ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

A yau zai maida ita gida, domin jirgin karfe hudu na yamma zai bi zuwa gida Najeriya. Tunanin Mairo na yadda za ta fuskanci Dina ne da Yaya Habibu idan ya dawo ya ji ta bi miji, kwana da kwanaki ba a gansu ba.
Har kuka ta yi saboda damuwa, don ta lura shi ko a kwalar rigarshi. Ba karamin tausayi da dariya Mairon ta ba shi ba. Don haka ya shiga lallashinta, yana nuna mata wannan ba wani abu ne na tada hankali ba.
“Shi Yaya Habibu da Dinar ba daki daya suke kwana a gabanki ba? Su ba su ji kunyarki ba, sai ke ce mai jin kunyarsu akan haka?”
Ta balla mishi harara cikin hawaye. Ya tarairayota ya rungume yana dariya, ya ce.
“Shikenan ki barni da su, ni zan fitar da ke”.
****
Lokacin da suka iso gidan Habibu da Dinan ne suke ‘lunch’ tare da su Muhammad. Cikin bagararwa Yaya Habibu ya saci kallon Mairon da ke bin bango tana son ta shige dakinta, ya ce.
“Ai na dauka kun wuce gida Najeriya ne?”
Amiru ya yi dan murmushi, sannan ya ce.
“Idan mun wuce ina ruwanka? Ni bana son aikin sa ido wallahi”.
Dina ta yi murmushi tana jinsu suna ta yi, Amirun na cewa.
“Sa ido sana’ar banza, Yayan banza, Yayan kwabo”.
Habibu ya dube shi, ya ce.
“Na ji dai, tunda ni dai mace ba ta taba kwantar da ni a gadon asibiti ba”.
To a nan ya kashe bakinsa, don bai kuma tankawa ba.


C
ike da himma Mairo ta dasa karatunta daga sabuwar shekara, duk da su Ir’eesh sun wuceta, ya kasance ta koma farkon shekara ta biyu.
Habibu ya ba ta wayarta, bayan wadanda Amirun ya mallaka mata guda biyu irin wadanda ba ta taba gani ba. Don haka duk dare suna makale a waya suna fadawa juna how much they miss each other.
Yadda ba ta iya sakewa su yi hira fuska da fuska, a waya idan ka ji su, sai ka sha mamaki. Kullum tambayarshi shi ne, har yau babu ajiyarshi ne?
Da ya fadi hakan zata yi sauri ta kashe wayar, sabida kunya.
To haka rayuwarsu ke tafiya, cikin so da kauna, ba sa taba gundurar juna. A Najeriya ne ko a Michigan, har Mairo ta kare karatunta, ta fiddo kwalin first class degree a B.Sc Sociology.

Har zuwa wannan lokacin shiru, babu haihuwa babu alamarta, don ko batan wata Mairo ba ta taba yi ba. Tun abun na damunsu har suka hakura suka fauwalawa Allah.

Sai dai kuma kamar yadda kowanne dan Adam ba ya rasa makiya, to hakan ce ta faru da Mairo daga dangin Amiru, musamman a Gaya da suka fara kishin-kishin Amiru ya auro musu juya, don ma Hajiya tana tsawatarwa ne amma har su Sabah sun soma sauya mata fuska.
Aka soma yi wa Amirun tushen ‘yammata, ‘ya’yan gata, kyawawa wadanda suke ganin zasu iya gogawa da Mairon da duk abin da ta ke takama.
Zuwa lokacin shi ma Habibu ya yi ‘retire’ daga ‘barclays’, haka Dina ta bar kotun da ta ke aiki. Sun tattaro da ‘ya’yansu duka sun dawo gida Najeriya garin Abuja, cikin unguwar colorado close.
Don haka Mairo cikin farin ciki ta ke, ga ta ga iyayenta, wadanda su ne kadai ta ke gani ta ji dadi, kasancewar Hajiyar ma ta soma daukar hudubar ‘ya’yanta da ‘yan uwan mijinta na Amiru ya kara aure.
Daddy bai san abin da ke faruwa ba na matsalolin da Mairo ta soma fuskanta cikin gidan ba. A lokacin tana hidimar kasa a nan jami’ar Abuja, ta kai ga ko ta gaida Hajiya a ciki ta ke amsawa don gani ta ke Mairon ta mallake mata da, yadda har ba ya damuwa da samun dan kansa.
(Matsalarmu ke nan al’ummar Hausa, babu ta yadda za a yi a ga mace na zaune lafiya da mijinta yana sonta, yana gudun bacin ranta, sai a ce ta mallake shi.
An fi so a ji kullum yana kawo kararta ana yi musu sasancin sulhu, ko ya dinga aura yana saki, ko ya dinga aibatata cikin yan uwansa, Allah Ya sa mu gane mu gyara zuciyoyinmu, amin).

A yau ne Amiru ya shirya musu ‘wedding anniversary’ na cikarsu shekaru biyar da aure. Taro ne da ya tara manya-manyan ma’aikatan bankunan Najeriya, bankunan kasar America, irin su World Bank, Barclays, Bank of America, Comerica, Citigroup, HSBC, Chase… da sauransu. Abokansu na karatu ne da yawa da suka watsu a wadannan bankuna suka gaggayyato. Taron wanda aka gabatar da shi a wani conference hall na ‘hotel’ din ‘Nicon Noga’ ya yi matukar yin armashi, kowane bako da maidakinsa, wato by couple’.
Mairo da Amiru sun samu kyaututtuka na ban mamaki daga ‘yan uwa da abokan arzikinsu. Kudi wannan tsurarsu da Mairo ta samu sun tasarwa lissafi mai girma, ba’a maganar sauran kadarori irinsu gidaje, hannun jari da sauransu.
Daddy kadai abin da ya bayar ya girgiza kowa, wai! Ina wuta a jefa marainiyar Allah Mairo a wajen kannen Amiru, dangin Hajiya da dangin Daddy da suka zo daga Gaya.

Sun sha alwashin idan Habibu a tafe yake yana tsaface musu Da ta yadda har ba ya jin shawarar kowa sai tashi, baya ganin owa nasa da gashi sai shi, to su a can suka kwan, kuma acan suka wuni.
Gadararsu shi ne Amiru shi ne silar arzikinshi, wannan bai ishe shi ba, sai da ya kakaba mishi kanwarshi da a yanzu ta zame musu alakakai, karfen kafa.
Don haka sun sha alwashin sai Amiru ya yi auran dangi, kuma sai sun raba shi da Habibun koda za su yi yawo tsirara ne.

A wannan dan tsukin Mairo ba ta samun zama, sabida shirye-shiryen fara karatunta a ‘Wayne State University’ da ke Michigan. Komawa karatun da ya janyo mata kace-nace da dama har ta gwammace dama ba ta tarki zancen ba.
Domin Hajiya ta kira Amiru kai tsaye ta fada mishi cewa ba ta yarda ba. Idan ba zata yi karatun a nan ba, to ta bar shi, amma sun daina daukar wannan rainin hankalin na Habibu da mace tana gidan aure zata tsallake ta tafi wata uwa duniya wai karatu.
Amiru ya sha mamaki kwarai, don bai taba ganin ranar da wani sabani ya gitta tsakanin Hajiya da Mairo ba. Biyayya ta ke mata tamkar ta yi mata sujjada. Hajiyar da ke fada da shi idan ya batawa Mairo rai, amma yau ita ce ta ke mishi magana kamar ba ta taba sanin Mairon ba. Bai san ba abin da ‘zuga’ da ‘karfar baka’ ba sa jawowa ba. Cikin nutsuwa ya soma yi mata bayani cewa.
“Hajiya babu hannun Habibu a cikin wannan lamari. Idan ma da wanda yake da ruwa a ciki to ni ne. Don ni na amince mata, Mairo tana karatunta na aure ta, wanda hakan har ya janyo mata asarar shekara guda, kuma Hajiya wanda ya saba karatu a waje ba zai iya karatu cikin gurbatattun jami’o’inmu ba. Da wannan dalilin da kuma wasu da yawa ya sa…..”
“Kai! Rufe min baki!! Shirmen banza shirmen wofi, sallamamme , bawan mace. Da dai ba a san asalin balbelar ba ne zata zo ta ce da mu daga Makkah ta zo, kuma kowa ya samu rana ai sai ya yi shanya inda yake so.
Don haka ka tashi ka ba ni waje, maganar karatu na soketa. ‘Ya’yan Abdurrahman Gaya ma a nan suke karatun, bare wata ‘yar karkarar da ko kwalta babu.
Allah dai Ya isa tsakanina da Habibu, tunda ya mayar min da da sammatacce. Ya kanainaye dukiyarka, kanwarshi ta kanainaye zuciyarka ta tsiyata ka, don ba na jin abin da ta samu din nan kai ka samu rabin-rabinsa. Sabida haka wannan hadin gwiwar da aka yi aka bude Habib Bank raba shi za a yi, wallahi ba zan yarda ba. Ku biyu ke da banki, amma sunasa ne shikadai keda bankin. Sabida kai wawa ne. Don haka na ba ka kwanaki bakwai ka kawo min takardun komi mai nuna ka raba dukiyarka da ta Habibu, idan ba haka ba, wallahi TSINE MAKA ZAN YI!!!”
Haka ya taso ya fito ko gabanshi ba ya gani. ya yi taga-taga zai fadi, ya yi saurin dafa bango. Kanshi ya kulle tamau, kwakwalwarshi ta daina aiki. Bai san yaushe Hajiya ta koma haka ba, bai san laifin da Habibu da Mairo suka yi mata haka da zafi ba. Bai san me zai cewa Habibu ba.
Ya yi tunanin ko ya samu Daddy ya fada mishi ya ba ta hakuri, kuma ya yi tunanin kada haka ya janyo ya kara laifi a wajenta.
Don haka a kwanakin da suka biyo baya duka Mairo ta kasa gane kan Amirun nata. Kullum yana kwance a daki yana tunanin ta inda zai bullowa al’amarin ba tare da ya batawa kowannensu ba.
Don ta Mairo mai sauki ce, yasan ba ta musu da shi, idan ya ce bai yarda ta koma Michigan ba yasan ba zata nuna bacin rai ba, zata bi umarninshi.
Amma Habibu fa, me zai ce mishi? Mutumin da ke dawainiya da dukiyarshi dare da rana tana kara bunkasa tana kara habaka shi yana kwance a gida, sai ya ga dama ne zai dan tabuka wani abu. Ba ya son sunan Hajiya ya fito ko kadan cikin lamarin kada mutuncinta ya zube a idanun Habibun.
To wannan tunanin su ne suka hadu suka haifar mishi da ciwon kai mai tsanani, wanda ya kai shi har tsayin kwanaki biyar da yin maganarsu da Hajiya amma ya kasa yin wani yunkuri. Ga shi yau saura kwana biyu kwanakin da ta deba mishi su kare.
Mairo ta shigo cikin shirin barci dauke da dan karamin faranti a hannunta. Ta zauna a gefen gadon ta dauko kanshi ta dora a cinyoyinta, bayan ta ajiye farantin da ke hannunta bisa durowar jikin gadonsu. Ta daura kanta akan nashi tana jin yadda ya yi zafi rau. Cike da tausayawa ta ce.
“Don Allah A.A (kamar yadda ta ke kiransa idan ta so nishadi, wato Amiru Abdurrahman) ka daure mu je asibiti tunda ka ki yarda na kira Dr. Fred, ya kake so na yi? Jin ciwon kan nan nake kamar a cikin jikina, sannan ka ce ba zaka hadiyi magani ba? So kake nima ciwon ya kamani sabida damuwa?”
Sai ta sa kuka sosai, ta tura kai cikin kirjinshi. Ya mika hannu yana shafar gadon bayanta a hankali. Amma bai ce komi ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi ke ciki. Kukanta na tsuma mishi zuciya, yana kara gigita shi.
“Ya isa Mairo, ya isa don Allah, ba ni maganin na ji zan sha”.
Ta dago da idanunta jage-jage da hawaye tana kallonshi, kwanaki biyar kacal, duk ya rafke, ya rame, ga wata kasumba mara tsari ta fara bayyana, kamar ba Amiru mugun dan kwsalisar nan ba.
Ta mike zuwa lokar jikin mudubi, ta dauko kwayoyin paracetamol ta ciri biyu ta hada da gorar ruwan ‘swan’ mara sanyi ta ba shi. Da kyar ya ke hadiya yana bata fuska don shi sau dubu gara a yi mishi allura goma da dai ya hadiyi kwayar magani.
Ya tura yatsunshi cikin sumar kanshi yana cudawa a hankali. Mairo ta gane kwarai, akwai muhimmin abin da ke damun Amirun nata. Wanda zurfin cikinshi ba zai bari ya bayyana ba. Sai ita ma ba ta takura da lallai sai ta ji ba. Yinin yau ma ya kare baki daya ba tare da ya hassala komi ba.
Ya rage gobe ne wa’adin da Hajiya ta dibar mishi zai cika, suna kwance kankame da juna kamar masu jin tsoron kada wani abu ya gitta a tsakaninsu. Ya yi gyaran murya ya ce, “Maryam”.
(Sunan da bai taba kiranta da shi ba).
Ba ta amsa mishi ba, illa ta kalli kwayar idanunshi ta cikin dan hasken fitilar barci (dim light). Ya sake kiranta a karo na biyu, ya ce.
“Alfarmarki nake nema Mairo, za ki yi mini?”
Ta ce
“Babu alfarma tsakanina da kai, sai biyayya da bin umarni. Don haka fadi abin da kake so, ni kuma ji da bi shi ne nawa”.
Ya kara lullube ta da katafaren kirjinshi, ya sarke ‘yan yatsunsu cikin na juna, ya ce.
“Maganar komawarki karatu Michigan, na ke so ki bari, ki yi hakuri, ki yi a nan Gwagwalada ya fiye min kwanciyar hankali”.
Ta ce
“Idan don wannan ne ai babu komai. Sai dai na fi son na yi karatu a jami’a mai nagarta da tsohon tarihi, kamar Ahmadu Bello ko jami’ar Bayero”.
“Duka ki hakura, ki barsu, tunda kika ji na ce ‘alfarma’ to alfarmar nake nema da gaske. Kin san haka kawai bazan sa ki yin abin da ranki bai so ba, don haka ki yi min uzuri”.
“Na yi maka A.A, Allah Ya ba ka lafiya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button