ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna isa Airport din Malam Aminu, suka tarar da Habibu ya riga su isowa, ya kwashe su zuwa Yakasai gidan Baffa.
Daidai lokacin da Mairo ta yowa Uncle Junaid rakiya zai tafi, tana dauke da Amir yana dauke da Habib. A kuma daidai lokacin da Habibu ya sanyo hancin motarsa wadda ke dauke da su Daddy harabar gidan. Daga Habibu, Daddy, Hajiya da Amina babu wanda zuciyarshi ba ta buga ba da ganin Mairo da wannan sankacecen mutum, ma’abocin zati da kamala, da kwarjini bayananne daga sarkin halitta.
Karo na farko da Uncle Junaid ya dora idonshi a kan Yaya Habibu da baya bukatar a gabatar mishi, sakamakon tangamemen hotonsa dake sitting room din Baffa.
Shima Habibu a take ya gane wannan shi ne JUNAIDUN MAIRO, da Baffa ya kyankyasa mishi a waya, cewa ya dawo neman auren Mairo.
Jikin Habib a sanyaye ya fito daga motar, gwiwoyinshi kamar an rarrade su da murfin kwano. Suka yi hannu da Uncle ya yin da Uncle ya kai gwiwoyinshi kasa yana gaida Alh. Abdurrahaman. Amina ta mika hannu ta karbi Amir a hannunshi suka hada ido da Junaidun. A take ya ga fuskar Amir da Habib a fuskarta, ita kuma ta ji wani ‘magnet’ na jan zuciyarta a kan wannan mutum da ba ta sani ba, ba ta taba gani ba. Ya dago suka hada ido ta yi saurin sunkuyar da kanta.
Mairo na son gabatar da Yaya Habibu ga Uncle amma kunyar su Daddy ta hana ta. Ya shiga mota ya tafi su Amir na ta kuka sai sun bishi. Hajiya ta kama hannun Mairo, Amina kuwa rungume ta tayi tana hawaye, a haka suka shiga dakin Habiba. Shi kuma Habibu da Daddy suka wuce falon bakin Baffa.
Cikin dan lokaci Habiba da Hajara sun baibaye su Hajiya da cima ta girmamawa da ruwa da lemu, sun zauna ana ta gaggaisawa. Mairo da Amina dakin Hajara suka wuce suka bar Hajiya da su Habiba. A nan ne Amina take labartawa Mairo rasuwar Ghali (mijinta) watanni biyar da suka gabata. Ba tare da Allah ya basu haihuwa ba.
Mairo har da hawaye na tausayawa Amina, don ita kanta shaida ce a kan matsananciyar soyayyar da suke yiwa juna. Mairo na so ta tambaye ta AMEERU ba ta so ta bada kanta. Amiru ya yi mata miki mai girma a zuciyarta. Tunda suka rabu bai taba nema ko sau daya ya ganta ba, sai ‘ya’yansa. To akan me ita zata nemeshi?
Ta tabbata duk inda yake yanzu ya dade da shafe ta a babin rayuwarsa. Watakila ma ya kara aure bayan Hanan, ya sallamawa wata wannan gangar jikin da ada ta dauka mallakinta ne ita kadai. Don ta san Dan Abdurrahaman Gaya, ba zai iya kaiwa tsawon wannan lokacin ba tare da aure ba, in ta yi la’kari da halittarsa, na mutum mai tsananin yawan bukata. Sannan Hanan, bata da surar irin matar da yake son aure. Ko kuma watakila ya komawa banasariyar matarshi? Allah masani.

Amina ta ce
“Rayuwa tafe take tare da destiny (kaddara) kala-kala Aunty Mairo, kin manta da brother, kin bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki, kin kara kyau, kin kara kiba, kin kara haiba da kamala. Sabanin shi da a kullum yake kara lalacewa.
Cikin shekaru ukun nan ban kara ganin dariyar Yaya Amiru ba, ki yafewa mai kaunarki wanda ya sadaukar da zuciyarsa ga soyayyarki. Ku tallafi juna, ku baiwa zuciyoyinku abin da suke so.
Hajiyata da ‘yan uwana sun yi kuskure, sun kuma gane kuskuren su, sun yi nadama mai suna nadama amma ku, (keda Amiru), Daddy da Habibu har yau kun ki karbar tuban su, ban san me yasa ba”.
Mairo ta yi murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce,
“Mun karbi tubansu man? Watakila dai iyakar zaman ke nan, babu saura, tunda aka kawo wannan lokacin. Shi ya gaya miki yana son komen? Yana da mace irin Hanan a gefe?”
Mamaki ya kama Amina, ta tabbata Mairo ba ta san tare suka yi waje ita da Hanan ba. Ta ce,
“A kan sakin Hanan aka yi naki, Allah sarki brother! Zurfin cikin shi na bani mamaki. A halin yanzu Hanan tana Porthercourt ‘ya’yanta biyu tare da mijinta Ramadan wani ma’aikacin kwastom”.

Mairo ta yi shiru, kamar an zuke jinin jikinta. Tausayin Amiru ya kama ta, Allah kadai ya san halin da rayuwarshi ke ciki.
Ta tura hannu cikin jakarta ta zaro wasu kananun katina da aka yiwa rubutu da kumfar golden, ta dorawa Amina a cinya.

A kasalance Amina ta dauka, kati ne na gayyatar daurin auren PROF. JUNAID ATIKU GALADANCHI da DR. MARYAM MOHAMMAD BEDI, wanda za a gabatar kwanaki goma sha hudu masu zuwa. Ba ta kai karshen karanta katin bikin ba Amina ta rushe da kuka.
Ashe masu kukan suna da yawa, domin a can falon Baffa ma Hajiya ce ke ta kuka tana rokon Alh. Abbas ya yi wa Amiru uziri, su ne da laifi ba shi ba. Su kuma ba su yi hakan da nufin A BARI YA HUCE…… ba, sai don a bawa Mairo dama ta sarara ta cika burin neman iliminta. Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali

Daddy ya ce.
“Idan da mai laifi to ni ne, don ni na hana Amiru yin wani yunkuri na dawo da iyalinsa har tsawon wannan lokacin. Ina so in koya masa jarumtaka, in nusar da shi cewa;
“kallafa rai a kan abin da ake so, da amanna da cewa samuwar abin nan kadai shi ne samun lafiya da kwanciyar hankali ba shi ne ba”.
Dauriya, hakuri da juriya da tawakkkali sune halayen da ake son namiji ya suffantu dasu. Kuma na gode Allah……. DUK WASU EXPERIMENTS DANA YIWA AMEERU BAI FADI KO DAYA BA…………..!!!”

Baffa ya jinjina kai ya ce.
“Nima in son samu ne, na fi son Mairo ta koma wurin mijinta ta tarbiyanci ‘ya’yanta a gabanta. Amma Alh. Junaidu ya zarta duk yadda kuke tunani a wurin mu. Don haka bana cikin wannan magana….. Zabi yana ga Mairo, tunda ita Allah ya baiwa damar zaben mijin da za ta iya zama da shi a halin yanzu. Don haka ku bani kwana biyu zan tuntube ta”.
Habibu bai ce komai ba, don ba shi da ta cewar, bai san me zai ce ba, bayan Allah ya yiwa Mairo zabin alheri, wannan karon ba zai yi shisshigi ba.


SUNA tafe cikin jirgi amma Daddy baya cikin nutsuwa. Tausayin gudan ransa ya ishe shi, ko ma me ya faru ya tabbata shi ya jawo mishi. Shekaru uku ba kwana uku ba!!! Ya nesanta Amir da iyalinshi a kan laifin da ba nashi ba. A kan hujjojin sa da basu da karfi.
Don haka suna sauka a jirgi ya bude waya ya kira Amiru yana nishi kamar mai ciwon asthma. Ya ce,
“Ka bar duk abin da kake ka taho, ka wuce Kano ka nemi sasanci da iyalinka in har kana so. Na amince maka Amiru, da sanya albarkata…. saura kwana goma sha hudu a daurawa Mairo aure!!!”

Ga mamakin Daddy sai ya yi murmushi, wanda har sautinsa ya ratso cikin wayar, ya ce.

“Ka kwantar da hankalinka Daddy, na dade da sanyawa zuciyata salama, na yi amanna da cewa idan akwai sauran zama tsakanina da Mairo, to za ta dawo mini ko ba dade ko ba jima”.

           ****

Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa ne a harabar gidan Dr. Mairo, wanda ke a Area C cikin sabuwar jami’ar Bayero suna wasan kwallon kwando, ya yin da a gefensu Habib da Amir ne tare da wasu sa’o’insu ‘ya’yan makota suke wasan tsaren kekuna, yara masu ban sha’awa. Suna sanye da kayan sanyi masu laushi farare sol, an rubuta I LUV MUMMY, kafafunsu daure cikin farin cambas, sunyi kyau har sun gaji kamar ‘ya’yan South-Western.

Daidai lokacin da motar kirar (Camero, 2 Door) ta yi parking and hankali a gefensu, matukin motar ya duba katin da ke hannunsa ya tabbatar lambar gidan ta yi daidai da wadda ya gani a rubuce. Sai ya kashe ya fito.
Sanye yake da suwaitar ‘Dolce & Gabbana’ mai dogon hannu, da shudin wandon jeans. Ya yin da rigar ta kasance fari da ratshin ja da blue. Ga duk wanda ya san shi, ba zai yi gaggawar gane shi ba, saboda yadda fatar jikinshi ta kara kwanciya, tare da goguwa mai nuni da alamun hutu. Ya jawo bakin PRADA ya saya kwayar idanun shi. Daidai lokacin da idanunshi suka kai ga sanyin idaniyarshi.
Ya dade yana kallon su yana murmushi, har bai san tsayin mintunan da ya bata a tsaye ba, ba tare da yaje gare su ba, don ganin yadda hankalinsu ya raja’a a kan wasansu. Har sai lokacin da Amir ya karawa Habib keken shi ya fadi, ya sanya kuka.
Da sassarfa ya karasa garesu, ya mika hannuwa ya dauki Habib wanda ke ta kuka ya rungume a kirjinshi, ya kuma kama hannun Amir suka doshi kofar gidan. Su Lawan suka gaishe shi suka koma ga kwallon su, Lawan na radawa Ahmed Baban su Amir ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button