ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun daga nesa ta hango Uncle yana rubutu akan allo, wani irin dadi da farin ciki suka ziyarci zuciyarta. Ji ta yi tamkar Baba da Innanta ne suka dawo.
Daga can mazauninsu Nabilah ta hango ta, ta kuwa sheko da gudu ta rungume ta, ba tare da la’akari da cewa akwai malami a cikin ajinsu ba. Ya dakatar da rubutun ya juyo, juyowar da ta ke nufin al’amura da dama a gare su a wannan ranar.
Mairo ba ta iya ta hada ido da Uncle ba saboda matsanancin kwarjinin da ya yi mata a yau, shi kuma kokari yake ya kalli cikin kwayar idanunta cike da tuhuma da tarin laifuffukanta gareshi. Ya mannawa Nabilah harara ba shiri ta koma cikin nutsuwarta, kai tsaye Mairo ta wuce wurin zamansu shi kuma ya cigaba da bada darasi cikin wani sabon kuzari da nishadi gami da wani karfin gwiwa da ya same shi duk a lokaci daya.
Aka fita break amma ita da Nabilah ba su fita ba, sun nutsa hirar bayan rabo. Nabilah ta ce “Yaya Inna? Kusan kullum sai na yi mafarkinku Mairo, tun bayan rasuwar Baba nake jin tausayin Inna, ina gayawa Mamana da Daddy. Dama idan kika yi sati baki dawo makaranta ba zan bi sawunki ko makaranta ta yi min izini ko ba ta yi ba”.
Idanun Mairo suka kawo kwallah, ta ce “Innar ma na rasata Nabilah … Ba ni da kowa a yanzu sai Baffana sai Allah da Ya halicce ni. Na zama marainiya Nabilah, ba uwa ba uba…….”Hawaye suka kece mata, ta dukar da kanta cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka.
Nabilah ma sai ta sa kuka, tana tuna Inna da kirkin da ta yi mata. Sun dauki mintuna suna kuka, kamar wasu kananan yara. Ba su san yaushe Uncle ya shigo ba, har ya tsaya a kansu. Ya sanya hannu ya kwankwasa desk din da suke sunkuye. Duk hirarrakin da suke yi ya ji su, ya rasa inda zai sa kansa da tausayin Mairo. Ba kankanin abu ne ke sanya Junaidu kuka ba, amma a yau ya ce Maryama I cannot control my tears………..”Suka dago ido suka dube shi cikin ido, Mairo da Junaid ke kallon juna, irin kallon da ba su taba yi a rayuwarsu ba. Wani muhimmin al’amari na samun muhalli cikin kwayar idanunsu. Nabilah sai ta bude baki, galala! Tana kallonsu, tana cewa cikin ranta “A yau dai, dole Mairo ta yarda Uncle Junaid yana sonta……..”.
Mairo kwana ta yi ba ta yi barci ba, baya ga dacin mutuwar iyayenta da ya dawo mata sabo fil, sai kuma SOYAYYAR Junaid da ke dawainiyya da zuciyarta, amma ta kasa ganewa, sabida kuruciya da wauta. Ga dai zahiri al’amarin ya sauya, amma ta sanya kafa tana takewa da gan-gan.
A ganinta mai Junaid zai ci da ‘yar kauye kamarta? Sai dai ta ce zuciyarta na yaudararta, tunda shi din bai furta ba. To ita ma ba zata taba yarda da tunaninta ba.
Shirye-shiryen jarrabawar fita ya kankama. A wannan dan tsukin Uncle ya takura musu matuka da karatu, musamman akan lissafi (mathematics) da Ingilishi (English). Burinsa kawai Mairo ta lashe dukkan takardunta. Ta gama makaranta with flying colours’, ta samu gurbi a babbar makaranta, ta yi karatun da zata dogara da kanta cikin kowanne hali. Idan hakan ta faru to shi kam Alhamdu lillahi… Ya sauke nauyin alkawarin da ya daukar wa Malam Bedi, sannan ne yake jin zai fallasa mata soyayyar shi, don haka wannan ba lokaci ne da ya dace ya fallasa asirtacciyar soyayyarsa ga Mairo ba. Ya manta masu iya magana sun ce “A BARI YA HUCE… Shi ke kawo da rabon wani.
Ba ta da abin da zata ce da Uncle Junaidu sai godiya, domin da taimakonshi da kwarin gwiwar da ta ke samu daga gare shi ne ta zana jarrabawar Jamb, Waec da Neco cikin kwanciyar hankali, tamkar ba jarrabawa ta zana ba, sabida yadda komi ya zo mata da sauki. Sai dai kuma wannan gama jarrabawar na nufin al’amura da dama cikin rayuwarta. Rabuwa da UNCLE JUNAIDU? Wani muhimmin al’amari ne da ke cinta a zuci, da zuciyar ba zata iya jurewa ba, da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Ina ma Uncle zai ce yana sonta ya aure ta? Ya rabata da rayuwar maraicin da zata je ta fada a gidan Baffanta?
Hawaye suka ciko idanunta. A karo na farko da zuciyarta ta kawo shawarar ta nemi Uncle ta roke shi ya aureta, ya tserar da ita daga rayuwar kunci da zata je ta fada, ko da ba ya sonta.

Ta shiga neman Uncle cikin makaranta, lungu-lungu, sako-sako, abun kamar wasa ko mai kama da Uncle babu. Tuni dalibai sun soma tafiya, don duk wacce ta fito daga last paper daukar kayanta ta ke ta tafi, bayan anyi sallama da kawaye da abokan arziki. Tana tsaye nan cikin tashin hankali Nabilah ta iskota,
“Ga can Baffanki ya zo daukarki yana ta aike a nemo mishi ke”.
Hankalinta ya kara tashi da ta tabbatar a yau zata tafi ne, tafiya ta har abada daga Minjibir, ba tare da ta yi sallama da Uncle ba, wani mutum daga cikin mutane biyu da ke ba ta farin ciki da buri (hope) a cikin rayuwarta.
Tabbas yau ya sauke nauyin alkawarin da ya yiwa mahaifinta. Ta kammala makaranta cike da kyakkyawan zaton samun nasara. Muhimmin al’amarin da ke dawainiya da zuciyarta akan Uncle, ta ke so ta sauke, amma babu Uncle a cikin Minjibir, babu alamarsa.

Sai ta sa fuskarta cikin tafukanta ta soma shesshekar kuka. Nabilah ta rungume ta suka ci gaba da kukan tare, sai dai ita Nabilah ba ta san hakikanin dalilin kukan Mairo ba.
Ita kuka ta ke na kewa da rabuwa da Maironta, yayin da Mairo ke kuka na tausayawa rayuwarta. Ta kullaci Uncle mummunar kullata, (irin kullatar data yiwa Habibu) ta tuhume shi da YAUDARA da wasa da rayuwarta. Ba tasan inda za ta ganshi ba, ta gaya mishi shi kadai zuciya da ruhinta ke so. Ya taimake ta ya aure ta koda BA YA SONTA. Shi kadai ne namijin da ta ke jin zata iya aure a rayuwarta. Shi kadai ne ta ke jin zai kula da rayuwarta a bayan idon Baba da Inna. Shi kadai ne ta ke kalla ta ji shi kamar Yaya Habibu. Yau shekaru dai-dai har shidda dai-dai da rana daya zuciyarta ba ta taba hutawa da kaunarshi ba.
A da kam ba ta gane ba, amma yanzu ta yarda ta amince da mahaukaciyar soyayyar da ta ke yi wa Uncle Junaidu. A yau da ta yanke shawarar fada masa don su tallafi rayuwar juna ta neme shi ta rasa.


K
arfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta litinin suka iso gida, inda direban su Nabilah da ke biye da su don ya ga gidan ya juya da Nabilah, da alkawarin bayan sati zata zo su je da Mairo gidansu, don ba ta taba zuwa ba.
Tun daga soro Mairo ta soma cin karo da kwanuka, da busasshiyar miyar kuka a jiki. Gabanta ya ci gaba da faduwa don ta tabbatar ita da rayuwar farin ciki, sun yi hannun riga ke nan. Ta fado cikin wata sabuwar rayuwa ta MARAICI, wadda Innarta ta ke jiye mata. Ta tabbata Inna tasan rashin kirki na matan Alhaji Abbas shi yasa a lokacin rayuwarta ta ki yarda ta zauna da su. Mai za a yi da hali irin na Hajara da Habiba? Sai Allah Ya kyauta.
Karatu dai an kare shi, yanzu zama ne za a yi na din-din-din. Kowacce waina za a toya? To bari mu bi Mairo da iyayen rikon nata mu gani.
Habiba na daki lokacin da suka shiga, sai Hajara ce a tsakar gida tana tankaden garin tuwo. Baffa ne a gaba rike da jakar mairo, ita kuma ta biyo bayansa rike da wata jakar.
Hajara ta amsa musu sallama fuskarta ba yabo ba fallasa. Bayan haka ba ta kara tofawa ba. Baffa cike da takaici ya ce “Hajara baki ga ‘yar taki ba ne, ko sannu da zuwa babu? Ai ba a haka”.
Ta cira kai ta jefe shi da harara, “Cewa za ka yi tashi ki yi tsalle ‘yar gaban goshina ta dawo, ba sannu da zuwa ba”.
Jin cece-kucensu sai Habiba ta leko. Ita kam tayi fara’a ta ce “Ah! ‘Yan makaranta an dawo? Lale-lale”. Ko ba komai ta samu jakar da zata yi ta yi mata bauta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button