ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Habibu ya karkace kai ya yi ta ba Innarshi hakuri, ya ce “Inna ku yarda da ni, ba ni da nufin cutarku, sai dai ma na yi kokarin ganin duk abin da zai zamto cuta a gare ku na yake shi iya karfina. Ina nufin Maironki da alheri ne, bayan wannan ba wani abu. Ke da kanki wata rana za ki gane gata na yiwa rayuwar Maryam. Don Allah Inna ki sauko ki yafe min, kisa min albarka!”.
Zuciyarta ta yi sanyi lakwas, ta ce “Ai shi ke nan, nasan iyakar gaskiyar ke nan, laifina shi ne, ina son Mairo da yawa”.
Ya yi murmushi ya ce “Hakan ma ba laifi ba ne. Sai dai ki yi kokari kada son da kike mata ya sa ki kasa lankwasata. Ni ma ina son Mairon ki, son da bana yi wa kowa a duniya, amma idan har da gaske ina sonta, dole in inganta mata rayuwa da gishirin zamani, wanda idan babu shi miya duk dadinta lami ce. Wannan gishirin kuwa ba komi ba ne, face wannan ilimin dana ke so Mairo tayi. Shi ne zai haskaka mata ragowar bangarorin rayuwarta, tasan kanta, tasan inda ta sa gaba.
Amma a yanzu wallahi Mairo ba ta da maraba da ‘ya’yan birrai”.
7/28/21, 10:59 AM – Buhainat????: 80

Dariya Inna ta yi, ta ce “To Allah Ya taimake mu ta kimtsu”.
Ya ce, “Amin–amin, ko ke fa Innata? Ni ma karatun zan tafi…” Ya warware mata zare da abawa.
Ga mamakinsa sai ya ga damuwa karara ta bayyana a kyakkyawar fuskarta, ita da a kullum, ta ke nuna ba ta damu da shi ba. Ya shiga kwantar mata da hankali cikin tausasan kalami, yana nuna mata shekaru shida kamar yau ne, idan da rai da lafiya. Da kyar ya samu ta sa ma abin albarka.
Da wannan Habibu ya koma Kano ya ci gaba da shirye-shiryensa, da taimakon Baffansa. Cikin watanni uku kacal komi ya kammala, ya zo wa iyayenshi sallama.

Ya ji dadin yadda ya ga Mairo cikin wankanta fes! Ba ta kuma yi masa wannan damuken oyoyon ba, an fara nutsuwa ke nan.
Ya yi murmushi, ya ce, “Mairon Inna ‘yan makaranta, ya ya dai?”
Ta yi murmushi ta kawar da kai ba ta ce komi ba. Ya kamo hannayenta ya ce “Ba ki ga yadda kika soma sauyawa ba? Ina fatan duk runtsi za ki dage da zuwa makaranta? Zan tafi karatu Mairo, sai Allah Ya dawo da ni kimanin shekaru shidda a nan gaba. Ki kula da Innarki, ki dinga tayata aiki, ba wasan ‘yar bebi ba kin ji Mairo nah?”
Ta shiga damuwa sosai, nan da nan sai ga hawaye rau-rau a idanunta. Ta ce “Yanzu Yaya Habibu shekaru shidda zan yi ban ganka ba? Ina zaka je? Mai yasa ba zaka ci gaba da zama gidan Baba Abbas ba kana zuwa makarantar a can?”
Ya ce “Kamar yau ne Mairo za ki ga na je na dawo, idan dai da rai da lafiya. Ki kula da kanki, ki dinga wanka kullum, ki dinga yanke akaifarki ta kafa da hannu duk sati. Ki kuma dinga wanke gashin kanki shi ma duk sati, kin ji?”
Ta ce, “Na ji Yaya Habibu, Allah Ya dawo da kai lafiya”.

Ya ji dadi sosai, bai zaci Mairo tana da dan hankali ba ko yaya ne, har ta yi wa mutum addu’a. Ya sa hannu a aljihunsa ya ciro naira ashirin ya bata, ta yi ta murna ta je tana nunawa Innarta.
Haka Habibu ya tafi cike da tunanin Mairo. Yana addu’a, Allah Ya sa ta dore da hakan. Watau turbar da ya sanyata.
Washegari ya tashi zuwa Malaysia, inda ya samu gurbi a Unibersity of Malaya.

Ya sha wuya matuka kamin ya samu ya mance da tunanin gida. Da taimakon abokinshi Amiru wanda shi ma dan Kano ne ya samu ya soma fuskantar karatun, amma babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai tuna Mairo ba.


BAYAN TAFIYAR HABIBU
M
alam Bedi tsaye yake akan kafafunshi kan karatun Mairo don cika alkawarin da ya daukarwa Habibu. Da taimakon Allah Mairo ta saba da zuwa makaranta, kuma lokuttan makarantar sai ya shafe lokacin da ta ke samu ta hau bishiya ko ta yi wasan ‘yar tsana.
Idan ta dawo makaranta karfe daya na rana wanka zata yi ta ci abinci, ta yi sallah. Karfe biyu cikin ajinsu na islamiyya ya ke mata. Ba kuma za su taso ba sai goshin magriba, don haka ranakun alhamis da juma’a da yamma kadai ta ke samun hutu. A cikinsu kuma tana tare da Innarta suna ayyukan gida wadanda ta alkawarta wa Yaya Habibu taimakawa Innar.
Rannan Mairo na surfen masara Inna Hure tana bakacewa, Mairo ta aje tabaryar ta ce “Oh Inna, Yaya Habibu yau watanninsa bakwai ke nan, yana can a cikin Turawa”.
Inna ta ce “Wa ya ce miki a Turai yake? Kasar Larabawa ne”.
Mairo ta yi murmushi, ta ce “A’ah Inna, rannan na tambayi malaminmu na makarantar book, a ina Malaysia ta ke? Ya ce min Asia ne, can wajejen India da Pakistan”.
Inna ta kama baki ta ce “Ke Mairo, yaushe kika iya Turanci haka?”
Mairo ta ce “Ba Turanci na yi miki ba Inna, sunan kasashe na fada miki”.
Wani dadi ya kama Inna Hure, ba tasan sanda ta ce “Kai Allah Ka sakawa Habibu da alheri”

MARYAM BEDI, ta ci gaba da karatunta cike da himma da kwazo. Takan sanya wa ranta cewa, kawai Habibu na kallonta, yana jin dadin kwazonta. Yana kara mata karfin gwiwa. Ba ta yarda wai shekaru shidda zai yi bai dawo ba. A ganinta shi ne Habibu na iya dawowa yau, ko gobe, don kawai ya rutsa ta, ya ga irin kwazonta.
Saboda haka cikin shekara guda kacal, Maryam Bedi, ta zama zarrah a ajinsu na boko, kan gaba a ajin islamiyyah, wadda ke da haddar izfi ashirin na Alkur’ani a cikin kanta.
Sauran littattafan addini kuwa idan ta bude su tana karantawa tana fassarawa Inna tsarki da alwala, da irin sallar khashi’ai da sallar da ake dunkulewa a jefowa bawa kayarsa, tun kamin ya tashi akan dardumarsa. Sai Inna ta sa habar zaninta tana share hawaye, ta ce “Ba karamar cuta na so na yi miki ba Mairo”.

Shekaru uku ke nan cif da tafiyar Habibu, kuma a yau ne ranar saukar su Mairo. Ta sha wanka da sabon dinki na atamfa (hitarget) da suka yi anko gaba dayansu. Ta dora wani sabon farin hijabi akai, wanda ya tabo har gwiwarta. Ta azalzali Innarta ta yi sauri ta gama shiryawa su tafi kada wajen zama ya cika ta rasa inda za ta zaunar da ita. Innar kuwa sai sake murza kwalli ta ke a idanunta yadda zata fito radau!
Ta kuwa fito din, sai kyallin wanka da basilin ta ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu’ar samun nutsuwa cikin zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al’ummar kauyensu wadanda ake nufin ta yi karatu a gabansu.
Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba, yana ta ware ido don ganin ta inda Mairo zata bullo.
Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar da ita, sannan ta karasa cikin ‘yan group dinsu suka yi sansani.

Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu’a, daga limamin garin Gurin-Gawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur’ani cikin daddadar kira’arta kai ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi, wato ayar nan ta “Muhammadurrasulullah…….”
Gaba dayan jama’ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa aya aka dauki kabbara kowa na cewa “Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi”.
Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce babar Mairo, sai gaisawa suke da ita. Yayin da ‘yan bakin-ciki, wato wadanda ke da ‘ya’ya a makarantar ba a kuma kirawo ‘ya’yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban karamar hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi tiryan-tiryan cikin kira’ar da ta fi ta malamin.
Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da’a a gaba dayan daliban shekararsu. A sa’ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin gabatar da jawabinsa na babban bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi
“Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren ‘yammata ta gwamnatin tarayyah da ke Minjibir”.
Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa kansa don farin ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da Chairman.
Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara daurewa. Ta shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu. Malam Bedi ya gabatar musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da zana jarrabawar fita firamare. Ya kare da cewa.
“Amma fa makarantar ta kwana ce”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button