ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Amiru ya baro kujerarshi ya iso inda Daddyn ya ke ya zauna a gefensa suka soma hirarsu. Ta mike ta je kicin ta kawo mishi ruwan (Eva) mai sanyi da lemun ‘shany’ sannan ta gabatar mishi da abinci.
A nan ne ya yi murmushi, ya ce
“Lemun kadai zan sha Maryamu, na Hajiyarku yana can yana jirana, kada inci a wajenki inje in kasa cin nata”.
Ta yi murmushi ta ce
“To Daddy babu komai”.
Ta koma daki ta barsu don su gana.

Yau ma irin kwanciyar jiya suka maimaita, wato shi yana bisa kilishi ita tan kan gado. To haka kwanakin da suka biyo baya. Idan ka gansu a gaban Hajiya da Daddy. ko su Amina, ba zaka taba zaton cewa zaman ‘yan Marina suke ba. Kowanne na ji da miskilancinsa ya kasa kwantar da kai ga dan uwanshi. Ga ita Mairo, a ganinta shi ne namiji, shi ya kamata ya nuna mata kulawa irin ta kowadanne ma’aurata amma ba ita ba. Sannan ba haka Dina ta gaya mata ana yiwa amare a renakun su na farko a gidan aure ba. Ba haka kuma ta ga Yaya Habibu yana yiwa Dinan ba. Amiru yace yana son ta baka da zuci, amma bayan aurensu ta ga ba haka ba. Wannan al’amari yana sanya ta cikin wani irin tunani mai zurfi da wuyar fassarawa. Har ta kasa jin dadin rayuwar gabadaya.
Shi kuma Amirun, a nashi bangaren, ya riga ya saba samun tarairaya ta karshe daga banasariyar matarshi, kamar ta goya shi. Bai san cewa matar Bahaushe da matar bature akwai wasu manya-manyan banbance-banbance ba. Hakika mu Allah Ya ba mu wannan darajar ta kamun kai da alkunya, wanda ya zamo kowanne irin namiji, duk kyau, aji, mukaminsa da iliminsa dole ya lallame mu idan har yana son ganin yadda ya ke so.
Yau juma’a ta tashi da kewar Dina kwarai a ranta, ba abin da ta ke so irin ta ji muryarta. Ya dawo daga sallar juma’a shi da Daddy daga babban masallacin Abuja kamar yadda suka saba kowanne sati idan suna nan. Ta rasa yadda zata yi ta roke shi ya ba ta aron waya. Dabara ta fado mata don haka ta nemo biro da ‘yar takarda ta rubuta mishi, ta soke a jikin kofar dakin da ta tabbata shi ne nasa.
Ya zo shiga dakin don sauya manyan kayan da ke jikinsa ya cimma sakonta. Ya yi murmushi ya sumbaci takardar ya share ta bai ce mata komai ba.
Sai da daddare sun yi shirin kwanciya, bayan ya jefa filonshi ya mike. Ta zuba tagumi a gefen gado abin duniya ya dame ta, idan jurinta miskilanci ta gamu da wanda ya fi ta miskilanci. Ta juyo kadan, ga dukkan alamu barci mai nauyi ya tafi da shi. Cikin sanda kamar barauniya ta iso gabanshi don ta dauki daya daga cikin wayoyinshi sai caraf! Ya damke hannunta tareda wayar ya kuma bude lumsassun idanunshi sannu a hankali a kanta.
Kunya ta duniya Mairo ta gama jinta. Ashe ba a yi komai ba sai sanda ya fizgota ta fada gaba daya a jikinshi. Ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, fargaba da wani bakon tsoro da ya ziyarce ta duk a lokaci guda.
Jikinta ya soma rawa kamar mazari, amma hakan bai sa ya cikata daga sassaukan rikon da ya yi mata ba. Duk yadda ya so da su hada ido cikin dan sauran hasken fitilar baccin dake dakin amma Mairo ta ki. Runtse idon ta shiga yi da karfi. Wani sabon Son mijinta AMIRU da kaunarsa ne farat daya suke tsirgawa a zuciyarta. Wadanda bazata iya tantance tun tsahon wane lokaci hakan ya soma ginuwa a zuciyarta ba. Yana danne wancan feeling din mai karfi da dukkan tasirin sa, wanda zuciyarta ta dade tana kallon Amiru dasu. Tareda gina mafarkanta da shi a kansa.
Ya dago fuskarta daga kirjinsa, a wannan lokacin ya yi nasarar hango cikin kwayar idanunta, cikin murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya ce
“Sata ko Mairo?”
Ta ce
“A’a, ina so in kira Anti Dina ne, kuma na fada maka ai ba ka ba ni ba”.
Ya ce
“Ni ban kai kararki wajen Anti Dinan ba, sai ke za ki kai karata?”
Kamshin ‘mouth fresh’ dinshi na fizgarta, yana sanya mata rashin kuzari ta ce,
“Me ka yi min da zan kai kararka, kuma nima me na yi maka da zaka kai karata?”
Ya ce,
“Kin yi min laifuffuka da yawa Mairo, wadanda idan na fadawa Anti Dina sai ta zane ki wallahi”.
“Dame-dame ne laifuffukan nawa?”
“Ai ba ki ma sansu ba?”
“Da na sani bazan tambaye ka ba”.
“To sunkuyo nan na fada miki”.

“Kinga na farko ba kya gaishe ni da safe, sannan ba kya zuwa dakina taya ni kwana, sai dai ni na biyo ki dakinki. Sannan idan na biyo ki ba kya hada makwanci da ni, sai ki bar ni a kasa ki dare gadonki. Haka Dinan ta fada miki tana yi wa Habibu? Ko ba ki ga har kaya ita ta ke saka mishi ba? Amma ke bana jin ko inda nake wanka kin sani a gidan nan ko don har yanzu ba kya sona?”
Taji zafi a ranta da kalamansa. Da zai taimake ta da ya daina zancen rashin so a tsakaninsu. Ta ce
“Maganar ina sonka ko bana sonka, tunda mun riga mun kasance cikin inuwar AURE, to bata taso ba, bare kuma ni wallahi ban taba jin kiyayyarka a raina ba. Ko wancan lokacin da na fada, na fada ne kawai don ban amince da irin son da zuciyata ta ke yi maka ba”.
Ya lumshe ido a hankali, tare da sake yi mata muhalli cikin ni’imtaccen kirjinshi mai cike da gargasa.
Yace “wane iri ne shi wancan son?” Ta dan rufe ido kafin tace “irin na shirme!”.
“Wane irin so ne irin na shirme?”
Amiru ya tambaya cikin mamaki.
Mutsu-mutsun kwacewa ta hau yi, ko zai kashe ta bazata iya yi masa wannan bayanin ba.
Sako riko ta yayi da karfin da yafi na dazu, ya juyo ta sannan ya sa hannu ya dago habarta. Yana iya ganin kyallin dake cikin idanunta wadanda ke cike taf! Da soyayyar data mamaye su. Soyayya mai cike da kauna mara algus or material attachement. Zaiyi rantsuwa bai taba ganin wannan yanayin cikin kwayar idanunta ba, wani yanayi da yake matukar jira, yake kuma da yakinin zai iya cigaba da jiran zuwansa cikin idanun Mairo har nan gaba da shekaru goma kafin ya yarda ya hada shimfida da ita.
“To yanzu fa? Mairo! Mairo yanzun kina sona?”
Amiru ya tambaya, da wata murya tamkar ba tashi ba.
Sai ta yi murmushi, irin wanda bai taba gani bisa siraran labbanta ba.

Wannan kadai ya tabbatar mishi da cewa, ya gama mallakar soyayyar Mairon, saura da me? A take shi ma ya soma mallaka mata ta shi. Cikin wani irin salo mai ban mamaki da Mairo ba ta taba tunanin akwai irin wannan soyayyar a duniya ba. Koda a duniyar karance-karancen novels dinta kuwa.
Su Hajiya Mairo, tun ana dauriya, ana cijewa, cikin bin shawarwarin uwardakin ta Dina, har lissafin ya soma kwace mata……aka kai ga gejin kiran Anti Dinah, Baffa, da Yaya Habibu su zo su kawo taimako. Yau har Ladidi da Nabilah sun sha kira don tana ganin karshen rayuwarta yazo! Shi kanshi Amirun ya rasa control din kansa, ta yadda har zai yi tunanin cewa Mairon virgin ce, ba kamar matarshi ba. Tunda yake a rayuwarsa bai san akwai Hurul-eeni tun a duniya ba. Bai san aure iri-iri ne kuma suna ya tara ba. Don haka bai farga da aika-aikar da ya yi ba, sai da ya duba ya ga Mairon ta sume mishi.
Ba ita ta dawo hayyacinta ba sai da sanyin ruwan ‘ragolis’ ya ratsa kwanyarta, da sauran sassan jikinta. Ya rungume ta sosai, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, cikin shauki ya ce
“Mairo kar ki gudu ki barni! Mairo ki ci gaba da zama da ni ko ba kya sona, ni ina sonki da dukkan ruhi na! Ki rike naki son ko bazaki bani ba! Zan zamo ‘impotent’ a duk ranar da kika guje ni, ko kika juya min baya…!”


MAIRO A GIDAN AURENTA!

Zuwa yanzu, wato watanni biyu a gaba, Mairo an zama manyan mata, an iya komai na kula da miji. Ta iya daukewa mijinta lalurar da mata hudu ba zasu iya dauke masa ba. Soyayya, kauna da shakuwa ke kara kamari tsakaninta da mijinta. Ga kauna da kulawa da ta ke samu daga surukanta kamar su suka tsugunna suka haife ta.
Cikin wannan dan tsukin Amirun ba ya samun zama sosai, sabida shirye-shiryen bude bankinsu da suke yi shi da Habibu. Shi Habibun ke tafiyar musu da komi ta can, shi kuma yake tafiyar da komi ta nan.
Gaba daya ya mance da wata Harrit da ya sanya lambarta a (divert call), sannan a ka’idarshi bai daukar wayar da bai san lambar ba. Al’amuran gabanshi kadai sun ishe shi, sannan Mairon shi kadai ya sanya a gaba, a yadda yake ji cikin ransa, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button