ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu ya kara sanya mishi jin son taimakonta.

Mairo da ta fito ‘pref’ ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta ‘essay’ dinta mai taken ‘My first day in secondary school’. Da jagwalgwalallen turancinta mara ‘tenses’ har haduwarta da Uncle a aji ta rubuta, inda ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce “shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba ra’ayinta ke nan ba.
Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta.
Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi ‘assignment’ din shi ba sai da period dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama Bedi. A zahiri duka ‘yan ajin sun fi ta iya Turanci, da kula da ‘tenses’ sabida su sun sami kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To amma idea da ke cikin rubutun Maryam fasaha ce tsagwaronta.
Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana nuna mata kura-kuranta, tare da cewa “Matsalarki daya ce a Ingilishi (tenses), don haka darasinmu na yau tenses ne”.
Nan da nan ya fara darasi inda Mairo ta dauki dukkan hankalinta ta likawa Uncle. A yau da aka fita break ma ba ta yi saurin fita ba, ta zauna ne tana aikin lissafi (maths). Uncle Junaid ya kwankwasa desk dinta, ta yi hamzarin dagowa kamin ta yi murmushi ta ce “Uncle dama ba ka fita ba ne?”
Ya ce “A’ah na fita, dawowa na yi. Tun daga staff room na hango ki kina rubutu, zuwa na yi na gaya miki ki daina zama cikin aji yayin da kowa ya fita. Komi na makarantar nan cikin tsari yake, yanzu lokaci ne na cin abinci ba na yin aiki ba. Idan wani bai ga abinsa ba yana iya cewa ke ce”.
Ta rufe littafin ta mike ba tare da ta ce dashi komi ba. Ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ya ce, “Maryama”.
Ta juyo cikin damuwa, ya ce, “Ina fatan ba ranki ne ya baci ba?”
Sai ta koma dariya, ta ce “A’ah Uncle”.
Ya ce “To mai yasa kika yi shiru?”
Ta ce “Ka yi hakuri Uncle Junaidu”.
Ya yi murmushi ya bi hanyar kofa shi ma ya na kissimawa a ranshi Maryam na daga cikin miskilan yara.
Cikin sati biyu kacal Mairo ta fahimci tsarin komi na makarantarsu, sai dai ma ta nuna wa wani. Babu ruwanta da su Kausar, duk kuwa da basu fasa yi mata izgilanci ba, a daki ne ko a aji. Sai dai su kansu sun san akwai wani aminci, ko kuwa shakuwa ta musamman tsakanin Maryam da Uncle, don haka basa yi mata a gabansa. Saboda Maryam Uncle Junaid ya kirkiro tutorial class da yamma da yake yi akan darasinsa English da darasin Uncle Wahhab (mathematics), wanda ba karamin taimakawa Mairon ya yi ba.
Duk wasu matsalolinta akan karatu Mairo ba ta shayin gayawa Uncle Junaidu shi kuma ya tsaya mata kamar Yayanta. Shi kansa bai san mai yasa ya tsani Kausar da Nabilah ba, tun daga ranar da ya lura sune kawai matsalar Maryama cikin makarantar.
Ita kuwa kullum kokarinta shi ne, ta boye abin da suke mata, kada ya gane. Don duk ranar da ya hora su sabida ita, idan sun koma daki akanta suke hucewa. Rannan da ya sa su noma sabida sun karya bencin ta karfin gaske, duk don kada ta zauna kusa da su, da suka komo hostel suna ta digar da gumi. Sun yi jawur sabida wahala, Kausar ta yi kuka ta ce “Wai Nabilah wannan bakauyar kanwar uban Uncle ce ne?”
Nabilah ta ce “A’ah, ina jin tare aka haife su, don shi ma da alama dan talaka ne ya soma daukar albashi ya je ya sayo gwanjo yana zanzarewa”.
Kausar ta ce “Uban wa ya gaya miki? Abokin Yayana ne tare sukai karatu, dan chief justice Atiku Galadanchi ne. Har gidansu na sani sanda muka zo Kano daga Jos da Yaya Yusuf bikin wani abokinsu, abin da na kasa ganewa shi ne, mai wannan billager din ta ke gaya masa yake damuwa da ita? Ni kam da nasan har da irin wadannan a makarantar nan ai da ban yarda Daddy ya kawo ni ba”.
Nabilah ta ce “Ke kika ga zaki iya, amma ni nan idan an yi hutu bazan dawo ba, Edcel collage zan koma. Minjibir ta rube, ta zama ta yaku-bayi”.
Suka kwashe da dariya, Mairo dai na jinsu ba ta dago ta dube su ba, sai rubutunta ta ke kamar alhudahuda.
Ranar ziyarar ‘yan makaranta, wato bisiting day ta zo. Kowanne dalibi ya sha wanka ya yi fes, ya fito neman nasa. Mairo dama ba ta sa a ka ba, tasan Babanta da Innarta duka ba su san da wata ranar ziyara ba. Tunda ko radiyo ba su damu da su saurara ba, don haka ta samu can wani gefe gindin wata bishiyar goba mai inuwa ta zauna akan benci tana nazarin littafin the boy slabe da ta karbo a library.
Can anjima ta daga kai ta kalli motoci na gani na fada da ke ta fakin yara na rugawa su rungume iyayensu, sannan a soma kokawar fito da manyan ma’adanan abinci da katon-katon na kayan masarufi ana ajiyewa.
Waje ya cakude kowa na nemawa ‘yan uwansa wurin zama, babu wanda yasan da ita, a lokacin ne ta ji babu dadi, ta ji kewar Innarta. Idanunta suka cicciko da kwalla. Kamar daga sama ta ji muryar Uncle a kanta ya ce. “Mariama”.
Da sauri ta dago tana kokarin boye kwallar idonta, Uncle ne rike da manyan ledoji guda biyu, a bayansa wata yarinya ce budurwa da akalla zata girme ta da shekaru biyu da kuma wani yaro da zai yi tsara da ita, su kuma niki-niki da manyan kulolin abinci da picknick cooler wato irin kular nan da ake zuba lemuka da kankara mai hade da dan famfo a jiki. Ko ba ta tambaya ba tsabar kamanninsu da juna ya gaya mata wadannan yaran kannen Uncle Junaid ne.
Ta zame kasa tana gaishe shi, ya ce “Kuka kike ko Maryama, sabida mene?”
Ta share kwallar idonta dai-dai lokacin da shi da budurwar suka zauna akan bencin nata, ta ce “Lah Uncle ba kuka nake yi ba”.
Ya ce “Mai yasa ‘yan gidanku ba su zo ba?”
Ta ce “Ba su san ana yi ba”.
Ya ce “To ki fada min adires na garinku ni da kaina zan je na taho da su a bisiting na gaba. Yanzu dai ga kannena Ilham da Sagir sun zo miki bisiting, are you o.k?”
Farin cikinta ya gaza boyuwa, bakinta ya gaza rufo don dadi. Ba tasan mai zata ce da Uncle Junaid ba, sai ta kama hannun Ilham tana murmushi, ta ce, “Na gode Ilham”.
Ilham ta ce “Ba komi Maryam, yadda Yaya Junaid ke ba ni labarinki sai na dauka zan ga wata babbar budurwa, ashe kamar Sagir ce Maryama?”
Ya mike yana cewa “Ki tabbata ta ci abincin, kuma ba ta yi kewar kowa nata ba, I know you Ilham. Zan dawo nan da awa daya mu tafi”.
Ta ce “To Yaya Junaidu”. Tana murmushi.
Ilham ta ce “Amma ko kannenki ba su zo ba Maryam?”
Ta ce “Ba ni da kanne, ni ce auta a wurin Innata”.
Suka ci gaba da hira, Ilham na kokarin cika umarnin Yayanta na ganin cewa, ba ta bar Maryam da kewa ba kamar yadda dan uwanta ya umarce ta. Ta zuba mata abinci mai rai da motsi cikin filet da kirjin kaza ta mika mata tana cewa “Ci maza kamin Yaya Junaidu ya dawo ya tuhume ni da barinki da yunwa”.
Dariya ta yi, da ta lotsa kumatunta, tana tambayar kanta ko wane matsayi Uncle Junaid ya ba ta haka a wurin ‘yan uwansa? Girmansa da kimarsa ya karu a zuciyarta. Tana ganin bayan Baba da Inna da Yaya Habibu ba ta da kamar Uncle Junaidu.
Ya dawo da wata leda mai dauke da ruwan (Faro) roba uku masu sanyi ya mikawa Ilham. Suka sha dukkansu sannan suka yi haramar tafiya, Mairo ta ji babu dadi.
Cikin ‘yan awoyin da ta yi da Ilham sun saba sosai. Ta bude baki cikin al’ajabi tana kallon Uncle da ya ce duka wannan kayan nata ne. Abinci kuma daga mahaifiyarsu ne sai ta rasa irin godiyar da zata yi wa Uncle din nata.
Bayan tafiyarsu ta kinkimi kayanta daya bayan daya ta nufi hostel. Cikin ledojin ba komi ba ne sai biskit na kwali kala-kala da crackers na shan shayi irin wadanda ta ke ganin su Kausar na ci, dayar kuwa alawoyi ne, cakulet kala-kala masu dan karen tsada da katon na irin taliyar da ta ga dalibai suna jikawa (indomie), sai katon na lemon gwangwani (Rani).
Baki ta bude cikin matsanancin firgici, ba ta taba tsammanin wai ita Mairo zata taba cin irin wadannan abincin ba a rayuwarta. Cikin kulolin kuwa bayan abinci akwai soyayyun kaji wadanda suka soyu rakau yadda za su jima ba su lalace ba, cin-cin mai nama (meat pie), cake da sandwitch masu yawa sosai. Kenan godiya ga Uncle Junaid wadda ba ta karewa.
Mutanenta suka shigo, wani abin mamaki kulolinsu duk iri daya ne da nata, sai kala da ta banbanta. Suka yi kasake! Cikin mamaki ganin irin garar da ke gaban Mairo wadda ko a mafarkinsu ba su zata ba. Abin da suka dauka shi ne, ramar da ta ke kwadawa mai tsamin tsiya da kanzo su za a karo mata. To sai ga sabani ga tunaninsu, ina ruwan Allah Mai azurta bawa.
Mairo dai jeren kayanta ta ke a loka, ba ta kula su ba. Nabilah ta kasa shiru ta ce, “Kausar yau billager ta shigo gari”.
Kausar ta ce “Ke ina jin ‘charity’ ne daga (MSS), ba ki san ta shiga MSS ba? Kungiyar ‘yan a bamu saboda Allah?”
Ita yaran sai suka koma ba ta dariya sabida yadda suka sa mata ido babu gaira babu dalili, ko mai ya yi masu zafi da ita? Allahu A’alam.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button