ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuciyarshi ta kasa amincewa Mairo na sonshi, a ganinshi Habibu ne ya takurata ta aure shi, don haka akan me zai sallama mata soyayyarshi? Yana son ya koyar da ita sonshi da kaunarshi, ba wai sha’awarshi ba kamar yadda ya karanto karara cikin fararen kwayar idanunta.
Haka suka yi ta zama dungur-gur bisa kafet har aka yi kiran assalatu, kowanne na ji da miskilanci. An rasa wanda zai fara keta billensa, ya kwantar da kai ga dan uwansa. Ya rausayar da kai, ya ce
“Mu je mu sake alwala”.
Ba musu ta mike domin dama ta tsauwala da wannan zaman na babu gaira babu dalili.
Don haka koda suka idar da sallar Mairo gefen gado ta koma ta takure. Shi kuma ya ja filo ya jefa bisa kilishi ya kwanta. Ta leka ta hango idonshi a rufe ta dauka barci ne ya dauke shi, don haka ta mike ta warware laffayarta, yadda zata ji dadin yin barci, ta nade a gado ta ja bargo ta rufa. Wani irin fitinannen barci na fizgarta, hakan yasa ba da dadewa ba sarkin barayin ya yi awon gaba da ita.

Mairo ba ita ta farka ba sai wajejen karfe goma na safe. Shi ma din sakamakon feshin ruwan da ta ji akan fuskarta ne. Ta juya a hankali saitin da feshin ruwan ya ke, Amiru ne ke taje sumarshi. Ya yi shiri cikin bakaken ‘suit’ masu ban sha’awa.
Ta zuba mishi ido kurr kamar mayya, har yawun bakinta na tsinkewa, sakamakon wata matsananciyar sha’awarshi da ta kara saukar mata. Wannan mutum kamar Romeo ya ke, kamar an ce da shi ‘juya’ ya juyo suka yi ido hudu da ita, ya daure fuska sosai, ya ce
“Lafiya kike kallona? Ko na yi kama da tsohon saurayinki ne mai sunan aljanu? Haka kawai yarinya kin zama kurma, in dai ni ne to mu zuba, shege ka fasa”.
Ya kuta, ya sake cewa
“Halan Dina ko gayar da mutane ba ta koya miki ba?”
Ta dauke kai ba ta ba shi amsa ba, sannan ta yunkura ta mike ta fada bandaki ta yi wanka tare da wanke baki ta fito. Yana tsaye jikin sif dinta yana amsa waya, ga dukkan alamu da Harrit yake wayar, wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare ta. Ta yi saurin komawa bandakin don ta dauka ya fita ta aje tawul din ta maida kayan jikinta. Ta sake fitowa wannan karon ya gama wayar yana sanyata a aljihun wandonshi.
Ya bi-ta da wani irin kallo kasa-kasa ya girgiza kai, ya fita yana cewa
“Abinci za mu ci, ko yau ma ba za a ci da ni ba?”
Ko ta tafas ba ta ce masa ba, don ta lura neman baki yake yi da ita.
Ta shirya cikin shadda ‘orange’ babbar riga ‘senegalese’, ba ta yin kwalliya rankacau don haka kullum fatarta ta ke danya shar (fresh). Ba kankanuwar yunwa ta ke ji ba, don haka ta nufo falon ta cimmashi a ‘dinning area’ na falon. Kallo daya ya yi mata ya dauke kanshi, zuciyarshi na bugawa. Wannan yarinya kamar Juliet ta ke.

Ta ja kujera mai fuskantarshi ta zauna, sannan ta fara bude ma’adanan abincin, sinasir ne da waina, sai hadaddiyar miyar agushi wadda ta ji naman rago, a gefe farfesun hanta da Koda ne sai Shawarmah da snacks dangin su meat-pie, samosa, spring rolls da sauransu.
Cikin sassanyar murya ta ce “Can I serve you?”
Hakika ya ji wannan muryar har cikin kokon ransa. Bai iya ya amsa ba, illa kai da ya gyada mata, don haka ta fara da hada mishi ruwan ‘lipton’ mai zafi da ganyen ‘Hemorrhoid tea’, sannan ta zuba mishi Sinasir din da farfesun a faranti daban-daban.
Ya yi mata wani sassanyan kallo ba tare da ta sani ba, sannan ya soma ci. Ta hada ‘lipton’ ta sha, amma ta yi-tayi ta ci abinci a gabansa ta kasa. Ta mike ta ce
“Zan shiga wajen Hajiya”.
Ya ce
“A’a, sai kin ci abinci na gani tukunna”.
Ta koma ta zauna, ta dauki sinasir guda daya, ta sanya a faranti ta soma ci cike da kunya. Ya tura mata farfesun gabanshi ya ce, “Cinye shi”.
Ba musu ta karba don ba zata iya yin jayayya da shi ba. Sai da ya tabbatar ta cinye, sannan shi ma ya mike yana cewa
“Mu je na rakaki wurin Hajiyar”.

Tare suka jera har gidan Hajiya. Tana sallar walha sanda suka shiga a karamin falonta. Sai da ta idar ta shafa addu’o’inta sannan ta juyo gare su, cikin matsananciyar kauna ta mikawa Mairo hannu
“Zo dawo nan kusa da ni diyata”.
Sai ga su Sabah su ma sun fito, suka gaida Yayansu wanda ya maida hankali ga amsa kiran da ke shigowa cikin wayarshi.
Daga karshe ma fita ya yi ya barsu, bayan ya fadawa Hajiya zai je ya raka bakinshi airport. Su Amina kamar su hadiye Mairo. Nan ta wuni sur tare da su.
Bai dawo ba sai bayan la’asar, lokacin da ya shigo tana kicin ita da su Sabah suna hada abincin dare. Hajiya na falo ta ce
“Sai yanzu?”
Ya ce
“Wallahi kuwa, ai bakin nawa ne suna da yawa, kuma jirage daban-daban za su shiga, amma dai alhamdulillah duk sun tafi sai fatan Allah Ya sauke su lafiya”.
Hajiya ta kwalawa Mairo kira, ta fito ba tare da ta iya hada ido da Amirun ba. Wanda ya bita da kallo kamar bai santa ba. Ta russuna gaban Hajiya cike da girmamawa, Hajiya ta ce, “Shi miji idan ya dawo yana bukatar kulawar matar sa, ta hanyar yi mishi sannu da zuwa, da ba shi abu mai dan sanyi ya sha kafin a gabatar mishi da abinci. Don haka bi shi ku tafi, su Amina za su shigo muku da abincin idan an karasa”.
Cikin jin nauyi ta ce
“to Hajiya”.
Shi abin ma dariya ya ba shi, wai wannan katuwar ake koyawa kula da miji, Hajiya ba ta san yaran zamani da wayonsu ake haifarsu ba, balle Mairo rainon Dina, kula da miji sai dai ta koyawa wasu, sai dai in ba ta sa kanta ba.
A ‘bedroom’ dinta ya cimmata, tana kokarin sauya kayan jikinta. Duk dauriyarshi da jarumtakarshi ya kasa sarrafa kanshi, don haka ya yi hanzarin komawa da baya ya ja mata kofar. Ta yi saurin juyowa amma ba ta ga kowa ba, sai karar rufe kofa.
Ta ci gaba da abin da ta ke yi kamin ta jiyo sallamar Amina da Rayyah a falo. Ta fita suka aje abincin a ‘dinning. Suka yi ‘yar hira ba su jima ba suka fita. Ba ta san dakin da ya shiga ba, ko ta sani ma ba zata shiga ba, don haka ta zauna nan falon tana jiran shi sai zuba kamshi ta ke.
Zamanta da wajen mintuna ashirin sannan ya fito, da alama wanka ya fito. Wannan karon cikin shigar kananan kaya, farar shirt din (Tommy Hilfiger) da bakin wando Tokyo. Sai ‘miyaki’ ke tashi. Mairo ta daga kai a hankali tana kallonshi. Wani irin abu na tsirgawa cikin jikinta yana tada tsigogin jikinta. Kallo daya ya yi mata ya karanto halin da zuciyarta da ma gangar jikinta ke ciki.
Ya murmusa ya daga gira ta kara rikicewa, a ranshi ya ce “munafuka! Idan dai wannan Amirun ne yarinya, to kwalelenki har sai kin so shi, kin kaunace shi don Allah, tunda kiri-kiri kin fada mishi cewa ba kya sonshi, akwai wanda kike so, don haka wannan jikin ma da kike wa marmari ba zaki same shi ba”.
Abincin da Mairo ba ta iya ta ci ba ke nan, sabida gani ta ke kamar Amirun yana karanto zuciyarta. To da gaske hakan ne, tunda yake shi din ba yaro ba ne. Ya fita ilmi da hankali nesa ba kusa ba. A kwayar idanunta ya gama gane ta tsaf.
Yana kallonta sai caccaka cokali ta ke cikin abinci ta kasa kai ko loma guda. Shi kuwa cin abincinshi yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana kallonta a kaikaice. Wani zubin ya yi murmushi, wani zubin ya girgiza kai. Wannan karon bai takurata da lallai sai ta ci ba, don ya tabbata ba zata ci din ba. Dan Abdurrahman Gaya, kadai ta ke so a jikinta.
Kararrawar kofar shigowarsu ta yi kara, wannan ne ya ceci Mairo daga kaifafan idon Amiru. Da azamarta ta mike ta nufi kofar ta bude. Ta sha mamakin ganin Daddy da kansa. Cike da girmamawa ta ba shi hanya ya wuce.
Sai da ya zauna a ‘seater’ ta zube a kasa tana gayas da shi. Ya ce
“Yaya bakunta Maryamu?”
Ta ce
“Alhamdu lillah”.
“Babu wata matsala ince ko?”
Ta ce
“Babu Daddy”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button