ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Baffa ya ce “Amma Habibu na yi mamaki da ka iya yin wadannan shekarun ba ka waiwayi gida ba, ko gaisuwa ce ai ka aiko mana, idan ba ka zo ba (a lokacin ba kowa ke da wayar hannu ba, sai wane da wane)”.
Habibu ya ce “Kuskuren da na yi ke nan, amma kusan kullum ba a rasa masu zuwa Najeriya daga Malaysia. To sai dai ita kanta Maleshiyar na dade da barinta, tun bayan da na kammala karatun digirina na farko.
Dina abokiyar karatuna ce, diyar Ambassadan Nijeriya a kasar Maleshiya. Mun dade muna soyayya, mahaifinta ya so mu dawo gida ayi auren gaban iyayena, na nuna masa ni ba yanzu zan koma gida ba, ina da babban uzurin da ya rabo ni da gida, idan na koma mawuyaci ne Babana ya barni na dawo. Don haka ya tsaya tsayin daka har muka yi aure.
Da taimakon mahaifinta na samu aiki na wucin gadi (temporary) ina yi a wani kamfanin kera takalman fata. Na dade ina aiki a nan kuma na samu alheri yadda ba kwa zato. Daga baya wani abokina Amiru da taimakon mahaifinsa ya yi min hanyar da na samu gurbin karo karatu a Michigan din Amurka, akan kwamfuta da duk abin da ya shafe ta. Ina gamawa ba da jimawa ba na samu aiki a Bankin Barclays reshen kasar Amurka, don haka muka koma can. A can aka haifi Alhaji da Mairo, Muhd ne kadai aka haifa a Kuala-Lampur (Malaysia). To kun ji, don haka bazan dade ba, don wajen aikina suna bukatana, ina so zan tafi da Mairo”.

Mairo ta yi azamar dago kai ta dube shi, da gaske ya ke ko wasa ya ke? Babu alamun wasa ko kankani a fuskar Habibun. Shi kuma ya kafa mata ido cike da tsoron, kada ta ce ba zata zauna da shi ba. Shi kam nan duniya bai ga abin da zai sake raba shi da ‘yar uwarshi ba, wadda ta rage mishi kwal a duniya. Baffa ya ce, “Anya a yi haka? Ni dai na fi so inyi mata aure, hankalina zai fi kwanciya. In lissafina dai-dai ne shekarunta goma sha takwas cif, aure shi ne ya dace da ita”.
Cikin murmushi Habibu ya ce “Ta fitar da mijin ne?” Ya fadi yana kallon Mairon, ta yi hamzarin sunkuyar da kanta. Baffa ya ce, “A’ah, ita ko zancen nan da samari irin na su Ladidi ba ta yi, idan ka ganta ta fita, to muhimmin abu ne ya fitar da ita. Amma akwai wani abokina Alh. Salisu da ya yi min maganarta tun wancan watan na ce ya dakace ni sai na yi shawara da ita tukunna”.
Habibu ya ce “Har nawa Mairon ta ke? Ka yi hakuri Baffa ka ba ni ita makaranta zan sa ta, idan ta soma ko ba ta kare ba idan mijin ya fito sai a yi auren, amma Alh. Salisu ai ya yi mata tsufa”.
Baffa ya ce “Ni ma abin da na yi la’akari dashi kenan, shi yasa ban baiwa zancen wani muhimmanci ba, sai ka yi mata fasfo ku tafi, Allah Ya sa hakan shi ne alkhairinta”.
Habibu ya ce “Amin”. Ya dubi Mairo ya ga ta sunkuyar da kai, ba ta dago ba ya ce “Mairo ko ba kya son zama da ni da ‘ya’yanki?”
Ta yi murmushi ta ce “Mamarsu zata yarda?”
Shi ma ya tayata murmushin, ya ce “Kada ki damu. Dina mace ce mai fahimta, ga kirki da hankali. Na yi mata kyakkyawar shaida. Ta sanki, ta san labarinki ba tun yau ba. Ta fi ni damuwa da a dauko ki, ina gaya mata akwai lokacin da nake jiran isowarsa ga shi Allah Ya kawo”.
Baffa ya ce “Ita tana ina?”
Ya ce “Tana garin Dutsinma, can home town dinsu, gobe insha Allah zan je na dauko ta”.
Rahma diyar Hajara ta shigo da kular abinci da farantai ta aje ta fita, Mairo ta matso ta zubawa Habibu, ya karba yana cewa, “Yaushe rabona da cin dan wake?”
Baffa ya yi dariya ya ce “Ai ga Mairo nan sai ta dinga yi maka dan wake, idan matarka ba ta iya ba”.
Ya ce, “Tana yi min na fulawa (gudun kurna), amma ba irin shi nake so ba, wannan da ake yi da rogo da kuka shi na fi so, don ya fi sulbi, yafi saukin wucewa a makogaro”.
Mairo ta zuba filet daya da yaran ta ja su suna ci, Baffa na bai wa Habibu labarin bayan rabo. Habibu ya kammala ya ajiye farantin, ya tsiyayi ruwa a jug ya sha, ya ce “Na zo da ma’aikata Baffa, gobe insha Allahu za a rushe gidannan a yi ginin zamani yadda su Inna Habiba da sauran yara za su fi sakewa”.
Baffa ya yi murmushi ya ce “Allah Ya ba da iko Habibu”.
Ya juya ga Mairo ya ce “Je ki share min dakina na zaure, anan zan sauka zuwa gobe, yaran ki kwana da su, ni zan shiga cikin gari wajen tsoffin aminai, gobe idan Allah Ya kaimu sai mu je can immigration maganar fasfo”.
Ta ce “Ita kuma Anti Dinan a ina zata sauka idan ta zo?”
Ya ce “Tana da inda ya fi nan ne? Duk nan zamu sauka”.
Ta tasa yaran a gaba suka nufi cikin gida. Habiba da Hajara dai duk kunyar Habibu ta ishe su, sakamakon rashin arzikin da suka san suna yi wa Mairo. Ba su taba zaton Habibu zai dawo ba, ga wata irin galleliyar mota da ya iso da ita mai nuni da lallai Habibu ya kama kasa, ga ‘ya’ya firda-firda kamar ‘ya’yan kajin gidan gona, da gani babu tambaya iyayensu sun gama samun nasibin rayuwa.

Habiba ta karbi ‘yar daga hannun Mairo, ta sa zani ta goyata, ta ce da Mairo “Ladidi har yanzu shiru, ina kika barota ne?”
Ta ce “Tana can asibitin ta ce zata dan jima”.
Baffa ya fita ya dawo da gyararrun kaji guda goma, ya ce a yi wa Habibu girki. Mairo ta je ta share dakin Habibun da ke soro, ta kunna turaren wuta ta gyare ko’ina. Ta shigar da kayan Habibun, bayan ta ware kayan yaran. Daga Hajara har Habiba sun shiga hankalinsu musamman ganin yadda ake sauke buhunhunan shinkafa, katon-katon na taliya, garewanin mai, katon na juices, na gwangwani da na kwali, buhunan sugar, doya, dankali da sauransu, duk aka jibge musu a store.
Ladidi ba ta dawo gidan ba sai dare, wujiga-wujiga da ita, ba wanda ya ga shigowarta sai Mairo don duk sun yi barci, ta lallaba ta kwanta a katifarta, ga dukkan alamu ta je an cire mata cikin. Ladidi sai ta daina bai wa Mairo mamaki, ta koma ba ta tsoro.
Washegari ta shirya ta yi wa yaran wanka ta shirya su, Hajara ta ba su abin kari koko ne da kosai da agada, da suka kammala suka tadda Habibu a dakin Baffa suna kalaci shi da Baffan. Yaran suka nufi Babansu suka baibaye shi, ya ce “Ba ku gaida Baffa ba Muhammad”.
Suka hada baki suka ce, “Baffa ina wuni?”
Ya ce “Ina kwana dai takwara na, kamar ba haihuwar Turai ba, Hausa ras a bakinku”.
Habibu ya ce “Ai ni bana yi musu Turanci, Mamarsu ce ta ke musu. Ita ma ina hanata don kowa yabar gida gida ya barshi”.
Baffa ya ce “Wannan haka ya ke, Allah Ya raya mana su cikin addinin islam, amin”.
Suka bar yaran wurin Habiba, suka nufi Immigration office, can hanyar farm center cikin dan lokaci aka yi wa Mairo passport aka ce su dawo bayan kwana uku su karba.
A hanyarsu ta dawowa Habibu yana tuki cikin nutsuwa Mairo tasa ido tana kallon shi yana burge ta, ya yi kyau ya yi girma, ya zama ingarman cikakken mutum ma’abocin kwarjini na musamman da cikar zati. Ta fadi a ranta gaskiya wannan Dina ta caba miji. A ranta kuma tana kissima shin ita kuma Dinar yaya zata kasance? Jikinshi ya ba shi Mairo kallonshi ta ke, ya yi wani irin murmushi mai ban sha’awa har fararen hakoranshi suka fito. Ya dan juyo ya ce
“Ya ya dai Mairo? Irin wannan kallo haka? Ko na yi kama da saurayinki ne?”
Kunya ta kama Mairo, ta rufe fuska tana dariya, “Ni ba ni da wani saurayi. Ka yi kyau ne da yawa Yaya Habibu, ka zama babban mutum mai ban mamaki, don Allah mai Anti Dinar nan take ba ka ne?”
Ya yi murmushi ya kai hannun hagunshi ya shafi kwantacciyar sumar kanshi, ya ce “Soyayya ta ke ba ni Mairo. Duk wata kauna ta duniya Dina ta ba ni tun a lokacin da nake dalibi, ba ni da komai, ba ni da ko kwabon da zan aure ta, a matsayina na dan kauye da matsayinta na diyar Ambassador. Habibun kawai ta ke so ba wai wani abu da Habibun ya mallaka ba”. Mairo ta ce cikin zuciyarta, “Kamar ni da Uncle Junaidu”. Ba tasan cewa furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba
7/31/21, 8:31 PM – Kawata: 990
Ya rage gudun motar ya dube ta sosai, hawaye ne fal idanunta “Kika ce mun ba ki da saurayi, Mairo”. Ta kai ‘yan yatsu ta share hawayen idanunta “Kuka Mairo? Mairo me ya sanya ki kuka?”
Ba amsa, karewa ma, sai ta soma shesshekar kukan sosai.
Ya sauka gefen titi ya kashe motar. Ya mika hannu ya kama hannunta, ya damke cikin nasa “Daga yau ba zaki sake kuka ba Mairo, tunda ga ni. Babu abinda Allah bai mallaka min ba. Gida a America, gida a Abuja, motocin hawa sai wadda ranki yake so. Ga babban aiki da BARCLAYS BANKS, ga takardun ilmi har zuwa PhD, wanda nake da yakinin daga mu har jikokinmu da ‘ya’yan jikokinmu babu mu babu talauci.
Jami’a sai wadda kika zaba cikin kasar America. Gaya min wane ne Junaidu? Ni kuwa in aura miki shi ko shi ne beran masallaci sabida talauci, ko shi ne Bill Gates sabida arziki, amma fa sai idan yana da ilmi, ya kuma yi alkawarin zai rike min ke da amana”.
Mairo ta sunkuyar da kai, ta ce “Ai bai taba cewa yana sona ba!”.
Habibu ya ce “Ke ce kike sonshi ke nan?”
Ta ce “Ni ma ban sani ba ko son nasa nake yi. Alherinsa da kyautayinsa masu yawa ne a gare ni. Ya tsaya tsayin daka akan karatuna, ya tsaya tsayin daka akan lafiyar Baba da Inna, ya ce nima cikakkar mutum ce a lokacin da nake jin kaina cikin inferiority compled. Don haka bazan iya ce maka Uncle Junaidu saurayina ba ne, sai dai duk duniya babu wanda nake jin zan iya aure sai shi…….”
Ta shiga baiwa Habibu labarin tun bayan tafiyarsa, yadda akai ta je FGGC, haduwarta da Junaid, Kausar da su Nabilah, saran da maciji ya yi mata, ba da jininsa da ya yi gare ta, karfafa mata gwiwa da kwarin gwiwar da yake ba ta a karatunta, amanar da Malam Bedi ya ba shi a kanta, tsayawa da ya yi akan lafiyar iyayensu, har zuwa gama makaranta da nemansa da ta yi ranar candy ba ta ganshi ba. Ta kare labarinta da ba shi labarin zuwansu karbo sakamakonsu a makarantar inda aka gaya musu ya tafi karo karatu Russia. Ta dakata ta share hawaye, ta cigaba da ba shi labarin zuwanta gidansu wajen mahaifiyarsa, amma ba ta gaya mata ko ita wace ce ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button