ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara.
“Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?”
Cikin kuka ta ce
“Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba”.
Ya ce “To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?”

Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya kuta ya ce
“Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki?
Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi, sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya ba garin ba.
To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike so.
Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA… akan yi UWAR DAKI…? To ba da abokina ba!
Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi.
Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa. Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu ke babu tukin mota. To kin ji”.

Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din suit’ dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba.

Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina.
“Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?”
Dina ta yi shiru, ya ce “Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta magana ni kadai?”
Ta ce “To me ya faru?”
“Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a’ah?
Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?”
Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce
“Am… Eh, ai sako zata kai wa Amirun”.
A fusace ya ce
“Sakon me?”
Ta ce “Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu”.
Ya yi dogon tsaki, ji kake ‘tsiiittt!’ Ya maida kallonshi ga Mairo
“Ba ni wayarki”.
Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin.

Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri.
Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce “Kin same shi?”
Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo.
Dina ta sa yatsunta tana share mata, “Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah. Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba”.

Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta.


A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk ‘yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani. Maryam Muhammad Bedi, ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin ko da dar a zuciyarta ba.
Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud’s stages of psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga phallic-stage… Anal stage… da ‘yan uwansu.
Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!! Habibu da ke cikin ‘yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka.
Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace… Malam Muhammad Bedi, zai dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al’umma.

Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan ajinsu don yayi supervising hakan.
Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo.
“Mairo ‘yan makaranta……Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu”.
Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce.
“Zo zauna, mota zan sake miki”.

Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa “Gaya min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai.

Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al’amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi sati daya, me kike so in kawo miki?
Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da sauransu. Ke kuma fa?”
Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, “Ladidi nake son gani”.
Ya ce
“Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta”.
Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta.
Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman sociology. Habibu na addu’ar Allah Ya sa ba sociology’n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba. Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button