ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan bisiting da sati biyu, rannan Mairo ta fito domin yin fitsari da daddare a lokacin Kausar ma ta fito ta tsugunna a bakin rariyar hostel tana goge bakinta domin ta kwanta. Mairo na daga bandaki ta hangi wani mulmulallen abu mai sheki da tsayi na sanda ya nufi Kausar. Ta ware idanunta gabadaya sai ta gane katon maciji ne wanda ake rade-radin akwai a makarantar.
Ta yar da butarta ta sheko da gudu dai-dai sanda macijin ya fasa kai, ta angije Kausar tun karfinta ta wulwula ta fada kwatami da baka, abin tsautsayi, sai kulbar (macijiyar) nan ta huce fushinta a kafar Mairo, wato ta sare ta.
Kausar ta mike cike da bala’i a lokacin idanunta suka gane mata abin da ke faruwa, dai-dai lokacin kulbar ta sulale tana komawa inda ta fito, ga kuma Mairon da ta angije ta kwance a kasa ba yadda ta ke. Ta daura hannuwa aka ta rafsa ihu, wanda ya ratsa gaba dayan hostel din, student da metron suka fito. Kausar ta ce “macijiya ce ta sare ta.”
Ai jin haka captain ta suri Mairo, sauran yara suka bi ta yuuu! Har da su Kausar sai gidan principal ana buga mata kofa.
Ta fito a gigice ita ma nan take ta bugawa school doctor waya, nan da nan sai ga ta, aka wuce da Mairo asibitin makaranta, Doctor ta dukufa ga son ceto ranta.
Kausar da Nabilah suka kasa komawa hostel ko babu komai akwai tausayin rai a zukatansu, balle ita Kausar da tasan hakikanin yadda abinda ya faru. Nadamar abubuwan da ta ringa yi wa Maryam Bedi, suka shige ta. Ta ji tausayin Maryam matuka, ta kuma tambayi kanta, shin ko wace irin zuciya ce da ita? Irin su Maryam ne masu rama sharran da hairan, babu shakkah ta yi nadama.
Nabilah ta yi mamakin damuwar Kausar akan Maryam ta yi yawa, ta kasa ko magana. Ta ce “Kausar kowa ya koma hostel sai mu, ni fa tsoro nake ji”.
A salube Kausar ta sa kafa cikin dan karamin asibitin ta samu benci ta zauna, ba ta da niyyar tashi. Nabilah ta biyota cikin mamaki, ta ce “Wai me ya faru ne? Ba zaki zo mu tafi ba?”
Ta ce “Je ki abinki Nabilah. Amma ni a nan zan kwana”.
Nabilah ta kama baki, dai-dai lokacin da Mummy Dukku wato principal ta fito zata koma gidanta. Ta hango su Nabilah ta ce, “Ku kuma me kuke a nan ba ku koma hostel ba?”
Kausar sai ta sa kuka. Ta matso ta dafa kanta domin ta santa farin sani sabida mahaifinta, ta ce “kawarku ce ince ko?”
Nabilah ta yi saurin cewa “A’ah, dakinmu ne kawai daya”.
Mummy ta lura da kukan da Kausar ta ke sosai ta ce, “Ke kuwa tausayinki ya yi yawa Kausar, alhamdu lillahi dafin bai shiga cikinta ba, kuma Doctor ta zuke shi. Insha Allah zuwa safiya za ta warware, tashi ku tafi dare ya yi sosai”.
Sai da suka je daki ne Kausar ta ke gayawa Nabilah hakikanin yadda akai maciji ya sari Maryam. Ta ce “Yanzu ni tashin hankalina shi ne, idan ta mutu ban nemi gafararta ba ina zan sa kaina?”
Jikin Nabilah ma ya yi sanyi, ta ce, “Allah Sarki, irin su ne ake cewa masu halin ‘yan aljannah”.
Suka yi jugum-jugum har wayewar gari ba su runtsa ba, nadama ta ishe su, sai kuma kaunar Maryam farat daya ta bi zuciyoyinsu.
Washegari Uncle ya zo kiran suna kamar yadda ya saba, cike da mamakin rashin ganin Maryama a class don kullum ya shigo idanuwanshi akan wurin zamanta yake. Duk da haka bai fasa kiran sunan ba, har ya zo No. 40, shiru ba ta amsa ba.
Ya dago manyan idanunsa ya zubawa Kausar cike da zargi kamar ita ce ta boye Maryaman.
Ya ce “dakin ku daya, tana ina ban ganta ba?”
Kirjinsa har wani harbawa yake da sauri-da-sauri. Fargabarsa kada ace da shi iyayenta sun cire ta daga makarantar sabida su Kausar. Bakin-cikinsa shi ne yau ace Maryama ta bar makarantar nan. Tashin hankalinsa shine ko sunan kauyensu bai sani ba, alhalin yanzu yadda yake kaunar Ilham haka yake kaunar Maryama. Idan zai iya rabuwa da ita, to hakika zai iya rabuwa da Ilham.
Cikin in-ina Kausar ta ce “Maciji ne ya sare ta, tana kwance a maternity…”
Tun kamin ta kai karshe Uncle ya fita. Ya doshi maternity cikin matsanancin tashin hankali, ko gani ba ya yi sosai. Ya banka kofar da kafarsa babu neman izini.
A kwance ta ke, idanunta a rufe, rana daya kacal ta zabge, ta yi wani irin fari fat kamar babu jini a jikinta, sannan ta kumbura kamar an hura balam-balam.
Nurse din da ke kokarin daura mata ‘drip’ ta juyo a razane ta dube shi, bai kula ta ba ya karisa gaban gadon da Maryam ke kwance ya tsaya kurum yana kallonta. Kamar an ce da ita bude idonki, ko kuma alamar tsayuwar mutum ta ji a kanta oho, ta bude fararen idanunta a hankali wadanda suka kumbura suka yi mata nauyin budewa, a hankali ta ce “Uncle……..” Sai hawaye suka zubo ta gefen idonta.
Ya yi saurin kama hannun damanta, ya ce “Sannu Maryama, sannu kin ji. Allah Ya ba ki sauki”.
Ya juya ga nurse din ya ce “Edcuse me madam Serah, na yi miki shisshigi cikin aikin ki. Maryam na daga cikin dalibai na masu muhimmanci a gare ni. Ki yi hakuri”.
Ta yi murmushi ta ce “Ai na ga alama, wannan patient din taka akwai raki da saurin kuka. Na dauka dadi zaki ji da kika ga Uncle sai kuma ki kama kuka?”
Mairo ta maida idanunta ta rufe tana murmushi. Ta nemi ciwon da jikinta ke yi ta rasa, sabida kasancewar Uncle Junaidu tare da ita.
Suna magana a kanta shi da Madam Serah ta gaya mishi wannan macijiya ta dade tana sarar dalibai, anyi duk iya kokarin da za a yi don ganin an fitar da ita daga makarantar an rasa. Wani zubin sai a yi tsammanin ma ta mutu don sai a yi shekaru biyu ba a ji duriyarta ba. Amma yanzu kam za a daukaka zancen zuwa federal da yardar Allah za a fitar da ita.
Ya ce “Maryama ta kumbura, ta yi biyun yadda ta ke”.
Ta yi murmushi ta ce “Jini ne babu isashshe a jikinta, wanda aka zuke tare da dafin amma already an tafi a sayo wanda za a sanya mata a asibitin Aminu Kano”.
Hankalin Uncle ya tashi, ya ce yana son ganin Doctor Nanah, ta ce tana ofis ka karisa.
Ya samu Dr. Nanah a ofis cikin tashin hankali. Ta ce “Yaya dai Uncle Junaidu?”
Ya ce “So nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina”.
Ta ce “To bari in diba kadan a auna a gani”.
Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu gwaje-gwaje da akayi, sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai ringa ci har zuwa kwana bakwai.
Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A’ah, cece-kuce ya soma (round) zagaye makarantar musamman daga ‘yan ajinsa da daman suna hankalce da su. Yara kanana da su amma sun iya gulma. ‘Yan manyan aji kuwa masu yi masa asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu yi mata mugun kallo.
Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da ta ga Maryam din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta zauna ba ta ce komai ba.
Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce “Don Allah don Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da sacrifice (sadaukar da kan) da kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana”.
Mairo ta yi murmushi ta ce “Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni. Amma shi ke nan, komi ya wuce”.