lafiya dashi har karshen rayuwarmu”.
Kanta a kasa ta ce,
“Na yi wannan alkawarin Baffa”. Ya ce, “To tashi ki koma kan aikin ki, Allah ya yi miki albarka”.
Cikin zuciyarta ta ce, “Amin”. Ta taso ta fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Daga Amiru har Junaid ba ta kara jin duriyar kowa ba. Ta bi shawarar Nabilah, da ta ce dukkansu kar ta neme su ta rabu dasu.
Sai ana i gobe daurin auren da ba ta san da wa Baffa zai daura ba a cikinsu. Text din Uncle Junaid ya shigo cikin wayarta da misalin karfe uku na sulusin dare. Ta zaro wayar daga karkashin filonta, hannunta na rawa ta duba, ga abin da ke rubuce.

SAKON UNCLE JUNAID GA MAIRO!

“Marriage is much more important than mere relationship. It’s the root of all family tree. Any mistake in sowing the seed will be disastrous…. a mature seed has better chances for germinating than an immature one…. A garden close to one’s home has to be watered and tendered than that which is very far away……………….
-Mai son ki.

(wato aure yafi muhimmanci fiye da dangantaka kawai. Domin shine jijiyar bishiyar iyali gaba daya, don haka hadari ne babba asamu kuskure wajen dasa wannan bishiya…. kosashshen iri zai fi saurin yado fiye da talalabuwa…. lambun da yake kusa da gidan ka zaka fi bashi ruwa da kulawa, fiye da wanda yake nesa………….).

Ta karanta ya fi cikin carbi, kafin ta fahimci me sakon Uncle yake nufi. Yanzu ne ta fahimci ashe duk sakonnin nan da ake turo mata tana Michigan da ‘logo’ na hular ilmi, ashe Uncle Junaidu ne. Ta kifa kai cikin filon ta, tana kuka mara sauti. Kukan tausayin Uncle Junaidu! A lokacinda ta fahimci Uncle Junaid ya sadaukar da soyayyarshi ga aurenta da ‘ya’yanta….. Ta yadda har ya kira alakarsu da ‘mere relationship’. Ita ma ta yarda ta amince AMIRU SHI NE ZABIN ALLAH, ba zabin zuciyarta ba……!!!
[8/20/2019, 06:30] Meema: Daga kowanne bangare ba su samu matsala ba, sun samu kwarin gwiwa daga Baffa, Yaya Habibu da Alh. Abdurrahman Gaya. Wadanda burinsu kenan. Hatta Hanan wadda ke da ‘ya’ya biyu a lokacin da mijinta Ramadan ta samu halartar walimar maida auren Dr. Mairo da Amirunta, Amina da Uncle Junaidu, wadda aka gabatar a ranar asabar, juma’a, ashirin ga watan maris, daruruwan jama’a suka shaida daurin auren Mairo da Amiru a karo na biyu, a kofar gidan Alh. Abbas mai goro.
Wannan aure ya ga kusoshin ilmi, daga Kano da wajenta, da daukacin jami’o’in Najeriya. Furofesoshi, kwamishinoni da daktocin ilmi, abin ba a cewa komi.
Daga Mairo har Ameeru babu mai ra’ayin bidi’o’i, dokance suke da a sake mallaka musu juna. Tsohuwar soyayya ce ke aiki tare da taimakon sabuwar soyayya. Ta dankawa Alh. Abdurrahman da Hajiya Aisha jikokinsu kamar yadda suka nemi alfarmarta, sai fatan Allah Ya ba ta wasu masu albarka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button