ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce “Gaida mahaifiyarsa kamar yadda yake gaida naki”. Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce “Galadanchi”. Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce “Don Allah Yayana tambaya nake”.
Ya ce “Allah Ya sa na sani kanwata”.
Ta ce “Gidan su Junaid nake tambaya”.
Ya ce “Junaid? Ya ya sunan maigidan?”
“Gaskiya ban sani ba”.
“Babba ne ko yaro ne?”
“Babba ne, don zai girme ka”.
Ya yi dan tunani “Kwatanta min shi”.
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce “Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?”
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar Kano. Ta ce “Ina jin nan ne”.
Ya ce “Mu je na nuna miki”.
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan ‘yan bokon da, mai malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al’ajabi, sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya ba. Ko’ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana sallama.
Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta amsa, ta ce “Yammata wa kike nema?”
Ta ce “Babar su Ilham”.
Ta bude mata kofar falon, ta ce “Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu”.
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon, gauraye da ni’imtaccen sanyin na’urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa.
Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama, yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace ce ma’abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne (medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba.
Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce, “Yammata daga ina? Ban gane ki ba”.
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce “Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki. Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba”.
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya (kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta “Yammata daga ina kike ban gane ki ba?”
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce “Na zo wurin Ilham ne”.
Ta ce “Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki”.
Ta ce “Eh”. A takaice.
Ta ce “To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu”.
Mairo ta ce “Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba”.
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo “dan jiraye ni ina zuwa”.
Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata. Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode ne, to a’a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce “Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?”
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska, cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce “Na gode”.

Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke damun wannan yarinya, ta ce “Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya mata”.
Mairo ta ce
“Ki ce mata Maryam ce”.
“Maryam-Maryam!” Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba.
Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani.
Sai ana kiran isha’i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi, zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce “Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?”
Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace “Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba”.
Ya ce “Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan”.
Ta ce “To”.
Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, “Kai wannan yarinya da kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi”.
Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce “Ka je Baffa na kira”.
Ya ce “In an ki fa?”
Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce “Mama Na dawo, sannunku da aiki”.
Lawan ya ce “Wani feleke wai ‘Baffa’, mu ‘Baba’ mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?”
Habiba ta ce “Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo? Miko nan in gani”.
Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da ita.
Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba ta wuce daki cike da takaici.
Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki. Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa.
Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce
“Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya”.
Sai Mairon ta ce “Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki”.
Ta ce “Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki”.
Mairo ta ce “A’ah, ba za a yi haka da ni ba”.
Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce “Bana so ku dinga jerawa ne kada a ga muninki”.
Ladidin ta kyabe baki, ta ce “Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?”
Habiba ta ce “Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba”.
Ladidi ta ce “Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana sallama da ita?”
Ta ce “Haka kuwa, ku je sai kun dawo”.
Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka kirasu
7/30/21, 10:24 PM – Kawata: 98
Likitan yana rubuce-rubuce a file lokacin da suka shiga, Mairo ta tsaya ta harde hannuwa a kirji a bakin kofa. Ladidi ta karasa ta zauna a kujerar da marasa lafiya suke zama. Ya gama ya dube ta ta karkashin gilashinsa ya ce “Me ke damunki?”
Ta ce “Ina fama da haraswa, zazzabi da ciwon kai mai tsanani, ga wani yawu da yake taruwar min a baki, bana jin dadin bakina”.
Likitan ya dau abin awonsu ya sanya a hannunta yana sauraro, sannan ya yi rubutu a wata ‘yar takarda ya ce, su je laboratory su kawo masa result. Suka fita suka tambayi lab aka nuna musu. Nan aka bai wa Ladidi robar fitsari aka ce ta je toilet ta yi ta kawo. Nan da nan result ya fito suka koma ofishin likita. Ita dai Mairo tunda ta ga an rubuta positibe hankalinta yai matukar tashi. Likitan ya dube su bayan ya duba takardar ya ce da Ladidi, “Ina mijinki?”
Ladidi ta ce “Ba ni da aure”.
Ya kura mata ido na ‘yan sakonni ya ce, “Amma you are pragnant,(kinada juna biyu) watanni biyu cif?”
Ladidi ta fiddo ‘yan idanunta gaba daya suka yi kuru-kuru, wannan bai damu likitan ba ya ci gaba da aikin da ke gabansa bayan ya rubuta mata magani a wata ‘yar takarda.
Suka fito jikin Mairo har rawa yake, saboda dimuwa da razana, ita kuwa Ladidi in banda kuka ba abin da ta ke, wai likitan sharri yai mata, duk girman kan nan ta sauke shi tana rokon Mairo wai su je wani asibitin a sake dubawa.
Mairo ta sa mata ido, ta ce “Wannan asibitin specialist ne, duk Kano daga Aminu Kano sai shi, hakikanin gaskiya suka gaya miki. Don haka ni babu inda zan kuma zuwa”.
Ta yi shiru hawaye na zubar mata. Ba tausayin Ladidi ta ke ji ba, tausayin Alhaji Abbas ne, bawan Allah, Baffa bai cancanci ‘ya’ya irin wadannan ba.
Sun kusa Yakasai Ladidi ta ce “Wallahi Mairo duk abin da kike so zan baki, ki rakani a zubar min da cikin, in Baba ya ji wallahi-wallahi kashe ni zai yi”.
Mairo ta ce
“Ni kuwa mai za ki ba ni Ladidi in rakaki a kashe rai? Tukunna ma ni ban san inda ake zubar da ciki ba. Kin bata wayonki! Amma bana tausayinki, Baffa nake tausayawa. Iyakacin tarbiyya da ilmi ya baku, daga boko har na Arabiyyah, ya tsare muku cinku da shanku, da suttura dai-dai karfinshi. Bai cancanci wannan sakayyar daga gare ku ba…..”
Ta kai gefen mayafinta ta share hawaye, ta fyace majina, ta ce “Ladidi ke kuwa mai ya kai ki ga yin haka? Idan aure kike so mai yasa ba ki tsayar da daya cikin tulin samarin naki kin aura ba? Mai za ki ce da Baffa ranar da ya gane kin yi cikin shege?”
Ladidi ta kufula wai Mairo ta ce ta yi cikin shege, ta ce “Kinga malama bana son wani dogon Turanci, idan ba zaki rakani ba ne mu raba hanya, wancan karon ma da aka ce na yi cikin ai nasan inda na je aka kwakule shi. Ko ance da ke kowa ma kidahumi ne, bakauye irinki? Mtsew!!!”
Ta yayyaga takardar likitan da takardar maganin, ta ce
“Ki je ki gayawa Baffan naki ya yi duk abin da zai yi kada ya barni da rai idan shi ne………..”
Mairo ta sanya ‘yan yatsu ta toshe kunnenta, ita kuma Ladidi ta tare dan A dai-daita sahu ta shige, ta ce, ya kai ta Sabon Gari.
Tana shigowa gida Habiba ta ce “Ina kika baro Ladidin?”
Ba tare da ta dubeta ba ta ce “Tana zuwa yanzu”. Ta shige dakinsu ta danno kofa. Ta rasa inda zata sa kanta da tausayin Baffa. Ta soma kuka kamar ita ce abin ya faru a kanta.
Wani sassanyan kamshi ya doki hancinta, irin wanda ba ta taba ji ba a rayuwarta. Daga nan ta jiyo muryar Baffa yana salati, yana sallamewa. Ta sake saurarawa sosai sai ta ji ya ce “HABIBU? Wa nake gani kamar Habibu?”
Tamkar wadda aka cakawa mashi. Ta ji wani kululun bakin ciki ya taso ya soketa a kahon zucci. Amma hakan bai hanata mikewa ta fito ba, don gasgata kunnuwanta.
Wani magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da takwas, wankan tarwada, mai zarkadeden dogon karan hanci da yalwar idanu farare kal. Da ganin fuskarshi ka ga Malam Bedi, ta wani fannin kuma Alhaji Abbas sak! Yana sanye da kaftan na shadda Getzner kar-kar da ita, baka wul! Dinkin tazarce, sumar kansa a kwance luf baka sidik, kasancewar ba hula a kansa. Da gani babu tambaya, ka ga mutum da ya dama, ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban. Wasu kyawawan yara guda uku, maza biyu da mace daya, sai rarraba ido suke na rashin sabo.
Mairo dai tana nan rike da labule tana kallonsu, wasu irin hawaye suka zubo mata, ta yi saurin sakin labulen ganin zai juyo sashen da ta ke. Tana ji su Hajara duk suka firfito suna ta karadi da sallallami, ita kuwa ba ta kara lekowa ba. Mai ya dawo da shi cikin rayuwarsu yanzun? Bayan masu bukatarshi sun shude a doron kasa? Mai zai ce, mai zai yi, ya wanke mugun tabon da ya yi mata a zuciyarta?
Mairo kuka ta ke tamkar ranta zai fita, ba ta son ganin Habibu ko kadan a rayuwarta. Gara ta bar gidan, kada ace da shi yana da ‘yar uwa, mai zai yi mata wanda ALLAH da UNCLE JUNAID ba su yi mata ba?
Ta soma harhada kayanta cikin jakarta da sauri-da-sauri, tana yi tana fyace hanci da hawaye duka. Ba ta ankara ba sai ji ta yi Baffa na kwala mata kira daga tsakar gida “Mairo! Mairo!! Ko Mairo ba ta nan ne?”
Ta yi bakam, ta ki amsawa, ta jawo hijabinta ta zurma ta sungumi akwatinta ta yo waje, suka ci karo da Baffa a bakin kofa.
Ya ce “Zo Mairo, yau ga Habibu Allah Ya dawo mana da shi”.
Ta sa kuka, ta ce “don Allah Baffa ka bani hanya in wuce, bana son ganinshi, ba abin da ya hada ni da shi. Idan dai zai zauna a gidan nan to ni zan koma wajen Nabilah”.
Baffa ya ce “Haba Mairo, waye ba ya kuskure? Ki dinga yi wa dan Adam uzuri cikin kowanne hali, uzuri sau saba’in, kafin ki kama shi da laifi. Ki saurare shi ki ji da wacce ya zo, sannan ki yanke mishi hukunci”.
Da haka ya lallabata suka nufi dakinshi, inda Habibu da su Habiba su ke.
Habibu ya hada kai da gwiwa sai kuka ya ke, kamar karamin yaro. Ba kuma kukan komai yake ba, sai kukan jin rasuwar iyayensa daga bakin Habiba. Baffa ya fada su da fada kamar ya rufe su da duka “Ke kam Habiba ba ki ji dadin halinki ba, ko ruwa ba ki barshi ya kurba ba zaki ce Uwa da Uba sun mutu, gatsar, babu sakayawa, babu nuni da daukan hakuri da YAKANAH (Sunan Littafin TAKORI mai zuwa). Ku tashi ku fita ku ba ni waje, iyayen banza, wadanda ban san yaushe za su san Annabi Ya faku ba”.
Sum-sum-sum suka mike suka fita. Habibu ya dago kai yana kallon Mairo. Kyakkyawar budurwa ‘yar shekara sha takwas, wadda ya tafi ya bari tana shekaru takwas. Ita ma ta kalle shi cikin ido, sai kuma ta dauke kanta. Ta daure fuska sosai. Ya ce “Mairo Yaya Habibun?” Sai ta fada jikinsa ta sa kukan da ke cinta a zucci.
Allah Ya riga ya halicci zuciyarta da kaunar Habibu, babu yadda zata yi, shi ne dolenta a rayuwa. Suka rungume juna suka yi ta kuka, Baffa ma tunanin dan uwansa ya dawo masa sabo. Ya soma share ido da habar babbar rigarsa.
Sai da suka yi kukansu mai isarsu, sannan Baffan ya soma lallashinsu. Ya ce “Ni ina nan Habibu, zan zame muku uwa, uba, kuma abokin shawara. Dukkaninmu na haka ne, kowa jiran wa’adinsa ya ke”.
Habibu ya ce “Kaicona Baffa! Dukiyar da na zauna ina tarawa don Baba ya daina noma, Inna ta daina girki da icce, Mairo ta yi karatu mai kyau sun tashi a banza!
Na kintata ne zuwa sanda zata gama sakandire sannan in dawo, ashe bazan tadda Baba da Inna ba, sannan Mairon ba ta ji dadin dawowata ba!!”
Baffa ya ce “Wai haka Mairo? Ba ki ji dadin dawowarsa ba in sallame shi?”
Ta yi murmushi, ta sake sunne kanta a kirjin Yaya Habibun. Ya ja karan hancinta, ya ce “Ko kallon ‘ya’yanki ba ki yi ba, balle mai sunanki, mai kama da ke”.
Sai a lokacin hankalinta ya koma ga yaran. Cikin murmushin kaunarsu da ta mamaye zuciyarta farat daya, ta ce “Ya’yanka ne Yaya Habibu?”
Ya gyada mata kai, “Ya’yana ne. Na yi aure da mamarsu tun sanda na kammala karatun digiri na farko. Ga Abbas, ga Muhammad (Bedi), sannan ga Mairo”.
Baffa ya yi murmushi, ya ce “Taho takwarana”.
Abbas ya matsa gare shi, dan kimanin shekaru hudu, Muhammad shidda, Mairo kuma ‘yar shekara biyu ce.
Babban wato Muhammad ya ce “Daddy wannan ne Babanka?”
Ya ce “Eh, shi ne Babana”.
Ya kuma cewa, “Wannan ce Aunty Mairo?”
Ya ce “Eh ita ce Aunty Mairo”.
Ya matso jikin Mairo ya jingina da kafadunta, ita kuma sai kokarin daukar takwararta ta ke, amma ta ki, ta like jikin babanta. Ya ce “Ai ita kiwar tsiya gare ta, wanda yake kulaki ba ki kula shi ba”.
Ta yi murmushi ta ce “Abbana, Muhammad”.
Ya yi murmushi ya ce “Anti Mairo za ki je gidanmu?”
Ta ce “Insha Allahu”.
“Za ki yi min tatsuniyya ta gizo da koki irin wadda Daddy ke mana?”
Ta ce “A’ah, ni ban iya tatsuniya ba, ni sai dai na karanta maka labarin jaruman maza, irin su Ilya dan mai karfi, da Malukussaif Ibn Ziyyazanun”.
Ya yi dariya ya ce “Ni kuma zan tuka ki a jirgina (helcopter) wanda Daddy ya sayo min”.
Ta rungume shi ta ce “To Abbana”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button