ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Har suka iso gida, Dina na jinjina kalaman Amiru a zuciyarta. Ta sanshi, ta san halinshi kamar yadda tasan mijinta. Karya ko joking ba sa cikin halayyarsa, idan ya ce yes, to da gaske yana nufin yes din babu gudu babu ja da baya. Babu kuma abin da zai sa shi ya janye abin da ya sa gaba.
Wani irin mutum ne mai nasara akan duk abin da ya sa gaba, wato dai irin mutanen nan ne masu ra’ayin kansu, ba masu fadin karya don wani ya ji dadi ba. Hakanan ba sa iya boye abin da ke zuciyarsu.
Ta dade tana addu’ar zuwan ranar da Allah zai nuna mata mijin Mairo, ta sha kissima yaya mijin Mairo zai kasance? Domin ita din ‘yar baiwa ce kamar Habibu. To amma ba ta taba tunanin Amiru ne zai ce yana so ba. Kololuwar ilmi, nasaba, arziki, kyau, nagarta duk shine. Bankin duniya yana hannunsu, kudin Najeriya gaba daya yana hannun ubansa, sai ya rattaba hannu a kansu za a yi amfani da su, ko ‘yar shugaban kasa yake so zai aura. Duk kalar macen da yake so da gudu za a ba shi, amma ya ce; MAIRO, a ganinta wannan abin alfahari ne a gare su, ita da Habibu domin Amiru ba zai yi karya ba, ba zai yaudare su ba. Ba zai fadi abinda ba haka yake a zuciyar shi ba. To mai yasa Habib cogewa?
Ta san abin da yake gudu ba zai wuce Harrit da ‘yammatan Amirun ba, domin iyayenshi mutanen kwarai ne, ‘yan jiya, bana yau ba, kuma Habibu kamar Da ne a wajen Abudrrahman Gaya. Da irin wanda ya tsugunna ya haifa. Shi ya dau nauyin karatunshi tun daga master har PhD da sauran kwasa-kwasan da ya halarta. Yasan kuma amintarsu da Amiru ba tun yau ba, don haka ta ke ganin ta wannan fannin ba za a samu matsala ba.
Idan ma akwai matsalar ta fannin Harrit ai shi Amirun ba yaro ba ne, yasan yadda zai tsarawa kanshi rayuwa.
Suna kicin ita da Mairo lokacin da Amiru ya iso. Dina ba ta ce mata komai ba, sai ta yi ma kamar ba tasan zancen ba. Shi da Raymond ne sakatarenshi, suna hira kan harkokinsu shi da Habibu, amma duk hirar ta gundire shi, sai baza ido yake don ganin ta inda Mairo zata bullo, amma shiru. Habibun na hankalce da shi, yau surukuta sosai yake nunawa, duk sai dariya ta kama Habibu, sabida wani ‘respect’ na musamman da ya lura Amirun na bashi. Ya yi fes cikin ta-zarce, na farar shadda excellencior duk da kullum cikin kwalisarshi ya ke amma Habibun bai taba ganin ya yi mishi kyau irin yau ba, to ina ga ‘yammata?
Wadanda ke jin kamar su ja shi ta karfi, to amma fa banda kanwar Habibu ‘Mairo’, wadda kallon fuskarshi ma ba zata iya yi ba idan ba dole ba.
Hakurinshi ya kare, tare da duban agogon hannunshi. Shi dai kawai so yake ya ganta, ko hankalinshi ya kwanta, amma Habibu ya share shi kamar bai san halin da yake ciki ba.
Cikin ikon Allah sai ga Dina ta fito daga kicin ya ce “Wai Dina ina kanwarkin nan ne?”
Ta murmusa ta ce “Tana aiki ne”.
Tsam! Ya mike, kanshi tsaye ya doshi kicin din. Ta juya baya tana yayyanka fruits cikin wata katuwar silba, daga bakin kofa ya tsaya ya tokare hannunshi a kofar. Ya shagala sosai a cikin kallonta har ya manta abin da yake yi, bai san kuma iyakacin mintunan da ya bata a tsayen ba.
Dina ta dawo ta ce “Ba ni hanya malam”.
Ya matsa, ta wuce ciki tana murmushi kasa-kasa, a sannan ne ma Mairon tasan da mutum a tsaye. Ta cira kai ta dube shi, shi ma duban nata yake cikin lumsassun idanunsa. Bai san me zai ce mata ba ta fahimci masifar sonta da Allah Ya dora masa. Yana daga cikin mutanen da harshensu bai iya bayyana abin da ke karkashin zuciyarsu. Sai dai action da emotion dinsu ya nuna. Da Mairon zata daure ta dube shi, da ta gane yadda ya yi laga-laga cikin SOYAYYAH. To amma ta ki, kallo daya ta yi mishi ta dauke kanta, bata sake marmarin maimaitawa ba.
Ya karaso ya karbi wukar da ke hannunta ya ci gaba da yanka mata gwanda (paw-paw). Dina ta dau abinda zata dauka ta fita. Ta mika hannuwa cikin sink ta wanke hannu ta juya zata fita.
Ya dago a galabaice, muryarshi har ba ta fita sosai, ya ce “Idan kika fita zan yi miki Allah Ya isa ne…, tunda Manzo ma ya ce, “BAKONKA, ANNABINKA…” Idan kika fita kin wulakanta ni, shin ma mene ne gare ni da kike guduna? Na yi miki kama da dodon da zai cinye ki ne?”
Ta ja turus, ta tsaya, ita ba ta fita ba, ita ba ta juyo ba. Ya ajiye gwandar ya sha gabanta sosai har tana jin hucin numfashinsa. Wanda ke sauka da sauri-da-sauri. Kwayar idanun sun rikide, sun haukace da soyayya. Ban da alkawarin da ya daukarwa Habibu, da wallahi rungumeta zai yi, sannan ne yake jin zai iya gaya mata ko mene ne ke cin ransa, zuciyarsa da gangar jikinsa a kanta. Amma a haka ba zai iya bata bakinsa ba, ba zai iya ce mata komi ba. Da kyar ya daure ya langabar da kai, ya ce “Yi min magana mana, don Allah, Mairo? Mairo ko ba kya SO na?”
Nan ma shiru, kai ka ce da gunki yake magana. Don ita jin abin ta yi banbarakwai, wai namiji da suna Hajara, tunda dai babu wanda ya taba tararta da wannan kalmar, wai….. Ya katse tunaninta da cewa, “Mairo Allah Ya jarrabce ni da sonki, tun daga lokacin da Allah Ya dora idanuna a kanki. Duk wani saukar numfashina a yanzu da sunanki yake fita, duk wani tunanina a yanzu na yadda zan mallake ki ne a matsayin matata, uwar ‘ya’yana.
Sunana Ameeru Abdurrahman Gaya, ni kadai ne da namiji a wurin iyayena, ina da kanne mata goma sha biyu. Na yi dukkan karatuna tare da Habibu. Iyayena ‘yan Gaya ne suna zaune a Abuja, amma mu ‘yan asalin garin Gaya ne da ke cikin jihar Kano, ina aiki a Washington, sai dai kwanan nan zan bari in koma gida.
Ina da mace daya da ‘ya’ya zero. Duk wani abu da kike son ji game da ni, ki tambayi Habibu, zan samu karbuwa Mairo? Mairo ko ba kya so na?”
Ya tsare ta da wani irin kallo daga can karkashin kasan lumsassun idanunsa.
Mairo ta rasa inda zata sa kanta. Ga kunya da ta baibaye ta, ga jin nauyi, don ganinshi ta ke kamar Yaya Habibu. Idan ta ce ba ta sonshi ta yaudari zuciyarta, haka idan ta ce tana sonshi ta yi karya. Mutum daya ta ke wa ‘SO’ na hakika, wato UNCLE JUNAIDU. To amma shi wannan jinsa ta ke har cikin kasusuwa da bargonta ba zuciya kadai ba, da wani al’amari mai ban mamaki da ba zata iya fassarawa ba.
Tunaninta shi ne, ba zata iya hada rayuwarta da kowa ba, idan ba Uncle Junaid ba. Ta dauki al’amarin da ta ke ji akan Amiru da BURGEWA da SHA’AWA, wato yana burge ta, yana bata sha’awa, yana daukar hankalinta, yana bijiro mata da sha’awar tayi aure. Zata iya aurenshi don ta mallaki gangar jikinshi, amma ba don so ba. Idan aure ne kadai hanyar da zata samu mallakar abin da zuciyarta da gangar jikinta ke so daga gare shi, to zata iya aurenshi don ta samu, amma SO guda daya na UNCLE JUNAIDU ne!

Wata irin kunya ta kamata, da ta yi wannan tunanin, don gani ta ke kamar ya hango abin da ta ke sakawa da warwarewa cikin zuciyarta. Tana tunanin idan ta yi hakan kuma ai ya zama yaudara. babbar yaudara kuwa, don haka ta soma tunanin yadda zata yi ta gudu, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Yadda Uncle Junaid ya yaudare ta, ta san ciwon hakan, ko ba don komi ba don amintarsu da Yaya Habibu da mutumcin da ke tsakaninsu kamar yadda Yaya Habibu ya gaya mata, mahaifin Amiru shi ya dauki nauyin karatunsa daga masters har PhD. Sabida haka ba yadda za a yi ta yaudari Amiru wata rana ta rabu da shi idan ta samu Uncle Junaidu.
Haka nan idan ta ce ta yarda tana sonsa ita ma ta yi sallama da burinta na WATA RANA zata hadu da Uncle Junaid su yi aure a lokacin da Allah Ya nufa. Gara ta ci gaba da dakon soyayyarsa, don idan ta yi aure ya tabbata ita da Junaid kenan HAR ABADA!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button