ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

A yau ne Hajiya ta yi kiranshi don jin inda suka kwana. Ta tsare shi da dara-daran idanunta, kafarta daya akan daya cikin luntsumemiyar kujerar falonta. Ta ce.
“To yaya, kai nake saurare?”
Ya ce, “Maganar tafiya karatu ai an barta Hajiya, tunda ba kya so”.
Ta mika mishi hannu, ta ce.
“To ba ni takardun”.
Ya yi wuki-wuki da ido, can ya ce.
“Habibun ne ba ya nan, idan ya dawo za mu zauna a ware a kawo miki……..”.
Sai hawaye sharr-sharr wasu na korar wasu, domin gani yake Hajiya ta gama tozarta shi, a duk ranar da ya doshi Habibun da wannan zancen. Domin Habibun zai yi zargin abubuwa da dama, ciki kuwa har da tunanin ko Amirun na zarginshi da cin amana ne, ba zai taba kawowa ranshi Hajiya ce ta sa shi ba sabida yadda ta dauke shi kamar dan cikinta, shi ma yake daraajjata kamar mahaifiyarsa.
Hajiya ta kama baki, tana cewa.
“Yanzu sabida ina so na rabaka da abin da zai cuce ka, shi ne za ka sanya ni a gaba kana yi min kuka?”
Ya dago sosai yana dubanta da idanunshi da suka kada suka yi jawur. Muryarshi abin tausayi ya ce.
“Hajiya, Habibun ne zai cuce ni?”
Ta girgiza kai.
“A’ah, ba zai cuce ka ba. Ni uwarka ni ce zan cuce ka. Habibu sai ya je kauye ya biya malamansa. Tashi ka je, na yafewa Habibu da kanwarshi Mairo kai, idan har ba zaka kawo min takardun komi na dukiyarka ba. Kuma zan maka Habibu a kotu sai ya ba ni dukiyar da na!”
Zuciyarshi ta bushe da etsoro da al’ajabi. Ya ce, “Hajiya me ya yi zafi da za ki kai Habibu kotu? Ki kara min alfarmar kwana biyu. Na yi alkawarin zan cika umarninki ko da hakan shi ne aiki na karshe da zan gabatar a rayuwata”.
Fitowa ya yi zuciyarshi na suya, ya zaburi mota bai tsaya a ko’ina ba sai a kofar gidan Habibu.
A lokacin Habibu na shirin shiga mota zai fita, shi kuma yana danno hancin motarsa (Camero, 2 door) cikin ‘gate’ din Habibun. Don haka ya fasa shiga motar ya jirashi har ya karaso ya fito daga motar.ŕ
Ba karamin faduwar gaba ce ta samu Habibun ba ganin irin halin da aminin nashi ke ciki. Suka rankaya suka koma cikin gidan. Dina ba ta nan, ta je Malaysia ita da yara, duba jikin mahaifinta da ba shi da lafiya.
Habibu ya isa ga firij, ya dauko mishi gwangwanin ‘coke’ ya bincire hancin ya mika mishi ba tare da sun gaisa ba. Ya karba ya yi kurba daya, amma ya kasa wucewa a makoshinsa. Dole ya furzar da na bakinshi idanunshi sun kara kadawa sun hargitse.
Habibu ya zauna a gefenshi, ya ce
“Be a man, plz! idan kana raye ba abin da ba zaka gani ba”.
Ya rausayar da kai cikin amincewa da kalaman Habibun. Ya ce
“Alfarmarka nake nema, sai dai bana son ka tambaye ni dalilina, na yin hakan”.
“Ba zan tambaye ka ba Amiru. Fada min komi tsaurinta”.
“So nake na janye komi nawa daga cikin ‘Habib Bank!!”.
Habibu ya yi shiru, domin Amiru ke da kaso 60% wanda hakan ke nufin durkushewar bankin da ya faro da nasara cikin shekaru biyu kacal da kafuwarshi, wanda ke nufin shi kadai (Habibun) ba zai iya ‘running’ bankin ba.
Ya tabbatar makiya sun shigo cikin al’amarinsu, amma bai ga laèèifin Amirun ba, wanda da gani kasan tursasa zuciyarshi yakeyi, wajen furta kalaminshi.
Ya ce “Idan don wannan ne, ai babu damuwa Amiru. Idan har hakan zai samar maka kwanciyar hankali, ka ba ni kwana goma, insha Allahu komai naka zai dawo hannunka. Sai dai ina so ka samu lauya, wani daban, ba Dina lauyar bankinmu ba”.
Ya ce
“Ni ba ni da wani lauya”.
Habibu ya ce
“Dole sai ka nemo”.
Ya juyar da kai yana kwararar da hawaye, ya ce
“Daga yau ba zan kara neman kudi ba, tunda su din fitina ne. Ta yadda har wasu suke ganin su din (kudi) sun fi mutumci da amana, Ya Allah Ka tsiyata ni………..”
A gaggauce Habibu ya toshe masa baki.
“Kana hauka ne?
Kada ‘frustration’ (bacin rai) ya sanyaka fita daga imaninka. Ka je ka samo lauya, mu yi abin da zai kwantar maka da hankali”.
“Ni na ce da kai hakan kwanciyar hankalina ne?”
“Ba ka ce ba, don haka abar kazar cikin gashinta ba sai an fiffigeta ba”.
Cikin satin Habibu, tare da taimakon Barrister Dalha wani abokin aikin Dina daya daga cikin lauyoyin ‘CBN’ da Barrister Mujahid lauyan ‘starling’ sun hattama komi na dukiyar Amiru, ta koma hannunshi da sunanshi da sanya hannunshi.
Ya kwashi takardu cikin ‘briefcase’ ya yi sallama a dakin Hajiya. Kallo daya ta yi mishi ta ga yadda ya zabge, ya yi zuru-zuru sai karan hancin da idandanun kadai, amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, da dai ta kyale Habibu da kanwarshi su yi galaba a kanta. Tunda sanda ta ke nakudar abinta bayan rainonshi cikin mahaifarta, har wata tara da dawainiyarshi zuwa girmanshi, ai ba su zo sun tayata ba.
Don haka ta kudure sun daina cin arzikin Amiru, kowa ya ci gashin kansa.
Ya zauna a kujerar da ke fuskantarta, kwakwalwarshi na juyawa. Ya mika mata ‘briefcase’ ba tare da ya iya hada ido da ita ba.
Ta bude ta zaro takardun ciki ta sanya ‘medicated glass’ dinta tana dubawa daya bayan daya. Ita kanta ta razana da ganin abin da Amirun ya mallaka a ‘yan kananan shekarunshi.
Bayan ta gamsu da ingancinsu, ta maida su inda suke tana murmushi, ta ce.
“To ko kai fa?
Ba ga shi ba yanzu sai yasan zafin nema ba ya tashi daga cima-zaune? Yanzu wane kasuwanci zaka soma da wadannan din?”
Ya kalle ta kawai bai yi magana ba. Ta dauka bai ji ba ne, don haka ta sake maimaitawa.
Ya ce ba tareda ya dubeta ba,
“Sadakar da su zan yi”.
“Au fushi ka yi, sabida ina yi maka gata Amiru?”
Ya ce
“Ya ya za a yi na yi fushi da ke Hajiya? Ina juya su, kin ce in kawo miki. Na kawo miki kuma ki ce me zan yi da su?
Ban iya wani kasuwanci ba, bayan wanda nakeyi, ni ma’aikaci ne. Aikin banki shi ne wanda na iya tsawon shekaru goma.
A yau kin ce na barshi, don kada Habibu ya samu dan wani abu a jikina, wanda bai taka kara ya karya ba. Bayan kin san duniyar cudarni in cudeka ce, kuma shi ma ba matsiyaci ba ne, yana da rufin asirinshi wanda da kadan ne bai kai nawa ba.
Haba Hajiya! Shekarata nawa da Habibu bai cuce nin ba sai yanzu da muka zama daya?”
Hajiya ta ce
“Rabi (half) kuka zama ba daya ba, sallamamme, bawan mace. Tunda ba ka so ka yi zuciya har kana cewa sadakarwa zaka yi, ni ina so, zan yi maka sadakar, amma ba duk ba. Ranar da tsiya ta isheka ka waiwaye su, nima ina da ‘account’ din da zan adana maka su su hayayyafa ba Habibu ne kadai ya iya juya sisi ya koma kwabo ba”.
Duk abin nan da ake Daddy bai sani ba, don shi ba mazauni ba ne, sannan ko da wasa Hajiya ba ta yi gigin sanar da shi abin da ta yi ba, don tasan bazai goyi bayanta ba. Sai su Khalisa da Nina wadda ke aure a Lagos sune ‘yan abi yarima a sha kida, duk suka yi ta tsalle.
Nina ta ce
“Mun gama da wannan, saura ‘yar kauyen Gurin-Gawa, don Allah Hajiyarmu ki yi mana waje-road da ita”.
Hajiya ta ce
“Ku barni da su, duk na ishe su, ko ba ta yi waje ba, ai ta yi zaman boranci idan na aura mishi wadda zata cika min gida da ‘ya’ya”.
*÷
8/6/21, 5:15 PM – Kawata: F
An debi watanni biyu kwarara, Hajiya na tarairayar danta don dai ta wanke dattin ta dake idanunshi, tana kuma nuna kulawarta akan Mairo, wadda ita kuma ba ta san tana yi ba, karatunta kawai ta sa a gaba.
An yi bikin su Sabah tun shekarar da ta gabata, bayan sun kare karatunsu. Don haka yanzu sassan Hajiya babu kowa, daga ita sai ‘yan aiki. Watakila hakan ne ya sa ta kwallafa ranta ga son ganin ‘ya’yan Amirun, tunda sauran jikokinta iyayensu maza ba za su ba ta ba.