ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk a kokarinsa na son farantawa ‘yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina, ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba.
Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu.
Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba ta damu ba, ta ci gaba da ayyukan gabanta.
Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma an sanar da ita wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta samu Habib ba.
Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba ta shiga. Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba.
A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da labarin Habibu? Sun kasa samunshi a waya.

Baffa ya yi gyaran murya ya ce
“Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja wajenshi ban san halin da suke ciki ba”.
Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya kasance ciwon Amirun yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al’amuran rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban ikon Allah.
Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba.

Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce
“Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi”.
Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce “Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai ko? Tun ranar da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba”.
Dina ta shirga karya
“Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba”.
Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo ta wutsiyar idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu’azzam Kanti, ke kwararowa. (Alkawari bayan rai). Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta, da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani bakon al’amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba zata ce mene ne ko na mene ne ba.

Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta yaye labulen dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature yin harkokin gabansa ba.
Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma duk lullube suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani wajen rage azabtaccen sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba.
Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat da bakin wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk bakake wul. Sakonnin suka soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da sabbin sakonni guda goma sha biyar.
Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta kasa samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh inda ita kuma ta ke sanar da ita cewa akwai test’ karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin. Sai na wani dan ajinsu Henry baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta ba.
Ta yi mishi ta’aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta, kasancewar an yi shi ne cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin rubutun a gurguje.

“Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu kansu cikin gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a banza.
Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci ko matsatsi na rayuwa ba”.
-mai son ki.

Ta karanta ya fi cikin ‘ya’yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba. Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da zuciyarta ba.

To haka washegari, mai ‘logo’ na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.

“…….. Some one misses you!”.

Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu, wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.

Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce “Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?”
Ta yi ajiyar zuciya ta ce “Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina a tashe ya ke”.
Ya ce “Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don’t want to lose AMEERU. (bana so in rasa Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo”.
Dina ta kidime “Lafiya? Me ya faru da Amirun?”
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce.
8/3/21, 9:03 PM – Kawata: B
Cikin dauriya ta ce “Habib, me ya faru da shi? Ka gayamin don Allah. Sai dai na taho ni kadai, Mairo jarrabawa zata fara zanawa, wadda idan ba ta yi ba, sai ta maimaita shekarar”.
Da budaddiyar murya ya ce.
“Karatun ma, ai ina jin ta barshi kenan. AURE zan yi mata”.

Dina ta kyafkyafta ‘yan idanunta ta sato kallon Mairo, cike da fargabar Allah Ya sa ba ta jiyo abin da Yayanta ya ce ba. Ta ga hankalinta ba ya kanta, ya tafi ga lallashin Little Mairo ta ci abincin da ta ke ba ta da dan kankanin cokali. Ta godewa Allah da abin da ya darsu a ranta (mutuwar Amiru) ba shi ne ba. Ta kawo gwauron numfashi ta ce “Kano za mu taho ko Abuja?”
Ya ce
“Ku biyo jirgin Abuja, idan kun sauka ki kirani zan zo na dauke ku”.

Don haka a daren yau bakidayansa Dina ba ta samu isasshen barci ba. Tausayin Mairo ya cika mata zuciya. Irin yadda ta ke wahala akan karatun nan, ta kwallafa rai a kansa, kullum cikin ‘solving assignments’ ace ya tashi a banza! Shekaru biyu cur! Sai dai kwarin gwiwar da ta ke da shi, shi ne Habibu ba zai kai ‘yar uwarsa inda za ta tozarta ko ta wulakanta ba. Duk son da ta ke yi mata ta tabbata bai yi rabin-rabin wanda shi yake yi mata ba. Sannan akan Amiru ba abinda bazai iya ba.
Da safe karfe takwas ta yi shirin fita don yi musu booking din tickets na jirgin ‘Lufthansa’ wanda zai tashi karfe goma na daren ranar. Sannan ta dawo, ta cimma Mairo ta fito daga wanka tana shafa akan stool ta ce (tana mai kawas da kai) “ki hada kayanki masu dan yawa, gida Najeriya zamu tafi, ban san kuma ranar da zamu dawo ba”.
Tana mai kawas da idanunta daga gare ta, don ba zata iya fada mata abin da Habibun ya gaya mata ba.
Cikin mamaki Mairo ta ce
“Me ya faru? Irin wannan tafiya haka unexpected?”
Dina ta ce
“Bai fada min ba, amma dai ya ce lallai mu tafi”.
Kamar ta yi kuka, ta ce “Ina da ‘test’ yau, kuma jibi za mu fara jarrabawa, kuma Yaya Habibu ya sani, yaya yake so in yi?”
Dina ta ce
“Hakuri za ki yi, haka Allah Ya shirya miki. Wani hanin ga Allah baiwa ne”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button