ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko’ina kayan Ladidi ne a watse, nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta ga inda zata dosana duwawunta ba a dakin, don haka ta aje jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar.
Ta gabatar da sallar azahar da la’asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur’aninta ta soma tilawa. Ko aya biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma’idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe Alkur’anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta nuna mata tulin wanke-wanke ta ce “Kina ganin aiki ya kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan cikinsu zan kwashe tuwon dare”.
Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa “Ki dinga iza min wutar nan, sallah zan yi”.
Ta ce “To”.
Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce “Cika min randar can da ruwa, ga kuma tsummokaraina ba yawa, ki dauraye min su”.
Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce “To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken, ta ce tuwo zata kwashe”.
Habiba ta ce “Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki fuska?”
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce “Au, bar min wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama mini”.
Suka soma bala’i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu.
Baffa ya shigo yana “Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota ana jiyo ku, asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na matan aure ba”.
Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce “Habiba waye zai yi miki wannan wankin?”
Ta yi shiru, ya ce “Da ke nake magana fa”.
Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce “Au… to, kana nufin haka zamu aje gansamemiyar budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a katifa?”
Ya ce “Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?”
Cikin rashin gaskiya ta ce “Bai zo ba”.
Ya ce “To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi miki, ko ki tura ‘ya’yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba. Mairo ba baiwar uwar kowa ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba. Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke Ladidi!”
Ya kwala mata kira, ta fito a razane, “Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in kwashe miki hakora yanzun nan”.
Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare.

Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al’amarinta, ya sayo mata matsananciyar kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah, daga su har ‘ya’yansu, su suyi mata, ‘ya’yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo wuka ta mutu kowa ya huta da bala’in Baffa a kanta.
Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri, sai karan hanci da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata taba ganin mutane marasa imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba.
Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan mutum ba a wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu biyayya ba iyakar iyawarta.

Wata mota kirar Kia-Rio ta yi fakin a kofar gidan Alhaji Abbas, misalin karfe goma dai-dai na safe. Lokacin Alhajin bai kai ga fita kasuwa ba. Nabilah Bebeji, ta fito daga mazaunin direba tana duba agogon hannunta, ta doshi kofar gidan Alhaji Abbas, tana mai addu’ar Allah dai Ya sa Baffan Mairo bai fita ba.
Ta yi sallama a tsakar gidan, Habiba ta amsa yayin da ta bi ta da kallon mamaki. Sanye ta ke da atamfa mai karshen tsada shudiya ta karkata dauri mai ban sha’awa kamar nadin inji, a hannunta ‘yar matsakaiciyar jaka ce, samfarin Louis Buittion da takalminta marar tudun dunduniya. In ban da kamshin turaren Rasasi (blue-royale) ba abin da ke tashi a jikinta, ta yane jikinta da gyale kalar atamfarta, daure a hannunta agogo ne shudi samfurin polo.
Jiki na rawa Habiba ta dauko sabuwar tabarma ta shimfida mata, ta tsugunna har kasa ta gaishe ta, ta gaya mata ta zo wajen Mairo ne. A lokacin Mairon tana bayi tana wanka, cikin bakin-ciki karara Habiba ta yi mata nuni da dakin su Mairo kamar ba ita ce mai yi mata fara’ar da ta ke yi mata ba.
Dakin tsaf ya ke, da yake Mairo ba ta wasa da tsaftarsa, sau dubu Ladidi zata bata, sau dubu zata gyara.
Ta samu gefen katifar Mairo ta zauna, ta dauki wani littafi na Mairon da Mairon ta aje, da alama shi ta ke karantawa kamin ta shiga wankan na Dynasties the Ashtons (Condition of marriage), ta ce “Maryama na nan da karance-karancenta”.
Dai-dai lokacin da Mairon ta shigo, kanta na yararin ruwa domin wankan sallah ta yi, zata soma sallah. Ta harari Nabilah ta ce, “karfe taran ke nan?”
Ta yi murmushi ta ce “Go-slow ya tare ni, amma ai na yi kokari, ke fa da sai yanzu kika yi wanka, ni tun asuba Momi ta tashe ni wai inyi maza in shirya in dauko mata Mairo ta ganta”.
Ta yi murmushi, ta ce “Yau dai da yardar Allah zan ga Momi”.
Ta ce “kwarai kuwa”.
Mairo na shiryawa Nabilah na kallonta cikin yin tazbihi ga Sarkin halitta da Ya kaga halittar Mairo.
“MAIRO MATAR MANYA CE”. Nabilah ta ayyana a zuciyarta. Wani irin jiki lukui-lukui kamar mai shiga wankan inji, ga kwantaccen gashi na fulanin usuli, wanda ke kwance lambam akan dogon wuyanta yala-yala da shi kamar ba zai kitsu ba, alhalin ba ta taba shafa masa relader ba koda wasa. Idanuwanta dara-dara, farare kal masu wani irin maiko da sheki (oily-eyes). Kai ita ba ta taba ganin mace mai lafiyayyen kugu da shafaffar mara irin Mairo ba. Kai ka ce idan ta sunkuya karyewa zata yi. Tana sharce kanta ta lura Nabilah kallonta ta ke, ta ce “Ke don Allah wannan kallon fa?”
Ta ce “ke din ce, abun kallon ce Mairo, duk mijin da ya aure ki ya caba, ai ban san haka kike da kyau ba sai yau”.
Ta yi murmushi ta ce “Ni kuma ban taba ganin mai kyau irin naki ba Nabilah”.
Ta ce “Kayya! Gyara ne kawai Mairo, ina maganar natural beauty ne”.
Sai Mairo ta ja bakinta ta tsuke, ba ta kara cewa komai ba.
Ta kammala shiryawa tsaf cikin atamfarta ta ganin sarki (Ghana wad), wani tausayi ya kama Nabilah, mace har mace, sai dai ba kayan ado, da da suttura ya ya za a ga Mairo? A hakan ma Mairo abin a juyo a kalla ce, ina ga ta samu sutturu da kayan gyara? Sai dai duk yadda ta so ta dinga taimakawa Mairon tun a makaranta Mairon ba ta yarda, cike ta ke da wadatar zuci, kuma cikin godiyar Allah.
Mairo ta yi wa Nabilah jagora zuwa dakin Baffa. Ta zube a kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin far’a da cewa, “Lafiya kalau Nabilah, an gama karatu sai aure ko, ko kuwa babbar makaranta za ki wuce kamar kawarki?”
Ta ce “Eh, makaranta zan wuce”.
Ya ce “To Allah Ya ba da sa’a”.
Sannan ta gaya mishi ta zo ta dauki Mairo su je gidansu, iyayenta su ganta. Ya ce “Babu damuwa, don Allah kada Mairo ta kai dare”.
Suka ce “Insha Allah”.
Cikin nutsuwa Nabilah ke tuki har suka hau kan titin sakateriyar Audu-Bako, Mairo ta dauka Tarauni suka nufa, sai ta ga Nabilah ta karya akalar motar ta sha round ta hau kan titin state library, ba ta kai karshen titin ba ta yi kwana ta shiga unguwar Ahmadu Bello Way, ta tsaya a harabar gidansu mai lamba dari da biyu (No. 102), suka rufe motar suka karasa cikin gidan.
Tun Mairo na mamakin tangama-tangaman falullukan da suke wucewa har ta daina mamaki, sai tazbihi ga Allah Mai azurta wanda ya so. Ba ta taba shiga gida irin wannan ba ko a mafarkinta. Ba su tsaya a ko’ina ba sai a babban falon Momin Nabilah, wadda ta fito tana tafa hannu tana ‘Lale da Mairon Nabilah”.
Ta yi murmushi ta zamo daga cikin kujera tana gayas da Momin, kamin ai haka tuni Nabilah da wata dattijuwa wadda da alama mai aiki ce sun cika gaban Mairo da kayan tande-tande da lashe-lashe irin wadanda ba ta taba ci ba a rayuwarta.
Shi ma Daddyn Nabilah ya sauko yana marhaban da Maryam. Ya zauna a cikin su, Mairo duk ta kasa sakewa sabida bakunta da rashin sabo. Saukin kan iyayen Nabilah ya burge ta. Ta tabbatar Nabilah ‘yar gata ce ta karshe, ita kadai ce kwallin kwal, a wurin iyayenta. Daddy ya ce da Mairo da zarar takardunsu sun fito ta kawo mishi zai taimaka su samu gurbi a jami’a ita da Nabilah, ta yi godiya sosai.
Karfe biyar na yamma Mairo ta yi haramar tafiya. Akwati guda Momi ta shake mata da kayan shafa da dogayen riguna kala-kala, Nabilah ta maidota gida.
Tana shigowa idanun Hajara da Habiba akan jakar hannunta. Jikin Habiba har rawa yake, ta bi bayan Mairo tana son ta ji ina Mairo ta samo wannan diyar arzikin, har ga shi ta dawo da galleliyar jaka cike taf da kaya.
Har karo suke ita da Hajara wajen shigowa dakin. Habiba ta ce “Bude jakar mu gani, me muka samu?”
Hajara kuma ta ce “Wannan bakauyar ta iya bude irin wannan jakar ne? Gafara nan ki gani”.
Ta jawo jakar ta soma kici-kicin budewa. Ta zazzago duk kayan da ke ciki tana al’ajabi. Habiba ta ce “Ina kika samo wannan diyar arzikin kuma?”
Mairo ba ta yi magana ba suka soma kasawa, Habiba ta daga rigar da ta fi kowacce kyau a ciki, ta ce “Wannan zata yi wa Ladidi”. Ta sake daga skirt da rigarshi ta ce, “Wannan sai a bar wa Batulu idan ta kara girma zata yi mata dai-dai, ke ki rike wannan din”.
Ta tura mata wata ‘yar yaloluwar rigar barci suka tattara kashi uku bisa hudu na kayan suka yi waje da sauri har suna tuntube tareda karo da juna kada Baffa ya jiyo su suka gudu dakinsu.
Mairo ta ce, “Allah na tuba, suttura tsumma, mene da zan damu kaina?”
Duk da Baffa ya hana a bata aikin wahala wanda ya fi karfinta ba su fasa ba a bayan idonsa. Mairo na hakuri da su da kokarin kyautata musu su da ‘ya’yansu a kullum, amma ta rasa dalilin da yasa mutanen nan suka ki jininta, ko zata wuni tana aikin bauta, shara, wanke-wanke, wanki da wankin bandaki ba zata taba yi musu gwaninta ba, balle kalmar “madallah” ko “an gode” ta gitta a tsakani.
Watanni uku cif da gama makarantar su ta samu labarin fitowar jarrabawarsu, don haka ta soma shirin zuwa gidan su Nabilah don su je makaranta su karbo sakamakonsu.
Baffa da kanshi ya kaita gidan su Nabilah tana yi masa kwatance tana nuna masa hanya har suka iso gidan. Ya sauke ta ya juya da cewa, idan sun dawo Nabilar ta maidota gida.
Amma Allah sarki, sai ta tarar da Nabilah kwance ba ta jin dadi. Ta zauna a gefen gadon da ta ke kwance ta dora hannu akan goshinta, zafi rau! Momi ta shigo da filet a hannunta mai dauke da soyayyar plaintain da dankali da kwai, ta ce “Ungo ba ta Maryam da kanki, watakila zata ci, tunda ni nayi-nayi ta ki karba”.
Mairo ta ce “Haba Nabilah, ciwo da rashin cin abinci ai abin ba kyau, ki daure ki ci ko kadan ne don Allah”.
Ta karba tana kokarin mikewa, Mairo ta tusa mata filo a bayanta don ta ji dadin jingina. Momi ta fita ta bar su. Tana fita Nabilah ta fashe da kuka mai tsanani. Hankalin Mairo ya tashi, ta ce “Lafiya Nabilah? Wani abu ya faru ne?”
Cikin kuka ta ce, “Me ye bai faru ba? Hajiyar Daddy ce ta zo ta ce ba ta yarda na ci gaba da karatu ba, aure za a yi min da wani cousin dina. Bayan kuma bana sonsa, kuma sati mai zuwa za a daura auren, shi ma bai ce yana sona ba, wai wata Igbo ya zo musu da ita daga can inda yake karatu a Kudu, shi ne ba su amince masa ba, suka ba shi ni. Allah na tuba auren soyayya ma bai tsira ba a wannan zamanin balle auren tushe? Sabida Allah na yi kama da matar tushen iyaye?”
Mairo ta rasa abin da zata ce “Ki ce ba ciwo kike ba, tunanin aure ne. Ni ban ga aibu a nan ba, tunda iyaye ne suka hada, ai ALHERI ne, kuma alherin suke nufin ki da shi. Ki yi biyayya ga iyayenki Nabila za ki ga da kyau a rayuwa.
Soyayya aikin banza ce, don watakila yadda kike son mutum shi ba haka ba ne a zuciyarshi ba. Na gani akan kaina Nabilah. Har yanzu kuma ban ga inda soyayya ta kaini ba, sai kunci a zuci, ruhi da gangar jiki. Nabilah yau zan gaya miki abin da ke raina shekara da shekaru. Wato soyayyar Uncle Junaidu. Na dauka yadda na ke azabtuwa a zuci, da gangar jiki da soyayyarsa, shi ma haka yake sona, ashe ni ban sani ba, Uncle ba haka ba ne a zuciyarshi ba.
A ranar da na yanke shawarar fallasa mishi asirin zuciyata, a ranar ya zame, ya gudu ya barni, ba tare da ya sanar da ni komi a kanshi ba. Wanda ke nufin ba ya bukatar anymore mu’amala da ni. Har yau ni kadai nasan abin da nake ji a zuciyata Nabilah. Hasashenku ke da Innata, bai zamo gaskiya ba, Uncle Junaidu ba SO NA yake yi ba, tausayina ne da taimako”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button