ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a ranta “Shin ko dai Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu? Neman tabbacin hakan abu ne mai matukar wahala a kwawalwarta”.
Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta ya soma bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, babu Inna babu alamarta.
Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta ce, “Inna kina ciki ne?”
Shiru babu amsa, ta ce “Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba”.
Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata da abinta cikin kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda karfen guga ya makale ya yage. Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita. Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama, maganar motsi kuwa babu shi a tare da su.
Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu, kafarta babu takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama’ar kauye, ma’abota hadin kai da taimakon junansu, nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure Allah Sarki!!
Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama hancin suka rike, daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su.
Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta. Innan da ta rage mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda kanta yake ba.


F
arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an kai ta makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta kuka kamar ranta zai fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, “Wannan ba shi ne karshen rayuwarki ba Mairo. ‘Ya’ya nawa ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya rasu, lokacin haihuwata uwata ta rasu, amma gani nan da nawa ‘ya’yan goma sha uku. Ina yi miki ta’aziyya Allah Ya jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri”.

Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu’a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da uba ba karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya kamar iyayenta? Ina zata je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar da haihuwarsa tai wa iyayensu ba.
Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta dauki loma ta kai bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame hannunta tana sharce wasu dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna addu’a ba.
Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta suturce jikinta ta tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta bude Alkur’ani mai Tsarki ta shiga karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da (du’a’ul mutawaffa) tana addu’ar Ubangiji Ya yi mata masauki da aljannah.
Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta, ta ba wa Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin Gurin-Gawa suka zo suka same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta’aziyyah, sanan Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce amanar da za su sauke.
Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, “Wata kila abin da nake gudu ne dole sai ya faru… Zaman Mairo da iyalan Abbas”.
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce “Hakuri za ki yi Mairo, mutuwa riga ce akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure”.
Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta tana kuka.
Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin gadon bononta. Ta tattara ‘yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo.
Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da ‘ya’yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi.
Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa Yakasai ta nan.
Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai.
Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu.
Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce “Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba”.
Ta dukar da kai ta ce, “Gurin-Gawa”.
Habiba ta kalle ta sosai na ‘yan dakikai, nan da nan fara’ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko’in’kula ta ce
“Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?”
Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce “Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne”.
Sai da ta mula ta ce “Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa”.
Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar.
Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce “Bude motar ki kwaso kayanki mana ki shiga da su?”
Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce “A’a, mu dai jira Baffan”.
Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce “Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne”.
A ranta ta ce “Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa”.
Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce “Ah! Yau wace rana?”
Ta yi murmushi, ta ce “Ladidi ke nan, kuna lafiya?”
Ta sake kyabe bakin (ga alama al’adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce “Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?”
Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne zuciyarta ta bi ta a baya.
Suna shiga Habiba ta ce “Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan”.
Ta sake kyabe baki, ta ce “Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba”.
Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce “Wa nake gani kamar ‘yar gidan Hure?”
Habiba ta ce “Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo”.
Hajara ta saki labulenta tana cewa, “Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba wajenmu kika zo ba”.
Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji Abbas. Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki.
Haka Ladidi ta shige dakinsu na ‘yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa sororo! Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da Innarta ta ke guje mata ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa, kowa tasa ta fishshe shi.
7/29/21, 10:05 PM – Kawata: 0989
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, “Mairo?”
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
“Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?”
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
“Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki je?”
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin.
Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen kayan ma’ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka’ida da dokar duk da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka’ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
“Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin ‘yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata…….”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
“Wallahi bazan je ofishin ‘yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba”.
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button