ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Dai-dai sanda ya debo shanyayyun idanunshi ya dora a kanta, sannan ya mika hannu ya karba. A hankali ta ce
“Ba zaka wanke baki ba?”
Cikin kankanuwar murya shima ya ce
“Kin bani abin wanke bakin na ce ba zan wanke ba?”
Ta ce
“Ai ban san inda ya ke ba”.
Alh. Abdurrahman da kansa ya bude lokar ya fiddo sabbin burushi da makilin ya mika mata, ta bude ta shafa jikin burushin, Yaya Habibu ya mika mata roba. Tana zuba mishi ruwan robar ‘swan’ yana wankewa har ya gama, sannan ya soma cin abincin. Shi kanshi likitan ya yi mamakin yawan abincin da Amiru ya ci, wanda tunda aka kawo shi sai yau ya ci, “lallai so ba dama”. (Ya ce a zuciyarshi) sai ruwa ake kara masa mai dauke da sinadaran abincin maras lafiya.
Hajiyar Amiru ta shigo, bakinta ya kasa rufo, ganin Amirunta na cin abinci, alamun sauki sun bayyana sosai a gare shi.
Ta ce
“Kai masha’Allah, har abinci ake ci? Lallai sauki ya samu (don ita ba ta san musabbabin ciwon Amirun ba)”.
Ta kalli Mairo da fuska ma’abociyar walwala, ta ce
“Ina muka samo ‘yar kyakkyawar budurwa?”
Mairo ta dukar da kai, Alhajin ya ce,
“Kanwar Habibu ce, kuma surukarki insha Allahu”.
Murmushinta ya fadada sosai zuwa dariya, ta ce
“Da gaske?”
Ta juya ta kalli Habibu
“Na ce da gaske ne Habibu?”
Ya yi murmushi ya ce
“Idan Allah Ya yarda”.
Kunya a wajen Mairo, kamar ta nutse cikin kasa. Hajiya A’isha ta kamo hannunta ta rike cikin nata cike da matsananciyar kauna da kulawa.
Ana haka Dina da wasu daga cikin kannen Amiru suka shigo, don haka dakin ya yi albarka, ba masaka tsinke, wanda ke nuni da lallai Amiru dan dangi ne. Kowa na fadin albarkacin bakinshi. Akan yanayin jikin Amirun. Ba su bar asibitin ba sai dare, aka barshi da Habibu wanda shi yake kwana da shi.


8/5/21, 3:11 PM – Kawata: D

Awashegarin daurin aure, wato lahadi, tun safe motocin daukar amarya zuwa garin Gaya suka iso. Dina ta shirya amarya cikin fararen liffaya na Larabawan Mouritania, ta fesheta da turarukan ‘gibenchy’ su Habiba da Hajara suka sanyata a tsakiya, Dina na gidan gaba suka nufi garin Gaya.
Anyi musu tarba ta GIRMA, a gidan sarkin Gaya na lokacin, wanda ya kasance kaka ga Amiru, tunda kuwa shi ya haifi Alhaji Abdurrahman, dangin Mairo sun tabbatar Mairo ta yi aure da dan dangi, wanda ake so, ake kauna kwarai, ake kuma son abin da yake so, sannan aka san mutumcin dan Adam.
Kwanansu uku ana shagalin biki irin nasu na masarautar Gaya, kuma fulanin usli. Mai martaba Sarki Abdulkarim Sarkin Gaya III ya yi wa amarya kyautar bajimai uku da sabuwar mota.
Washegari suka nufo Abuja inda aka shiryawa amarya gidanta cikin gidan surukanta, bangare guda, wanda dama tun sanda za a gina gidan an gina shi ne musamman sabida Amirun.
Duk da dai gidan ba ya bukatar komi, wannan bai hana Habibu da Alh. Abbas yi wa Mairon su gata ba. Dakuna uku manya-manya aka ba su suka shakewa Mairo da dukiya.
Sai dai fa ba wai rambatsau ba, a’ah, komi ya dace da muhallinshi. Cikin tsari mai burgewa da ban sha’awa, sannan sun kawota da gararta (trailer) guda. Lokacin da suka shigo wajen Hajiya Aisha aka fara kai Mairo, inda dukkan dangin ango suke tare da Hajiyar a babban falonta.
Duk kannen Amiru guda goma sha biyu na ciki da na waje sun hallara, suka karbi amaryarsu cikin mutuntawa da kamala. Daga nan sai sassan Daddy wanda ya dade yana yi musu addu’a ta neman dacewa a duniya da lahira.
Daga nan aka taho da amarya bangarenta banda kuka da shessheka ba abin da ta ke yi. Ta kama Dina ta rike tamau, ta rantse ba zata tafi ta barta ba, sai dai su koma tare.
Dina na dariya ta ce
“Ina kika taba jin anyi haka Mairo? Ai auren ke nan, YAKIN MATA…… Ko ba ki ganin nima namu gidan na baro na ke zaune da Yayan ki, a inda ba ni da kowa? Ke kuwa fa? Ga ki ga su Hajiya, ga su Amina, ko su kadai sun isheki debe kewa. Duk lokacin da kike son zuwa Kano za ki je”.
Cikin kuka ta ce
“Yanzu Aunty Dina ni da ku shi ke nan? Ni da su Little Mairo shi ke nan? Sannan ba zan koma makaranta ba?”
Dina ta ce
“Idan na ce za ki koma makaranta, ko ba zaki koma ba na yi karya, sabida a halin yanzu ba mu da iko da ke, sai abin da mijinki ya hukunta a gare ki. Yara kuwa na yi miki alkawarin da zarar sun samu hutu zan kawo miki su. Ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki Amiru is a nice person”.
Sabah ta yi murmushi, ta ce
“Sai ma kin zauna da shi for a little while…”
Dina ta ce
“To kinji ba, kannenshi ma sun shaida”.

Wayarta ta hau ruri ta yi murmushi
“Ni ma nawa tsohon angon kirana yake yi in mishi tausar gajiyar da kujuba-kujubar aurenki ya sanya shi. Don haka amarya sai ince, asubah ta gari”.
Tana ji tana gani Dina ta fice, ji ta ke kamar ta dora hannuwa aka ta ce “Wayyo Allah”. Ko ta sami sa’idah.
Ya rage daga ita sai su Amina, don su Hafsat kannen Dina duk sun tafi tun dazun. Nabilah dama ba ta taho Abuja ba, daga Gaya suka nufi gida ita da Isma’il.
Suna so ta yarda su yi hira, amma amaryar tasu ta ki sakin jikinta. Ganin abin ta ke kamar a mafarki, wai yau ita ce a gidan wani mijin ba Uncle Junaidu ba.
Ta yi saurin yin istigfari da wannan mummunan tunanin ta amince, ta yarda da kaddararta. Ta amince haka Allah Ya rubuta musu dukkaninsu. Zata koyawa zuciyarta juriya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata.
Hajiya ta yi kiran wayar Amina, ta ce duk abin da suke yi su bari su taho gida haka dare ya yi. Dukkansu suka mike suna yi mata sai da safe Hajiya na kiransu. Ta rike mayafin Sabah tana kuka sosai har ta karyawa Sabah zuciya, ta ce su tafi zata taho.
Ta koma ta zauna ta ce “Haba Antinmu? Ya ya kike abu kamar karamar yarinya ne? Amare yanzu ba sa kuka, sakin jiki suke a sha soyayya. Kuma ni kinga idan ban tafi ba zan yi laifi wurin Hajiyarmu, don haka ki yi hakuri na tafi na yi miki alkawarin gobe da safe zan dawo idan Allah Ya kaimu”.
Haka ta kalallameta da dadin baki ta samu ta gudu. Ya rage sai Mairo kadai cikin katafaren gidanta, daga ita sai halinta. Ji ta ke kamar an kawo ta kabarinta. Don haka ta ce bari kawai ta yi ibada ko ta samu sanyin zuciyarta.
Ta mike a hankali, ba tare da ta ajiye nadin laffayar da ke jikinta ba. Ta nufi kofar da jikinta ya ba ta bandaki ne, ba don ta saba da ire-iren wadannan wuraren ba, da hakika ta tsaya kauyanci. Komi na bandakin wanda ya kasance (Jacuzzi) kalar ruwan hoda ne, watau ‘pink’ kamar yadda makeken bed room din shi ma ruwan hodar ne da ratsin fari.
Ta dauro cikakkiyar alwala ta fito. Ba tare da ta tsaya neman darduma ba ta nemi wani gefe a can wani korido na dakin ta tada ikama. Sallolin neman biyan bukatar duniya da na lahira da neman dacewa a rayuwar aurenta ne ta ke yi. Cikin sujudunta tana mai yi wa Babanta da Innarta addu’ar samun rahma da gafarar Ubangiji.
Cikin tahiyarta ta ji alamun ana taba kofa, kafin cikin nutsuwa ta ji an murda kofar an shigo. Angon ya bayyana a dakin cikin fararen kayan barci.
Dai-dai lokacin da ta yi sallah ta mike ta kara tada sallah, ya aje kwali da tambulan din da ke hannunshi, shi ma ya shiga ya dauro alwalar ya cimmata suka ci gaba da sallar tare. Agogon bango ya buga karfe biyu dai-dai na sulusin dare lokacin da kowane mai rai yake neman hutu, amma ga wadannan ma’auratan abin ba haka yake ba.
Sun fada wata duniyar tunani ta daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Abin nufi, kowanne da tunanin da ke cin ranshi. Ba auren sha’awa ya yi ba, auren so da kauna ya yi. Don haka babu sha’awar Mairo ko yaya a tare da shi a daren yau.
Ya dauko kwalin ‘fresh milk’ na madarar ‘oldenburger’ da ya shigo da shi ya tsiyaya a kofin ya mika mata. Ba tare da ta tashi daga inda ta yi sallar ba, ta mika hannu ta amsa. Ya sauko daga gefen gadon ya yi zaman rakuma a gabanta. Ya dauki dukkan hannuwanta ya rike cikin nashi. Wannan ya haifar da tashin tsigogin jikinta duka a lokaci daya.
Ta samu kanta cikin matsananciyar sha’awar mijinta Amiru, wanda sassanyan kamshinsa na turaren ‘Miyaki’ ke kara dagula mata al’amura, dama yaya lafiyar kura, balle an tsokaneta, amma ga shi Amirun, abin ba haka yake ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button