ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da ciwon kafar Inna ya yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da ita. Don haka Mairo ta kara kadewa ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda kacal zai yi.
Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu shakka ya manta da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa wani mugun al’amari ne ya faru da shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba.
Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya yi kuskuren fita babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga wani chemist inda ta amsowa Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta, wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta asibiti, amma Innar ta ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba.
Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt (Armani) da dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa. Duk hazo ya ba ta tsararren gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga Minjibir sabida rashin komawata makaranta.
Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa, tana karasowa ta russuna tana gayas da shi ya ce “Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi”.
Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan wuta, kana suka karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar ta yi, tana kwance bisa katifar auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin komowar Mairo makaranta.
Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido.
Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce “Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi asibiti”.
Ta ce “Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!”
Ya ce “Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi tare da maganinsa ba”.
Ta ce “Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru……..”
Cikin matsananciyar damuwa ya ce “Wane abu ne kike gudu Inna?”
Ta ce
“Zaman Mairo da Iyalan Abbas”. Daga haka ta yi shiru.
Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare suna kwance ta ce “Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI”.
Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce “Inna ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai mutunta juna”.
Inna ta yi murmushi ta ce “Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu.
Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba?
Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki…….”
Cikin gundura da zancen ta ce “Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne”.
Inna ta yi murmushi ta ce “Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a alkinta min ke”.
Ta ce (kamar ta yi kuka), “Ni dai don Allah Inna ki bari……..”.
Ta ce “Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba”.
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce “Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?”
Ta ce “Na bari”.
Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin alwala, ta zo gittawa ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga kafafun babu karfi, ta zame ta baya sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke hannunta.
Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta kasa yakice al’amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna ya tabbata gaskiya? Uncle Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa’a zata yi a rayuwarta?
A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka fara game mata jiki.
Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin sura, halayya da kyawawan dabi’u.
Ta kasance ma’abociyar karance-karancen littattafan nobels’ na Turanci. Littattafan Shakespear, Wole Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata karanta ba. A duk lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al’amarin jaruman littafin da Uncle da ita kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa cikin ranta, “Kaman Uncle Junaidu”.
Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma’abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da matsayin da yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne)
Mutum ne da yasan mene ne ‘dressing’ wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da da zubin halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan ya shigo, sabida kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara’a amma yana da zucciya, abu kadan sai ya bata mishi rai, haka abu kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta taba ce da Nabilah matar duk da Uncle ya aura ta caba.
Nabilah ta ce “Dalili?”
Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na sociology mai banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar da diya mace a shimfida, kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin da zasu yi masu. Tana jan layi-bayan-layi tana fassarawa Nabilah.
Ta kare tana murmushi, ta ce “Edactly Uncle ko?”
Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta nakalci harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce “Ke dai wallahi shegen karance-karancenki sai ya lalataki. Yanzu ina ke ina littafin ‘yan jami’a? Tukunna ma ina kika samo shi?”
Ta yi dariya cikin nishadi ta ce “A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi staff-room na ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke”.
Nabilah ta ce “To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce”.
Maryam ta ce “Da Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology. (With first-class honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan”.
Nabilah ta ce “Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu da Nasara?”
Ta ce “Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta”.
Nabilah ta kyabe baki ta ce “Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so”.
Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, “Ku gama kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….”.
Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu.