ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Malam Bedi da alama zancen Habibu na shigarsa. Ya ce “Yanzu ni me zan iya akai Habibu? Ba karamin abu ba ne Hure ta amince akai Mairo makarantar book ba. Ni kuma bana son tashin hankali balle abin da zaya bata mini rai, ina zamana lafiya”.
Habibu ya dubi mahaifinsa cikin ido, ya ce “Shin Baba kai ko Inna wa ke auren wani?”
Malam Bedi ya ce
“Ni ne”.
Ya ce “To matukar kai ke da iko da ita dole ka ba ta umarni. Kuma dole ta bi idan dai ita matar kwarai ce. Ka daina tsoron sababinta, kai ma ka bude mata murya. Ita ma ta iya ta bude maka makogwaro balle kai?”
Ya yi murmushi ya ce “To yanzu me za a yi?”
Ya ce, “Ni zan je na samu hukumar makarantar in musu bayani har halayenta duka zan fada musu, don su yi hakuri da ita, su kuma san matakin da za su dauka a kanta idan ta gudo ba tare da sun yi la’akari da fadan Inna ba. Ga kuma makarantar islamiyya da na ga yara suna zuwa da hijabinsu da uniform, nan ma zan je in ba da sunanta su sanyata ajin da ya dace da ita.
Kai kuma aikinka shi ne ka tabbatar tana zuwa akan lokacin, da son ranta da na Innar ko babu?”
“Malam Bedi ya ce “Sha Allahu za a yi kokari. Allah dai Ya yi maka albarka Habibu, idan ban da kai dan uwanta wa ya damu da ita balle har ya ce a sanyata makarantar?”
Habibu ya ce “Sai abin da ya kawo ni, amma ina ganin mu samu gindin bishiyar can mu zauna, maganar ta zaune ce”.
Malam Bedi ya ce “Inji dai ALHERI ne?”
Ya ce “Alheri ne, idan Allah Ya so Ya yarda, kai ma ka yarda”.

Suka samu kututturen bishiyar wata goriba mai duhu da inuwa mai sanyi suka zauna. Malam Bedi ya tattara dukkan hankalinsa akan Habibu, yana zake da son jin mai zai fito daga bakinsa. Shi kuwa Habibun in banda addu’ar neman rinjaye babu abin da yake dannawa Malam din daga zuciyarsa.
Malam Bedi ya ce
“Kai na ke saurare, kuma ka yi shiru”.
Habibu ya ce “Eh to, dama Alhaji ne ya ce in zo in shawarce ka, ko kuwa in nemi izninka, idan ka yarda shi ke nan. Idan ma ba ka yarda ba babu damuwa sai na hakura”.
Ya ce (a dan kufule) “Wai mene ne ka ke ta kwana-kwana? Daga ji ba abin arziki ba ne, don abu idan na arziki ne ba a kumbiya-kumbiyar fadarsa”.
Ya yi murmushi ya ce “Yi hakuri Baba. Wani abu ne na zamani ya shigo mana cikin na’ura mai kwakwalwa wai shi yanar-gizo (internet). Ta cikinshi babu inda ba zaka sadu da shi ba a duniya. To rannan ina lalube na, sai na ci karo da tallan wata makaranta a Malaysia suna neman dalibai. Kamar da wasa na cike form dinsu na tura musu.
To kwatsam har na manta, shekaran jiya sai ga sako sun turo cewar sun dauke ni, na zo na biya kudin makaranta na fara karatu. Na samu Alhaji na fada masa, ya tayani murna kwarai, to amma shi kansa ba ya da kudin da zai iya daukar nauyin karatun, amma yace zai yi min hanyar da zan mika neman taimako daga gwamnati ta hanyar wani abokinshi mai baiwa gwamna shawara akan harkokin matasa wai shi ALHAJI GAMBO ADO, kuma ya tabbatar min za a samu insha Allahu, ragowar shi Alhajin ya yi alkawarin cikasawa daga aljihunshi.
Shi ne ya ce na zo na fada maka tun kamin komi ya yi nisa, kada sai an gama wahala ka zo ka ce ba ka yarda ba. Yanzu kuwa ba abin da aka yi, sai da amincewarka”.

Shiru Malam Bedi ya yi kamar ruwa ya cinye shi, yayinda Habibu ya ci gaba da jifansa da, “Innahu ala raja’ihi la-kadir”. Bai gushe ba yana maimaita addu’arsa sai jin muryar malam Bedi ya yi tana tambayarsa har tsayin shekaru ko watanni nawa za a yi ana karatun?
Ya yi godiya ga Allah a zuciyarsa, domin da alama akwai nasara, ya ce “Abin ya fi karfin watanni. Shekaru shidda ne zan yi ina karatu akan na’ura mai kwakwalwa”.
Malam bedi ya ce “To daga nan kuma fa?”
Habibu ya murmusa ya ce “Sai na dawo gida na nemi aiki”.
Malam Bedi ya ce “A’ah, ba haka nake son ji ba, sai ka dawo ka yi aure ka tara min ‘ya’yan da ni Allah bai bani da yawa ba”.
Habibu ya sunkuyar da kai yana murmushi, ya ce “Insha Allahu Baba”.
Malam Bedi ya ce “To ka je, Allah Ya tabbatar da ALHERI………..”

Dai-dai nan Habibu ya ji “tim!” A tsakiyar kansa an nannako masa katuwar goriba a tsakar ka. Kwakwalwarsa ta daure, kansa ya yi dumm!! Kamar an kwala masa dutse. Wata azaba ta ziyarce shi tun daga tsakiyar kansa har yatsar kafarsa. Kamin ya gama farfadowa daga takaitaccen suman da ya yi, sai jiyo zazzakar muryarta yayi kamar zata tsige masa dodon kunnuwa tana fadin “Yaya Habibu sanya min a aljihunka, nawa aljihun bujen ya cika……..”.
Suka daga kai su duka biyun suna kallonta, Mairo ce kwance abinta akan reshen bishiya, a kalla ta fi karfin awanni biyu akan bishiyar. Tunda liman ya tada kabbarar sallah ta yi raka’a daya ta dago, ta hango goshin kowa a kasa, babu mai kallonta, ta yayibo tabarmarta da zummar tahowa gida. Sai kuma ta hango nunannun goriba ai kuwa ta daka tsalle ta dare.
Duk abin da suke cewa akan kunnenta, sai dai ba wani fahimta ta ke yi ba sabida hankalinta ba ya jikinta. Ita dai tana tsinkar goribar ta gutsira ta ji idan da zaki ta sa a buje, idan ba zaki ta cillar. Sai da bujen ya cika ne ga shi kuma ba ta iya barin wannan zazzakar, ta cillowa Habibu ajiya.

Ya bude baki da kyar ya ce “To sauko mu tafi”.
Ta ce “Bari na tsinkowa Baba”.
Ya ce “A’ah, shi baya da karkon hakori”.
Ta kamo reshe bayan reshe tana bin jikin bishiyar cikin kwarewa har ta sauko suka taho gida.
A ranar da ciwon kai ya kwana, amma bai daina yi wa malam Bedi magiya da naci akan makarantar Mairo ba, ko baya nan. Malam din ya yi masa alkawarin kada ya damu, da yardar Allah kamin ya dawo Mairo ta kimtsu.
Washegari ya je ya ba da sunanta a makaranta aka sata aji uku. Ya yi musu bayaninta dalla-dalla wani malami da yake makocinsu ne ya ce ya san Mairo farin sani, ko shi yana takaicin rashin sa ta makaranta, to amma kowa ya san sababin Inna Hure, idan dai akan Mairo ne, shi yasa kowa ya sa mata ido. Amma insha Allah zai tsaya a kanta kamar yadda zai tsayawa ‘yar cikinsa.
Habibu ya yi godiya mai tarin yawa, ya nemi taimakonshi a kan ya taimaka ya bayar a dinka mata uniform, ya kirgo kudi ya ba shi har na littattafai da jakar makaranta. Sannan ya nufi islamiyyar yaran Gurin-Gawa, nan ma ya ba da sunanta. Sun tabbatar mishi ba komai ai irin su Mairon ake son a gyara.

Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga Mairo ranar litinin cikin kayan makaranta da jakarta a rataye ta tafi makaranta. Duk da Inna Hure na kumbure da shi, bai damu ba, tunda ya cika kudurin da ya dade yana damun zuciyarsa. Don haka koda ya je yi mata sallama zai komo Kano ta yi masa kunnen uwar shegu.
Hure ta ga tijarar Malam Bedi irin wadda ba ta taba gani ba, ba ta kuma taba tsammanin ya iya ba, domin cewa ya yi idan Mairo ba zata je makaranta safe da yamma ba, to dukkaninsu su zo su fice masa a gida, su tafi duk duniyar da za su.
Ba ta yi magana ba, amma a cikin ranta tasan wannan aikin Habibu ne, don yadda Malam din ke jin maganar Habibu ko ubansa sai haka. Abin da ta ce da shi kawai shi ne, “Saboda ka tabbata tsohon bakauye ka zauna dan ka ya fi karfin ka”.
Ya ce “Eh, koma mai zaki ce ki ce, amma Mairo da uwarta ba su zama min cikin gida muddin Mairo ba zata nemo ilimi ba. Me ye marabarta da dabba? Babu! Dabba ce aka sani da hawa bishiya da cin abincinta daga ‘ya’yan itace, amma ba dan mutum ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button