ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL


J
irginsu ya sauka a Abuja karfe biyar na asubahi. Ban da kunci da kumburi ba abin da Mairo ta ke yi. Dina sai lallabata ta ke tana ba ta hakuri. Idan takaicin ya yi takaici, sai ta kai hankici ta tsane hakwayen da ke ‘racing’ a fararen kundukukinta.
Idan Dina ta ce “Ki yi wa Allah Mairo ki yi hakuri…”
Sai ta ce
“Haba Aunty Dina? Shekaru biyu ina wahala, in fadi, in tashi amma ace sun tashi a banza?”

Wani farin dattijo, dan kimanin shekaru sittin da biyar, wanda alamun jin dadi, tsantsar ilimi da gogewar rayuwa ya boye shekarun nashi. Sanye cikin kaftan na wata irin farar sassalkar shadda da akalla ta baiwa naira dubu dari baya, yana da tsagin biyu-biyu a gefen fuskarsa na Fulanin Gaya. Biye da shi escort ne har guda biyu cikin bakaken suit wadanda harsashi na kowacce irin bindiga ba ya huda su, sun maka ‘dark-spaces’ fuskokinsu kamar hadari, sabanin dattijon wanda kyakkyawar fuskarsa ke yalwace da ni’imtaccen murmushi wanda da alama tabbatacce ne akan fuskarsa cikin kowanne yanayi.
Abin nufi, cikin halin bakin ciki da farin ciki, kwanciyar hankali da tashin hankali, wannan sassanyan murmushin ba ya gushewa daga fuskarsa. A takaice dai na halitta ne, watau ‘nature’, shi ne a gaba wajen tarbar su Habibu a baya.
Don haka kwarjininshi da haibarshi ya sanya dole Mairo ta daina kukan da ta ke, ta tsugunna har kasa ta gaida shi. Ya dora hannun damanshi a kanta ya ce
“Barka da zuwa Maryamu. Godiya ga Allah da Ya sauke ku lafiya”.
Yaya Habibun kuwa ko arzikin kallo bai samu ba, sai matarshi ke binshi da kallon mamakin muguwar zabgewar da ya yi cikin kwanaki biyar kacal.

Mairo ta sha mamakin ganin ‘chebrolit’ yau a gida Najeriya. Motar da ko a America, sai wanda ya ci ya tada kai. Ba wannan ne kadai ya razanata ba, sai tangamemen ‘gate’ irin wanda ake kira ‘Mahdi ka-ture’ da aka wangame musu a lokacin da motarsu ta sawo kai cikin unguwar Asokoro. Ta hango wani irin ‘American billa’ mai kama da jirgin ruwa.
Ita dai Mairo ido ne nata, sai kuma ta cilla kafa duk inda ta ga an cilla. Tana cewa a ranta, watakila Yaya Habibu siyar da mu zai yi. Dama ni kudin nan nasa ai ban yarda da su ba. Sai dai kuma babu dar ko tsoro ko yaya cikin kalbinta, wadda ke cike taf da takaicin rabota da karatunta da aka yi babu gaira babu dalili.

A kofar wani kayataccen falo mai kofar gilashi Yaya Habibu, dattijon da sauran mutanen da ke take mishi baya suka tsaya. Su kuma aka sa wata mace wadda ga dukkan alamu mai aiki ce, ta yi musu jagora cikin gidan. Ta nuna musu dakin da za su sauka, sannan ta sanar da su cewa, matar gidan tana asibiti, idan sun kimtsa su danna ‘bell’ za a shigo musu da abinci. Dina ce ta amsa, amma Mairo ta zama hoto.
Dina ce ta fara yin wanka, sannan Mairo. Suka dauro alwala suka bada faralin sallar subhi da ta riske su a jirgi. Suka shirya tsaf, Mairo cikin ‘swiss lace’ ruwan madara da yarfin kananan duwatsu, riga da ‘wrapper zani’, ta yi ‘simple’ nadin kallabi a kanta. Dina cikin atamfar ‘super’ shudiya ita ma riga da zani da yalwataccen mayafi. A tsaitsaye suka ci abincin sabida kiran Yaya Habibu cikin wayar Dina cewa, su fito za su wuce asibiti.
A babban asibitin koyarwa na Abuja, ita Mairo ta sha wajen matar gidan suka zo da ta ji an ce tana asibiti, sai raba ido ta ke cike da son ganin wace ce mamallakiyar wannan ‘bungalow’ din. Wanda aka yi amfani da hikima, ilmi da tunani wajen sarrafa shi. Kai ita a iya yawonta cikin U.S ba ta taba ganin irin wannan ginin ba, wanda ta fahimci cewa gidan wannan farin dattijon ne, da ya je tarbo su filin jirgi.
Dattijon ne a gaba, sai ‘escort’ dinshi, sannan Habibu da Dina biye da shi, Mairo ce karshen shiga dakin, wanda ya kasance ‘amenity’. Sabida cikowar da dakin ya yi da kyawawan mata masu kama daya, kuma masu kananan shekaru akalla daga mai talatin sai mai kasa da haka, sai kuma ‘yammata tsararrakinta, wadanda ga dukkan alamu ko auren fari ba su yi ba, ta rasa inda tasan fuskarsu kamar ta sansu a wani wuri. Daga can gefe wata dattijuwa ce kyakkyawa cikin kyakkyawar suttura zaune bisa darduma, ta yi nisa cikin sujjadarta ba ta san me ake a dakin ba.
Cikowar da dakin ya yi, shi yasa Mairo ba ta yi nasarar hango ‘patient’ din ba, wanda ke ta kelayo aman jini, har da guda-guda. Daya daga cikin matan ta rike shi tana kuka, sauran ma duk sharar hawaye suke yi da gefen mayafansu, wanda ke nuni da cewa kauna ce mai tsanani tsakaninsu da dan uwansu.
Da sauri dattijon ya karasa gaban gadon ya tallafe shi cikin kirjinsa. Ya danna wani abu, da gudu likitoci biyar suka shigo. Nan suka yi umarnin kowa ya fita.
Mairo dama tana bakin kofa, don haka ita ce ta farkon fita. Dattijiyar ma tana sallarta ko dagowa ba ta yi ba, su ma likitocin ba su ce ta fita ba. Daga likitocin sai dattijon sai Habibu, wanda idanunshi suka kada suka yi jajur, zaka iya hango tsabar tashin hankalin da ke kwance cikinsu. Don ma yana dauriya ne, amma da fashewa zai yi da kuka.
Cikin gaggawa kowannensu ke ba shi taimakon da zai iya. Masu jona abin janyo numfashi na yi, masu auna bugun zuciya na yi, da ya ja wata doguwar ajiyar zuciya su dukka suka kalli juna suka girgiza kai, sannan suka ci gaba da aikinsu cikin kwarewa da sanin makamar aiki.
Kafin su cire ‘odygen’ din su yi wa Habibu da dattijon alamar su biyo su ofishinsu. Fitarsu ke da wuya leburori suka shiga dakin suka soma tsaftace wajen. Har zuwa wannan lokacin dattijuwar nan ba ta daina sallah ba. Ba ta daina kai goshinta gaban mahaliccinta ba, domin ta yi imanin Shi kadai ne zai tashi kafadar danta, amma ba wadannan tarkacen nasaran ba.

A can ofishin Dr. Fredrick Engles (consultant) na bangaren zuciya, bayani yake musu dalla-dalla na bugun zuciyar ba-zata da ‘patient’ dinsu ya samu, wanda ya yi mugun yi wa zuciyarshi illa farat daya.
Ciwon zuciya na lokaci daya ya yi mishi mugun kaye, wanda idan ba a yi gaggawar magance mishi damuwarshi ba, daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai zai iya faruwa. Ya kare da tambayarsu, shin ko sun san hakikanin abin da ke damun mara lafiyan? Domin su sunyi-sunyi ya fada musu, amma ya ki cewa komai.
A nan ne dattijon ya soma yi wa babban likitan bayanin duk abin da Amirun ya fada mishi ranar da ya dawo, kafin ciwon ya ci karfinshi. Wato kanwar Habibu yake so, ita kuma ta ce ba zata aure shi ba.
Habibu kuma ya dubi likitan ya ce
“Ni kuma na yi alkawarin zan aurawa Amiru Mairo, ko da a gobe ne, idan hakan shi ne zai zamo FANSA ga lafiyarshi. Ko da kuwa ace wannan shi ne abu na KARSHE da zan gabatar a rayuwata”.
Dattijon ya ce, “A’a Habibu, ba za a yi haka ba, a bi-ta a hankali, domin dai da na kowa ne, ban yarda a tursasata bisa abin da ba ta so ba”.
Dr. Fredrick ya ce
“Yanzu ina yarinyar?”
Habibu ya ce “Tana waje, sun zo tun dazu. Sai dai ba tasan abin da ke faruwa ba. Da kyar ma idan tasan Amirun ne kwance a gadon asibiti”.
Likitan ya ce “A kirawo ta”.

Habibu ya fita, jim kadan suka shigo tare da Mairo, duk da ranta a bace yake, amma ba zaka karanci hakan a fuskarta ba. Ta nemi kujera gefen Habibu ta zauna, kanta a sunkuye, Dr. Fredrick ya yiwa su Habibu alamar su fita, yana mai ci gaba da rubuce-rubucensa cikin ‘file’. Ofishin ya rage daga shi sai Mairo, har zuwa lokacin bai gama rubutun da yake yi ba. Daga bisani ya dago, ta karkashin farin gilashinsa yake kare mata kallo. Cikin ranshi ya ce, Dole maza su kwanta ciwo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button