ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau da ya shigo gaishe ta da safe, cikin sakin fuska ta amsa. Bayan sun gaisa ta janyo wata dirkekiyar jarka irin wadda ake zuwa da zam-zam daga Saudiyyah din nan, cike ta ke taf da ruwan rubutu bakikirin da shi ta girgiza ta tsiyayo a kofi ta mika mishi.
“Ungo shanye ka ba ni kofin”.
Ya ce
“Na mene ne Hajiya?”
“Maganin sammu da tsarin jiki ne, ko ba zaka sha ba? Idan ka shanye shi duk wani makaru da ke jikinka zai karye, don haka shanye ka ba ni kofin”.
Bai yi musu ba ya karba ya soma sha a kyankyame, don kam shi Amiru tun fil’azal mutum ne mai kyankyami matuka, ko (spring water) ba kowanne ya ke sha ba.
Tun yana kyankyami har ya zamo masa jiki. Don ka’ida ne kullum ta Allah ya zo gaishe ta, sai ta cika kofi ta ba shi tsawon sati biyu suna hakan. Ya ji ya fara jin wasu sauye-sauye a zuciyarshi akan Mairo, sai dai ko kusa bai alakanta hakan da cewa rubutun da Hajiya ta ke daddaka masa ba ne.
Yau da yamma da ya dawo daga ofishin Daddy inda ya koma zuwa yana taya shi da wasu ayyukan, sabida nauyin Habibu da yake ji ya sanya alakarsu yanzu ta ja baya.
Duk da cewa shi Habibun a nashi bangaren, ya maida komi ba komi ba, amma Amirun gani yake Hajiya ta riga ta gama tozarta shi a idon Habibu, ta yadda har abada ba zasu koma kamar da ba.
Ya yi sallama Hajiya da ke harde cikin kushin tana sauraron labaran Al-Jazeera ta amsa mishi. Ya samu kujera mai fuskantarta ya zauna. Ya dan zamo daga cikin kujerar yana gaishe ta.
Ta amsa mishi da sakakkiyar murya, can kuma ta ce.
“Anya Amiru, rayuwa zata yiwu da hakan? Ace mutum ya yi ta zama, ba ya tunanin samun dan kansa, duk tsararrakinka daga masu ‘ya’ya uku sai masu hudu amma kai ba abin da ya dame ka, sabida idonka ya rufe da son matarka. Alhalin kuma ba zata iya ba ka sanyin idanu ba, sai dai a cika maka masai da kashi, to wallahi bazan yarda da wannan ba”.
Ya dago idanunshi a kankance ya dubeta.
“Hajiya mun isa mu ba wa kanmu abin da Allah bai ba mu ba ne? Sannan ba ki san matsalar nan daga gare ni take, ko daga gare ta ba? Don haka bai kamata ki dau zafi akan al’amarin ba, don Allah Hajiyata”.
Ta ja dogon tsaki tsiiit!
“To ku je asibiti mana? Ko haka za mu yi ta zama cikin jiran gawon shanu? Ai gara a banbance, don a san matakin dauka”.
Da wannan tunanin na maganganun Hajiya ya kwana, har ya soma jin kamshin gaskiya a cikinsu. A shekarunshi ya ci ace shi ma ya aje masu yi mishi addu’a. Har ya soma zargin Mairo ko tana amfani da ‘contraception’. Tunda dama ai tun farko ba sonshi ta ke yi ba.
Ya yi gaggawar kwabar zuciyarshi daga wannan mummunan zargin da ta darsa mishi. Ya yarda da matarsa 100% (Azzannu zambun, wa lau kana hakkun), sai dai rashin damuwarta akan al’amarin ma ai abin dubawa ne, bokonta kawai ta sa a gaba, da son ganin kwalayen ilimi, tare da son hango kololuwar biro da takarda.

Ta murda kofar ta shigo cikin sallama cikin sassalkar doguwar riga baka sid, kirar Dammam, fararen duwarwatsu na ta walwali a jikinta, sannan ni’imtaccen kamshinta na din-din-din ya doki hancinsa.
A kwance yake ‘flat’ bisa makeken gadonsu ya lumshe ido kamar mai barci. Har ta zauna gefen kafafunshi ta soma ja mishi yatsu bai juyo ba. Haka nan ya samu kanshi da jin haushinta babu gaira babu dalili. Ta yi kiranshi cikin tattausar murya, amma bai bude idonshi ya dubeta ba.
Karewa ma kara runtse idonshi ya yi, tareda janye kafarshi dake ciin hannunta, don ba ya son ganinta, ba ya son kamshin turarenta.
Ta yi wa kanta kyakkyawan matsugunni a kirjinshi, ji ya yi kamar ta dosana masa wuta. Ya yi azamar angijita ya ce
“Leave me alone, please!”
Cikin mamaki ta ke dubanshi, idanuwanshi sun hargitse kamar ba Amirun nata ba. Ta ja gefe ta zauna jikinta yana rawa, don ko kadan bai taba yi mata magana cikin tsawa irin haka ba, sannan ita a rayuwarta ba ta iya tashin hankali ba.
Zuwa can kuma ya mike ya soma shiri, ya dan juyo a kai-kaice ya kalle ta.
“Ki shirya, asibiti za mu”.
Ta yi ta maza cikin sanyi ta ce.
“Waye ba lafiya?”
“Idon matambayi ne”.
Abin da ya ce da ita ke nan.
Kamar ta ce, ‘to ba zani ba’, amma kwarjinin Amirun da kimarshi dake cikin idanunta ya hana. Soyayyar da ta ke mishi wata kaddara ce daga Allah da ita kanta bata san adadin ta ba. Ta yadda ba ta iya fushi da duk abin da ya yi mata. To balle ma bai taba yin ba. Idan haka ne ya dace ta yi mishi uzuri, ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba.

Suna tafe a motar amma ba mai ce da dan uwansa uffan, kowanne abin da yake sakawa a zuciyarsa daban ne da na dan uwansa.
Tunanin Mairo shi ne, shin laifin me ta yi wa Amiru haka da zafi, da har ba zai iya budar baki ya fada mata ba don ta gyara?
Shi kansa Amirun ya rasa laifin da ta yi mishi ya ke ganinta bakikkirin da jin zafinta babu gaira babu dalili. Amma ransa na gaya masa rashin haihuwar tane, yazo wani limit na kasa jurewa. Har suka iso babban asibitin Abuja, kalma daya ba ta hada su ba.
Kai tsaye ofishin Dr. Fredrick suka nufa, Amiru ya ce da shi.
“Doctor mun zo ne yau ka duba mana dalilin rashin haihuwarmu, al’amarin ya fara damuna. Sannan Hajiya ta tada hankalinta, idan ba asibitin nan muka zo ba, ba zata barni na zaun lafiya ba”.
Sai a sannan ne Mairo ta cira ido ta dube shi. Yanzu ne ta gano dalilin bacin ranshi. Wato sun fara damuwa da rashin haihuwarta, wanda ita ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Dr. Fredrick ya hada su da Gynaec Doctor da za su gani, wato Dr. Ma’u. Bincike iri-iri Dr. Ma’u ta yi amma ba ta gano wata matsala a tare da Amiru ba. Da ta zo kan Mairo, sakamako ya nuna cewa, ita ce bakin mahaifarta yake a tsuke sosai. Idan har tana son haihuwa, dole sai an yi mata aiki, an bude bakin mahaifar.
Ya roki Dr. Fredrick da Dr. Ma’u lokacin da Mairo ta nufi mota cewa su taimake shi su bar wannan sirrin a tsakaninsu, ba ya son Hajiya ta ji.
Dr. Ma’u ta ce da shi.
“Ai ko ba ka ce ba, amana ce tsakanin likita da ‘patient’ dinsa, insha Allahu ba za a fada mata ba”.
Ya yi godiya ya barsu da alkawarin idan sun dai-daita ranar da za a yi mata aikin za su dawo.

Mairo ta shiga cikin tsananin damuwa. Tashin hankali da rudani. Yadda farat daya Ameeru ya sauya mata. Kamar ba shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai kidimata. Kullum daga fada sai hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko Dina ba ta taba tunanin fadawa ba.
Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da shi dashi ya ke amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa surukarta karfar baka, mai wuyar magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake mawa.
Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura mata da nacin maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke soya zuciyarshi.
Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga damar ba ta zata samu ne.
“Amma Shi Ya ce ‘tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba.
Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu muke jiranta”.
Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida tsakinta.
“Ni fa babu inda zan je”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button