ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikin Daddy a masifar sanyaye, da mamakin wai itama Hanan an saketa. To shi yana ina aka yi duk wannan kazamin aiki? Lallai Hajiya ta bashi mamaki. Ya kuma soma zargin koma menene itace ummul-haba’isi, haka kawai za’a kashe masa Da a banza.

Habibu bai bar jinyar Amiru ba, duk da tabbacinsa na sakin Mairo da yayi. Duk da zafin hakan dake ranshi. Duk wai wata kusan tafi wata kusan. A wurinshi ba Mairo ce ta hada shi da Amiru ba balle ta zamo silar rabuwarsu. Allah ne ya hada su, ya sanya kaunar juna da soyayya a tsakaninsu, ba kuma zasu rabu a dalilin ta ba. Ko ba komai Amiru ya wanke mishi zuciya da baiyi mummunan saki ba wanda Allah baya so. Yayi kokari ya karanta hargitsatstsen rubutun ya ga saki daya ne. Kullum kafin ya fita ofis zai zo, haka in ya tashi yana nan tare dashi har goman dare.
Amiru yana shaida kowa, amma baya magana. Sai bin kowa da ido. A ganin shi rayuwar bata cancanci a cigaba da itaba, ba tare da abinda zuciya da gangar jiki ke so ba. In za’a bashi zabi gara mutuwa da rayuwa babu Mairo.
Kasancewar Daddy da Habibu na kula da shan magungunan sa akan lokaci, ya sanya kullum sauki na kara samuwa.
Daddy ya shigo falon da ‘ya’yan sa, Hajiya da Hanan ke zaune, kowanne kai a kasa. Jiki yayi la’asar babu laka. Ita kanta Hanan ta tsorata da ganin yadda Amiru ya koma cikin dan lokaci kalilan. Sau daya ta shiga part dinshi, tausayi bai barta ta kara komawa ba. Ko babu soyayya Amiru dan uwanta ne wanda take ji har cikin kashi da bTa kuma alkawartawa ranta fadiwa Daddy gaskiyar duk abinda ya tambayeta ba tareda shayin Hajiya ba, don Yaya Amiru ya samu lafiya, ya samu abinda yake so, ita tayi hakuri, ta auri Ramadan wanda ke son ta kamar ya kashe kan shi.
Amina kadai ake jira a falon wadda bata karaso daga Switzerland ba har yanzu. Don haka ganin ana batawa ‘majority’ lokaci, akan mutum daya, Daddy ya yanke hukuncin ayi taron bada ita ba.
Ya bude taron da cewa kowa yayiwa Annabi salati goma. Ya ja doguwar addu’a suka shafa. Yasa gilashi ya soma duban ‘ya’yanshi mata su goma sha daya da fuska mara walwala. Ya maida dubanshi ga Hajiya A’isha yace
“Hajiya, keda Hanan kune a gidannan sanda abin ya faru, don haka ku zan fara tambaya. Yaya aka yi Amir ya saki matansa biyu duk a lokacin daya?”
Hajiya tayi shiru, ta soma share ido da gefen mayafinta, abinda ya riga ya zame mata jiki tun ranar da aka dawo da Amiru wai yana fama da ciwon zuciyar data yi tsammanin yayi hannun riga da shi. Tararradinta shine idan ta rasa Amiru ina zata tsoma ranta? Mutumin da ke yi mata biyayyar da duk cikin ‘ya’yan ta babu mai yi mata kwatankwacinta?
Mutumin da ya sadaukar da farin-cikinshi akanta. Bama wannan ba, ina zata kai hakkin Mairon da bata ci mata ba, bata sha mata ba, biyayya take yi mata tamkar tayi mata sujjada, kawai don Allah As-samadu bai bata haihuwar da bata isa ta baiwa kanta ba? Ta tabbatar ba komai ya kai ta yin umarnin data yi ba, bacin ran sakin da yayiwa Hanan ne. Wadda ita bata damu ba, kamar dama jira take, yana sakinta ta hada ya-nata-ya-nata tayi tafiyar ta, babu ko cikakkiyar sallama. Sai yau ta ganta cikin taron da bata zata ba.
Amma ko waya Hanan bata kara yi mata ba. Gatanan da ranta da lafiyar ta ba abinda ya dameta. Sai nata dan data jefa cikin halin ha’u’la’i. zaiyi-ba zaiyi- ba Allah masani.
Ta dubi Nina, kamar ta tsinka mata mari, domin dai ita ta kaita ga abinda bata taba tsammanin yi a rayuwarta ba. Wato bin malaman tsafi Yarbawan Lagos, haka-kawai zasu fidda ita a imanin ta. Kukanta ya tsananta ta kasa baiwa Daddy amsa.
Don haka ya juya akalar tambayarsa ga Hanan. Ta sunkuyar da kai ta soma fada masa duk abinda ya faru, tun ranar da Hajiya ta aika ta zo, abubuwanda ta rinka bata wai tayiwa Amiru amfani dasu, har zuwa ranar daya saketa, da tirkeshi data yi ya saki Mairo. Daddy ya jinjina kai cikin al’ajabi da mamaki, yaushe Hajiya ta koma haka?
Ya ce da Hanan ya gama da ita, kuma ya gode. Kuma menene ra’ayinta kan zama da Amiru? Tana so idan Allah Ya bashi lafiya zata dawo dakinta ne ko a’ah?
Ta sunkuyar da kai tace “ka fahimce ni Daddy. Ba wai bana son Yaya Amiru ba, amma shi wallahi-wallahi baya so na. Matarshi kadai yake so Daddy. Kuyi kokari ku dawo mishi da abarshi cikin gaggawa in har kuna son lafiyar shi fakat. Nikam har ga Allah na hakura, zan auri mai so na. Daman kuma babu iddarshi a kaina”.

Daddy ya sake jinjina kalamanta, yayi mata godiya ya sallameta ta fita ta koma wurin Amiru. Inda aka baro su shida Habibu. Daddy ya dubi Hajiya cikin wani irin fushi da ‘anger’ da bata taba gani daga gareshi ba. Fuskar shi tayi jawur abinki da bafulatani, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun canza launi daga farare sol zuwa jajaye. Jikinshi na tsuma, tsigar jikinshi na tashi yace
“A’isha! Hanan gaskiya ta fadi ko karya ne?”
Ta juya kai cikin tsoro da tashin hankali, nadama da yin kaico da kai, don bata taba ganin shi cikin wannan halin ba. Tace
“batayi karya ba anyi haka. Sai dai kuskure ne da ajizanci irin na kowanne dan adam. Na tuba Alhaji na bi Allah na bika. Sai dai komai ya faru ne da zuga da taimakon wadannan……….” Tana nuna Nina, Ni’ima da Khalisa.
“Su suke karbo komi a Lagos wallahi ban taba zuwa ba. Don nasan zuwa wajen irin wadannan mutanen haramun ne. Na roke ka, kada ka bari Habibu yaji wannan magana don GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN SA don ba iyakarta kenan ba…….”
Cikin nishi Alh. Abdurrahman yace “sai kuma me?”
Ta yarfe hawaye da majina tace
“Na sanya shi ya janye hannun jarinsa daga bankinsu shida Habibu……duk takardun dukiyar shi suna hannu na yanzu, bari inje in dauko…”.
Tana shirin mikewa ya daga mata hannu “bayan Nina, Ni’ima da Khalisa sai kuma wa?” tace “sai mutanen Gaya. Su suke cewa “juya” ce. Don haka ne na kulla auren shi da Hanan don ya samu ‘ya’ya kawai wallahi, amma ba don in raba shi da matarsa ba….. kai shaida ne akan cewa tsakani da Allah ina son Mairo”.
Ya kalli Nina da Khalisa da suka yi tsuru-tsuru, jikinsu sai kyarma yake. Don sun gigice da ganin ‘tension’ din mahaifinsu mai son su da gudun bacin ransu, tareda kyautatawa rayuwarsu tun daga yarinta har girma. Rayyah tace “wallahi babu ruwana……” Sabah tace “wallahi babu hannu na…..” Mami tace.
“ni Daddy da ba a kasar nake ba, wallahi bani da masaniyar komai…….”.
Juyawa yayi gefensa ya fizgo wayar talbijin. Ya soma binsu yana tsula musu. Duka na tashin hankali. Da masu ruwan, da wadanda suka ce babu ruwan su. Yana hawaye yana tafkarsu, yace
“Kun yi asara! Kun kashe auren mutumci da amana da soyayya ta gaskiya!!
Bazan yi muku baki ba. Amma kuji tsoron hakki. Kuje duniya kadai ta isheku, tunda kuma mata ne kuma aure kuke kamar yadda Mairo ke zaman aure.
Sannan abinda kuka yiwa Mairo, kuka sa aka yi mata, zai iya faruwa da kowaccenku. Dan uwanku kuma idan yana da hakkinku Allah zai fitar masa, muddin ya mutu bai yafe muku ba.

Kuma sai kun maimaita wannan magana agaban Habibu, sai Habibu yaji wannan maganar.
Ke kuma Hajiya ki tattara ya-naki-ya-naki ki tafi Gaya, sai na nemeki…….bana bukatar ganin ki a cikin gidana yanzu……”. Kowa a falon kuka yake, yana rokon gafara. Basu kara tsananta kukansu ba, saida suka ji wannan danyen hukuncin da Daddy ya zartas akan Hajiya. Suka rirrike kafafun shi suna bashi hakuri yace
“ni baku yi min komai ba. Wadanda kuka yiwa su zaku nema gafara amma ba ni ba. Sannan bazan taba sanya baki Mairo ta dawo gidan dan uwanku ba. Tunda bakwa son ta.
Ku aura mishi duk wadda kuke so tazo ta cika muku gida da ‘ya’ya. Ko ya mutu, ko yayi rai, na barwa ALLAH! Ku bace min da gani dabbobin banza. Hajiya ina kara gaya miki, kada in dawo in ganki cikin gida na….”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button