Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????
ABDUL JALAL
WRITTEN BY AISHA HUMAIRA
(Daddy’s girl)
1.1
Bismillahirrahmanirahim da sunan Allah me Rahma me jinkai Allah kayi salati abisa shugabanmu annabi Muhammad salallahu alaihi wassalam
Bayan haka ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wataba nayishine domin nishadantarwa dkuma wa azantarwa kubiyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa
Ina maraba da shawarwari, sharhi, kokuma gyara nagode.
This is my first novel

Misalin karfe biyu na ranaa a cikin garin kaduna, lokacine da rana ta kwalle tayi zafi sosai mutane wasu na hada hadarsu wasu Kuma sun koma gefe suna hutawa, tafiya take a hankali kaman batajin zafin ranar jikinta sanye da uniform take ratsa lungunan anguwarsu harta karaso wani matsaikacin Gida dayake rukunin gidajen layin dayakasance gamayyar masu kudi da masu rufin asiri, a kofar gidansu taci karo da wata hadaddiyar mota baqa, tana ganin mortar tayi murmushi ta shiga Gida da Sauri tundaga tsakar Gida tafara sannu dazuwa kawuna kuma babana, oyoyo da kyakyawar yata kuma ya tagari Cewar wani babban mutum dake zaune a daya daga cikin kujerun wani matsakaicin palour gefensa kuma wata matashiyar matace a zaune a kasa daka ganta kaga mahaifiyar wannan yarinyar saboda kamar dasukeyi, a kasa tazube tana gaida mutumin ya amsamata cikin sakin fuska yata ya makaranta lafiya kalau kawu aniyi mana Hutu yau mungama mock zanshiga ss1, masha Allah Ashe yarinyartawa ta girma shikenan faduwa tazo dai dai da zama kishirya anjima zan koma dake zan tafi muje kimana hutun acan to kawu d fara artata juyo ta kalli mamanta mama yau zan tafi ke Kadai zaki dinga kwana mhmmm Kawai mama tace amma har ga Allah bataji dadi ba batason yarinyarta ta yi nesa da ita amma yadda Alhaji imam yke nunawa yarinyarta so bazata iya cewa a’a ba kasancewar yarinyar yar Dan uwansa ce, ita kuwa murna take koba komai kwana biyu zata huta da fadan mama.
Misalin karfe Biyar na yamma sukashigo garin kano ta dabo jalla babbar hausa, rukunin gidajen sharada NNDC quarters ananne Inda gidan alhaji imam yake, gidane babba Wanda akayiwa gini na zamani gidan yyi matukar tsaruwa, yaran gidanne sukafito domin Tarar mahaifinsu suna masa sannu dazuwa ai daganin shida wadda yake tare suka dau murna, murna farinciki ya mamayesu Nana ce tariqo hannunta tana naji dadi JALILAH Hutu zeyi dadi ???????? ta rungumeta suka shiga cikin gidan, matar gidan da fara arta take fadin sannunku dazuwa yau munyi babbar bakuwa murmushi JALILAH tayi tazube har kasa tana gaida matar amsamata tayi Nanace tajata dakinta tace shiga ki watsa ruwa kizo musha hirar yaushe gamo,
karfe takwas na dare iyalan gidan suka hallara domin cin abincin dare, daga bakin kofa sukajiyo muryarsa kai kai kai wanake gani haka kaman wata Yar kauye nake gani cewar wani matashi dabaze wuce shekaru ashirin da biyuba yayin shigowa palourn dariya suka kamayi wuce nan wlh Niba Yar kauye bace, murmushi yayi yace to Yar birni saukar yaushe Nana tayi caraf tace saukar dazu da abbah yaje yataho da ita hakan yayi kyau Cewar matashin haka sukacigaba da hirarsu gwanin sha awa.


Zaune yake a cikin parlour yadora qafa daya kan daya yanata busa shisha sekace salansar tifa ta hanci ta baki gefensa mp ce ke fitar da sautin kida a hankali se lumshe ido yake alamu yanayin yayi masa dadi wayarsa ce ta dau ringing yanaji har ta katse be kulaba takuma ringing ya kallah seyaga mum a jiki ya kauda kai yacigaba da busa hayaqinsa karo na hudu wani kiran Yakuma shigowa a fusace yadaga wayar what’s is it ne mum kinkira ban daukaba ai seki hakura kinsan INA wani abunne haba Dan Allah ???????????? jalal kazo yanzu inason ganinka akace daga daya bangaren am having rest now komene let’s meet tomorrow bejira mezata kuma cewa ba ya kashe wayarsa yasata a flight mode yacigaba da babbakar hayaki qaramar wayarsa ce itama tafara ringing yaja wani dogon tsaki ya dakko Dan duba waye jeje ne akan screen din wayar dagawa yai kara wayar a kunnensa be maganaba ya danyi shiru yace karkutafi gani nan…
……………
Jalilah tawayi gari a cikin garin kano, da garin Allah ya waye tareda Nana suka Shiga kitchen suna hada breakfast sunayi suna hirar makaranta Nana CE ta dubi jalila tace sister dama kiyi zamanki a kano sekicigaba da karatun a an an kinga bani da Yar uwa mace se jimmai house girl din Ummi inajin dadin zama da ita amma ita kullum cikin yawon biki take, hmmm ajiyar zuciya jalila tayi taace idan nadawo kano mama fa in barta ita kadai a Kaduna naana bazan iyaba kam, Dama nasan bazaki yaddaba dallacan matsa kiban guri murmushi kawai jalila tayi, suka cigaba da aikin dasuke, wajenkarfe shadaya suna dakin Nana suna hira jalila take cewa gaskiya Nana garin kano tanada kyau matuka na Dade rabona da kano, ai ba kya ziyara taya zaki Sani ba kya zumunci kullum kina like da mama, kudin zuwa kuke ai hargara ni kuma ai bazuwa kuke ba dalla bari mu tambayi Ummi muje kiga gari Yar kauye kawai wuce nan wallahi kema Yaya jawwad dince ko dariya sukayi sukasa hijjabai suka fito parlour Ummi ta dubesu se INA Ummi zamuje gidansu nusaiba ne jalila ta danga gari kinsan kifin rijiyace, murmushi Ummi tayi tace to adawo lafiya akula da kai kuma karku Dade to Ummi sukasaka kai suka fita sunata hirarsu gwanin sha away Layinn shiru se kukan tsuntsaye dasuke shawagi akan manyan bishiyoyin dasuke cikin wasu daga gidajen dake unguwar suna tafiya suna hira,
a guje wata mota ta taho da gudu kaman zata tashi sama se uwar kura datake tashi kwata² tukin rashin hankali akeyi galalala jalila tabi mortar da kallo Nana ta tabota yadai tab amma nana direban motan nan bashi da Rabin hankali in akasamu akasi ya bige wanifa, hmm ko a jikinsa jalila me tukin nan baya ganin kowa da kima a anguwarnan babu me fadamasa yaji haka rayuwarsa take ko iyayensa basu ISA dashiba Yaya jalal kenan abokin Yaya jawwad ne, tab amma ya akayi Yaya jawwad yake abota da irin wannan Sam halinsu be kamaba, jalila kenan kema kyafada anyi2 arabasu abu yaci tira Allah ne yahada jininsu yana matukar son Yaya jawwad, hmmm Allah y kyauta Cewar jalila Nana tabita da Ameen, haka sukaje suka dawo suna ta hirarrakinsu, wayar hannun Nana Ce tafara ringing ta daga tayi sallama jalila bata iya jin abinda ake fada a wayar se dai murmushi da Nana tayi tace sorry mun Dan fitane sister tace tazo muka fita bari mu biyo, ta kashe wayar jalila zomuje wata qawatace tazo kai wannan hutun zemun dadi gaki ga ilham mtseww kekin cika gayyar kawaye wlh ni nagaji gaskiya, Dan Allah kizo muje to shikenan muje sarkin naci.
Kofar palourn ya tura ya shiga yanufi kitchen kai tsaye ya Shiga yadakko abinci a Warmer’s yana shirin fita jalal yaji ankira sunansa be waiga ba yatsaya INA ka kwana jiya matar ta jefomasa wannan tambayar yayinda take sakkowa daga kan bene ba magana nake maka ba INA ka kwana jiya juyowa ya kalleta a club yafada kansa tsaye batare da wata shakkaba jalal wato kai ko kimata baka gani kankaa tsaye kake gayamin a club ka kwana ohhh my God mum tambayata fa kikayi nagayamiki shima kuma laifi nayi I don’t want the way u are treating me mum kibarni inyi abinda ya dace dani cikin daga murya da gadara yake maganar Wanda yayi dai² da shigowar su jalila tundaga waje suke jiyo hayaniyar jalal da mahaifiyarsa abin yyimatukar bawa jalila mamaki itakuwa Nana ko a jikinta Dan ta saba jin irin wannan rashin ta idon da abokin yayanta yakeyi yaja wani dogon tsaki yafito waje, mommy INA wuni yawwa sannunku nana, mummy INA ilham tamin waya tazo nuni mummy tayimana da dakinta cikin damuwa ta koma sama, mukuma muka nufi dakin data nuna mana muna Shiga suka rungume juna suna murna, nana wannan sister dinkice kuna kama matuka eh kanwata ce sannu ya sunanta jalila nana tabata amsa hmm nice name thank u kawai jalila tace amma hankalinta na kan abinda tagani yau wannan Sa insa tsakanin da da mahaifiyarsa abin yabata mamaki kuma yadameta,
bayan sun koma Gidane jalila ta kalli nana tace nana gidan da mukaje dazu wlh wannan din nan bashi da tarbiyya wallahi wakenan kike nufi oho ban San sunanshiba wannan din nan me dogon hancin nan kaman tattasai tooo dariya nana takamayi tattasai ni banganeba mtseewww is not joke nana y kalli mahaifiyarsa yace mata a club y kwana yana mata shouting haka, mhmmn bakiga komaiba India jalal ne jalal ta maimaita sunan yeahp shine me driving a mortar nan dazu kafin kibar kano zakigane wayeshi bakiga komaiba, amma a haka Yaya jawwad yake abota da shi jalila ta tambaya cikin tuhuma, jalila ba se lallai hali yazo daya ake abota ba soyayya da shaquwa gamon jinine tsakaninsa da Yaya jawwad Allah ne yahada jininsu, Yaya jawwad se yasaka jalal ABU yayi amma mummynsa bata isaba, ga shaye shaye a cikinsa yawon club ba Wanda ba yayi, tabdijan nana wannan abotar bame yiwuwa bace inji jalila kaman yaya, basu dace da abotar ba wannan Sam bashi da tarbiyya Dan haka sena rabasu bashida tarbiyya Nana tirkashi!!!!!!!!!!!
More comments more typing

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button