ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba.
To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin dare, haka suke kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci.
Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar zuwa maternity inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida, domin abin ya fi karfin asibitin makaranta.
Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu’a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso. Kokarin Uncle shi ne Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin Kausar da halin da ta ke ciki ya hanata zama lafiya.
Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin. Captain da Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta.
A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin Metron suna tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar?
Ta ce “Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce”.
Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da Nabilah. Tun daga ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne, dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa.
Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan ta kara rungumar Maryam a matsayin ‘yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar.
Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah kowacce cike ta ke da zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta dauko na talatin da takwas yayin da Nabilah ta dauko na arba’in.
Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi abin da zai ji dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin.
Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana uku, don haka a kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin ma Inna Hure da shiga goma, fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ire-irensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba ta nemo ta ajiye mata ba.
Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa.
Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin kowa nasu. Nabilah ta ce “Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu wurin Auntyna”.
Maryam ta jinjina kai ta ce “Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin Fanshekara”.
Nabilah ta ce “Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan ki gaya min ki gani”.
Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon.
Mairo ta ce “Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan Malam Bedi kowa ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu ‘MAIRON HURE’ da gudu za su rako ki”.
Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma ya dauke cikin kakkaifar kwakwalwarsa.

“Lah, ga Babana nan!”. Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta rungume Malam Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta hango ta rungume da wani yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta ce a ranta, “Ya za a yi ace wannan ne ya haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta”.
Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba, a’a, wahalar rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye.
Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita ‘yar talaka ce futuk, amma she is contented with what she habe (a gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba).
Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita ‘yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah tambayar kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne kawai ya dame ta.
Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa.
Mairo ta ce “Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta rasu”.
Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, “Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar”.
Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, “Amin”.
Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A haka cikin rashin jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da ‘yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must Go) suka fita. Sun sha wuya matuka irin ta motocin haya kamin Allah Ya kawo su gida.
Ganin irin wuyar da Babanta ya sha ya sa ta alkawarta wa ranta daga wannan hutun zata hutar da shi kai ta makaranta da dawo da ita, tunda ta gane hanya zata dinga tafiya da kanta.
Tunda yaro ya shigo da jakar Mairo Hure ta biyo bayansa da saurinta. A soro suka yi kacibus, da Mairon nata. Suka rungume juna kamin Hure ta soma hawaye ta ce “Ashe wannan ranar zata zo Mairo, ranar da zan kara ganinki?”
Mairo kuwa baki ya ki rufuwa a haka suka karasa cikin gidan kamar wadanda suka shekara ba su ga juna ba.
Inda duk Inna ta mika hannu sai ta zarowa Mairo abin sawa a baka, ta ci ta yi nak! Ta ci girkin Innarta da ta yi kewa, ba kadan ba. Duk da cewa abin da ta ke ci a makaranta ya fi na gidansu amfani a jikin dan Adam.
Hure ta kasa boye mamakinta, ta ce “Shin mai kike ci a makarantar nan ne Mairo? Kinga kuwa yadda kika zama buleliya, kika yi fari sai sheki kike?”
Mairo ta sa dariya, ta ce, “Ba abin da bana ci Inna. Tun daga kan kwai, dankali, agada, doya, madara, nama da kifi ba abin da ba a bamu. Har ‘ya’yan itace (fruits) ba dole in zama buleliya ba?”
A ranar dai Mairo da iyayenta kwanan zaune suka yi, tana ba su labarin rayuwarta a makaranta. Sai dai fa duk rabin hirarta, “Uncle Junaidu” wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wurin sama mata farin ciki da walwala a cikin dalibai ‘yan uwanta.
Malam Bedi ya ce, “To Allah Ya saka mishi da alkhairi”.
Sai dai a cikin labarinta ba ta kawo labarin saran sa macijiya ta yi mata ba, don ta tabbata idan suka ji, kidimewa za su yi su ce ba zata koma ba.
Hutun Mairo gwanin ban sha’awa a gidansu, gabadaya yanayin rayuwarta ya canza, ba ta barin Innarta da aiki ko ya ya, sai ta karba ta yi. Haka ta ke bin babanta gona tana taya shi shuka da ban ruwa. Abokinta Rabe da ya ji ta zo hutu daga makarantar kwanan da aka kai ta, sai ya aiko yaro rannan da yamma wai Mairo ta zo su je su hau tsamiya. Malam na jin sanda ta maida dan aiken ya tambayo mata Rabe, shin yanzu ta yi masa kama da ‘ya’yan birrai ne da zai ce ta zo ta hau bishiya?
Sai ya yi murmushi yana kara shi wa Habibu albarka a zuciyarsa.
7/28/21, 4:41 PM – Kawata: 4999

*** ***

Uncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi ta zaman makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun yi wa Inna Hure gaisuwa. Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure, ya kara yi mata ta’aziyya, ya kara da nasihu masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba tareda ita ba.
Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce “Wata rana aure zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka ki taimake ni in rike nauyin da marigayi ya aza mani akan karatunki”.
Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa zai dinga nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji kan bawa, washegari sai ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce, wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu. Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata koma.
Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta’aziyyar babanta wanda ta ji a bakin Uncle Junaidu.
Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani tsakaninta da mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta samu kanta da son yin abin da zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU.
Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai cikin harshen Turanci a kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar sakandire aka ba ta kallabin ‘AMIRA’ sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce ja gaba a club din Uncle, watau English club.
Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa club din DRAMA Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata wadda ke bai wa kowa mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya da sharri, ba zaka ce akwai soyayya tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button