ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya yi gyaran murya, sannan ya yi murmushi, ya ce “Maryam”.
Ta dago a hankali ta dube shi cikin fararen idanunta ba tare da ta ce dashi komai ba.
Ya mike zuwa dan karamin firij da ke gefenshi ya fiddo gorar ruwan (Faro) ya bincire murfin ya sha, ya maida robar. Maimakon ya koma mazauninshi, sai ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna. Ya sake yin murmushi kafin ya sake kiran sunanta. Wannan karon kam ta amsa, ta ce
“Na’am”.

Ya ce “Sunana Dr. Fredrick, ni ne likitan da ke kula da lafiyar iyalin ABDURRAHMAN GAYA. Ina so ki ba mu hadin kai mu ceto rai, wanda ke cikin halin ha’u’la’i akan soyayyarki. Shin za mu samu wannan taimakon Mairo?”
Cikin murya mai sanyi ta ce
“Ni Doctor?”
Ya ce “Ke fa Maryam”.
“Ta ya ya zan taimaka?”
“Ta hanyar tayamu jinya, har sai ya samu lafiyarshi, domin a halin yanzu ba ya bukatar komai Maryam, sai soyayyarki, sannan ne mu ma za mu samu namu aikin ya yi kyau. Mai zai hana ki yarda ki auri mai sonki Maryam? Har ya ke neman rasa kyakkyawar rayuwarshi a dalilinki?”
Cike da matsanancin mamaki ta ce “wai wanene?”
Yayi murmushi ya ce
“Taso mu je”.

Dr. Fredrick ne a gaba, Mairo na biye da shi. Ya tura kofar dakin dazu ya shiga, ita ma ta sa kai. Dakin babu kowa, sai mara lafiyan, wanda ke barci sadidan. Sai dai fa da ganin irin barcin da yake yi kasan ba na Allah da Annabi ba ne, na karfin allurai ne.
Ba karamin bugawa zuciyarta ta yi ba (kamar wancan lokacin da ta fara ganinsa) a lokacin da ta sake yin arba, da dan Abdurrahman Gaya. Sai dai fa wannan Amirun ya sha ban-ban da wanda ta gani satittikan da suka gabata, ma’abocin kuzari da koshin lafiya, hadi da wasu nasibobi da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. Wannan Amirun ya rame fiye da tunaninta, sannan ga dukkan alamu ba karamin jin jiki yake yi ba.
Ta tsaya jikin gadon kawai ba ta ce komai ba, sai dai zaka iya karantar karyewar da zuciyarta ta yi, hadi da tausayi tsantsa, da shi ma ya bayyana bisa kyakkyawar fuskarta. Tambaya ta ke cikin ranta, ita kuwa wace ce da Amiru zai kwanta ciwo a dalilinta?

Kamar an ce da shi bude idonka, a hankali ya ke bude idonshi a kanta. To ita ma din kallonshi ta ke, sai ya dauka ko mafarki ne da gizon da ta ke mishi dare da rana, don haka ya dauke kanshi daga kanta, don bai gasgata idanunshi ba. Ya mayar da su kan Dr. Fredrick, wanda ke ta murmushi.
Shi kam al’ummar Hausa suna ba shi mamaki akan soyayya, shi wallahi har duniya ta nade, bai ga macen da zata kwantar da shi a gadon asibiti ba. Balle mutun irin Amiru, dan gata gaba da baya, wanda duk irin macen da yake so a duniya zai iya aura. Ganin abinnasu yake kamar irin a fina-finan India. Ya kama hannun Amirun yana murmushi, ya ce
“Kana da bakuwa fa? Wadda tayo tattaki tun daga U.S domin ta duba jikin ka!”

Bai juya ya kara kallon Mairon ba, wadda ganinta ya kara haifar mishi da faduwar gaba. Kirjinshi in banda bugawa ba abin da yakeyi. Zuwa yanzu ya yarda ita din ce, ba gizo idanun shi ke mishi ba. Likita ya kama hannun Mairo ya dora mishi kan kirjinshi, dai-dai santar zuciyarshi. Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa fat-fat-fat! Amma don karfin hali bai fasa magana ba cikin nishi.
“Ba wajena ta zo ba, ta biyo bayan Yayanta ne”.
Mace mai rauni da saurin karaya, sai ta soma kuka.
Tun fil’azal Mairo mace ce mai tausayi, abin kuka bai da wuya a gurinta, bare an ce a dalilinta ne Amir ya kamu da ciwon zuciya. Wato wannan ne dalilin Habibu na yanke mata karatunta, Allah sarki Yaya Habibu, a da har ta kullace shi tayi fushi dashi mai tsanani. Ban da abinsu ita wace ce? Da kasancewarta tare da shi zai sa ya samu sauki?
Likita ya daga mata gira, ya rausayar da kai, ta gane yana lallaminta ne ta rarrashi Amiru. Ta janye hannunta daga kirjinshi, cikin sassanyar murya ta ce
“Ni na fada maka cewa ba wajenka na zo ba?”
Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude ba. Dr. Fredrick ya zame ya fita, don ya lura Amirun ba zai iya yi mata magana ba idan yana kallonsu.
Ya sake bude ido a hankali ya dubeta, da wani irin sassanyan kallo. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, sabida wasu irin allurai da ta ji suna bin jinin jikinta. Hawayenta na diga a kasa dis-dis.
Ya tara hannu ya taro hawayen, ya ce “Wannan hawayen kuma na mene ne? Ni da kika ce ba kya so na? Ban yi kuka ba, sai ke?”
Muryarshi bata fita sosai, ba don tana kusa da shi sosai ba, da ba zata ji shi ba.

“How dare you want to me to believe you (ta yaya kike so in yarda da ke cewa) kin zo sabida ni ne? Bayan kin fada min ga wanda kike so, ni ba kya so na? Na hakura na tafi, don me Habibu zai takuraki ki biyo ni?
To me kika zo ki yi min? Kin zo ne ki kara min ciwon, ko kin zo karasar da ni zuwa kushewata ne?”
Ta dago sosai ta dube shi, ya yi saurin kauda kai, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanunta a wannan lokacin ba, wadanda suke kamar ‘magnet’ cikin nashi idanun, suke kuma sanyaya mishi zuciya, tare da karya karfin zuciyar duk da yake rikewa da jarumtar zucin duk da yake takama da ita. Har yake ganin zai iya jayayya da ita, ga shi tun ba a je ko’ina ba, ta fara karya lagon zuciyarshi.
Ta ce a sanyaye
“Har airport na bika, dai-dai lokacin da jirginku ya tashi. Ban ce lallai ka yarda da ni ba, amma Allah shaidata ne!”
Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa, ya tattara iya sautin da ya rage mishi a makoshi ya ce
“Mairo!”
Ta dakata, hannunta jikin marikin kofar, amma ba ta juyo ba. Ya yi tari kuful-kuful! sau uku, kamin ya ce “Fushi kika yi? Za ki sake tafiya ki barni? Ciwon sonki ya karasa ni?
Ki yi hakuri idan na fadi wani abu wanda ya bata miki rai, zafin sonki ne ya kawo hakan. Dawo ki zauna tare da ni, ina jin wani sanyi cikin zuciyata, a dalilin tsayawarki tare da ni.
Ki yi wa Allah, kada ki sake barina, har zuwa karshen rayuwarmu. My life has no meaning…… Idan na rasa soyayyarki. I’m impotent….idan ba tare dake ba!

Bana son Habibu ya takuraki ki aure ni, soyayyarki na ke nema, ba da tursasawar wani ba”.
Wannan lokacin ba ta ce komi ba. Ta rasa abin da zata ce, ta kasa tantance shin abin da ta ke ji game da Amirun cikin zuciyarta da illahirin gangar jikinta a halin yanzu, soyayya ce ko kauna ce? Idan kauna da soyayyar ne baki daya, to shi kuma Uncle Junaidu fa? Shi kuma me ta ke masa idan ba so da kauna ba?
Idan haka ne ke nan MAZA BIYU ta ke so ko yaya ne? Soyayya guda daya ce, wadda a halin yanzu ba ta san ko ta waye ba, don haka ba zata ce ba. Amma data tuna halin da Amirun ke ciki, yana bukatar lallashi da kauna daga gareta a daidai wannan lokacin kamar yadda likitanshi yace, sai ta dawo kujerar da ke fuskartarshi ta zauna kanta a kasa. Kamun kai da kunyar Mairon, su ne manyan al’amuran yarinyar da suke kara masa kaunarta.
Ya tabbatar ba zata taba bude baki ta ce, tana sonshi ba, sai dai idan su kwana a hakan, wannan din ma ba karamin burge shi ya yi ba. Domin duk yarinyar da zata budi baki gatsar ta ce da namijin da bai zamo mijinta ba, ina sonka. To wallahi ba matar aure ba ce.

Inda Allah Ya ceceta daga kaifafan idanun Amirun, shi ne shigowar Yaya Habibu, Dr. Fredrick da dattijon da a yanzu ta gane shi ne Alh. Abdurrahman Gaya. Mahaifin Amiru.
Cikin murmushin jin dadin ganin dan nashi cikin yanayin da ya bashi mamaki, zaune sosai bisa gadon ya zuro kafafunshi kasa. Fuskarshi cike da walwala da yalwataccen murmushi ya karaso gare su, shima Amirun murmushin yake yi.
“A’ah sauki ya samu, lallai, kai Mairo ta iya jinya!”.
Amiru ya harare ta, ya ce
“Ni ba wani jinyata da ta yi, sai kuka ta ke yi mini. Kai Yaya Habibu mai yasa ka takurata ta zo? Me ya hada ciwona da zuwan Mairo Nigeria? Alhalin karatu take yi? Da ka kyale ta ai zan samu sauki ne a hankali cikin yardar Allah”.
Habibu ya harare shi ya ce
“Kwarai fa, shi yasa na ga kamin ta zo ana ta janyo maka numfashi”.
Duk suka yi dariya ban da shi Amirun. Da kalaman Habibu suka jefa shi a tunanin anya ya cika namiji? Anya shigowar Mairo rayuwarsa bata maida shi mace ba?
Dr. Fredrick ya ce
“Ya ci abinci Mairo?”
Ta girgiza kai, sannan ta dubi kular abincin da ke kan lokar jikin gadon, ta dauko ta bude, farfesun kaza ne da ya ji kayan kamshi, a daya kular ‘chips’ ne da soyayyen kwai. Tana son ta tambaye shi wanne zai ci a ciki, amma kunya ta hana ta, don haka ta zuba kowanne kadan cikin faranti daban-daban ta mika mishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button