ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Malam Bedi ya ce, “Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya zo gaishe ki? Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne majibincin al’amarin ta nan gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata ranar da babu mu, wane ne zai shiga?
Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya daina cewa ‘yar ki ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar mu rasa jam’i”.
Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa, “Yaya Habibu ni ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba”.
Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, “To mu je, amma sai ki tsaya a wajen masallacin daga gindin bishiya kina bin jam’in, don mata ba sa zuwa masallacin maza”.
Ta ce “To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi yake dora ni, kai kuwa ka ma fishi tsawo”.
Ya kama baki, “Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?”
Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce
“Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto ta fado tim! Ta karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar ‘yar Birrai nake. Bana fadowa, sai dai in ciko bujena da goba da tsamiya………”
Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to ita me ye laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi.

Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da malamai ta Kano, wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake ma abin da ya kawo shi Gurin-Gawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa.

Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da Habibu da hidimar karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga makaranta da ranakun karshen mako.
Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu da ‘ya’ya bila adadin maza da mata. Saidai ‘ya’yanshi kanana ne da ake haifa akan idon Habibu. Cikinsu duka babu mai shekaru goma. Babbar diyarshi Ladidi sa’ar mairo ce. Don haka Habibu tamkar wani jigo ne ga iyalin Alh. Abbas wanda duk suke kauna sabida zumuncinsa da rikon amana.
A rayuwar Alh. Abbas bai taba ganin yaro mai kwazon neman na kai da amana irin Habibu ba. Tunda ya ke tare da shi, kwandala wannan bata taba bata cikin lissafinsa ba, kimanin shekaru ashirin ke nan. Watau tun Habibun yana dan shekara biyar. Wannan ne dalilin da ya sa ya maida Habibu dan cikinsa ba Dan dan uwansa ba.
Taimako dai-dai gwargwado Alh. Abbas na yi ma yayan shi Malam Bedi, kamar ta samar mai ingantaccen takin zamani, da taimaka mai da motocin noma a yayin girbi, wadanda yake dauko masa haya daga KNARDA.
Bayan wannan sallah da azumi shi ne sutturarsu, haka ta fannin abinci lokacin azumi, tun daga kan sukari, lipton, madara, da su taliya ba abin da ba ya taso Habibu ya kawo musu, sai dai idan suna nomansa a nan Gurin-Gawa.
Zumunci ne mai karfi a tsakaninsu, wanda iyayensu suka dora su a kai, har gida Alh. Abbas ya sayawa Mal. Bedi a Yakasai ya ce ya dawo su zauna tare, inda shi kuma ya ce shi da rabuwa da Gurin-Gawa sai dai mutuwarsa. Ko ita ba ya fatan a fitar da gawarsa daga Gurin-Gawa, su je can su tsinci abin da suke tsinta a birnin, shi kam a gareshi kwanciyar hankali shi ne komai.

To amma wannan zumunci na mazan ne banda matan. Babu shiri ko kadan tsakanin Inna Hure da matan Alh. Abbas wato Habiba da Hajara. Tun sanda daya daga cikinsu ta taba cewa a bata Mairo ta dinga taimaka mata hidimar ‘ya’yanta ta kulla gaba da su. Ta ce kuma wadda duk ta kara tako mata gida, Allah Ya isa. Ta rasa dalilin da ‘yar tata ta tsolewa kowa ido. Ba abin da ta ke so a rayuwarta irin ta budi ido ta ga Mairo na wasan ‘yar tsanarta a tsakar gida, suna harkokinsu gwanin ban sha’awa.
Don haka ne ko makarantar firamare da ake sa yara a kauyen taki yarda ta sakata, ita dai su zauna abinsu.
Sai da Mal. Bedi ya yi da gaske kamin Mairo ta dinga zuwa karatun allo a makwabtansu, daga takwas na safe zuwa sha biyun rana. Nan din ma ba wani abin arziki ta ke tabukawa ba da ya wuce tsokana, jan fada, surutu da guduwa idan Malam ya soma gyangyadi.
Abin da Mairon Hure ta kware akai shi ne hawa bishiya. Yadda kasan kadangaruwa koko Gorilla haka ta ke makalewa a jikin bishiya. kusufa-kusufa ta iya kurdawa ta tsinko abinda ranta ke so ta cika bujenta. Duk girman bishiya Mairo zata iya dafe ta, ko tsoron irin aljannun nan da ake ce suna zama a bishiyoyi ba ta yi. Ta tsinko musu su ci abinsu, ita da Innarta, wannan ya fi komai dadi ga Hure.
Mairo yarinya ce ‘yar kimanin shekaru takwas cif. Amma kaifin bakinta ya fi na dan shekaru ashirin. Kyau kam ba a magana, tsurarshi na Inna Hure, doguwa shafal-shafal da shafaffar mara gami da lafiyayyen kugu, wanda tun tana jaririya haka yake. Sumar kai yalwatacciya, yalo-yalo kamar ta hada jinsi da Larabawa. Sai dai fa dankare take da kwarkwata da amosani wanda ya bi ya cinye rabin gashin.
Wani aiki sai Hure Innar Mairo, don tunda Mairo kukan kitso ta ke, aka shafe yi mata kitso a doron kasa. Kai wata kila ma ta manta akwai suma akan Mairo, don kullum kulle ta ke tamau cikin wani bakin dankwali mai masifar dauda. Sai idan kwarkwatar ta ishe ta da cizo ne ta ke tube dankwalin ta samu gefe guda ta yi ta susa da hannu bibbiyu har sai jini ya bubbugo.

Wannan shi ne babban takaicin rayuwar Habibu, yana matukar bakin-ciki da tsarin rayuwar kanwarsa tilo, wadda kuma Allah Ya sanya masa matsananciyar kaunarta da tausayinta. Ta wani bangaren ba ya ganin laifin Inna Hure, domin haihuwar ce Allah Ya ba ta a tsufanta, bayan ta riga ta fidda rai da samunta.
Sannan yawan aiyukan gida da ke kanta ba zasu barta ta kula da irin wadannan kananun abubuwan game da yarinyar ba.
Duk ba wannan ya fi damunsa ba, kamar jahilcin Mairo. A ganinsa Mairo jahila za a kirata kai tsaye, ba arabi ba boko. A ganinsa da tana zuwa makaranta, wannan duk wani abu ne da ita kanta zata yi wa kanta nan gaba, ba tare da kowa ya sata ba.

Bayan sun fito masallacin ya duba inda ya ce Mairo ta tsaya ta yi sallah, ba ta ba alamunta, balle dardumar karauninta. Ya juya gabas da yamma, Kudu da Arewa babu Mairo. Ransa ya sosu, ya kira wata ‘yar yarinya mai tallan rogo, ya ce “Don Allah ko kinga Mairon Hure?”
Ta ce, “Na ganta ta mika kwanar gidan su”.
Ya ce, “To madallah. Ta yi gaba abunta dai-dai sanda Malam Bedi ya cimmasa da cazbaha a hannunsa ya ce, “Mai kake tambaya ne?”
Ya ce “Mairo mana, sama ko kasa na nemeta na rasa?”
Dariya ya ba wa Malam Bedi, ya ce “Mairon ce zata zauna maka waje daya? Ai yadda kasan tsuntsuwa haka ta ke. Idan dai ba gaban Innarta ba ne babu inda zata zauna. Ai jin ku kawai nakeyi da ka ce wai ta zauna nan mu fito”.
Ya girgiza kai suka ci gaba da tafiya yana ba shi labarin Mairo. Wanda duk mai bakanta zuciya ne ga Habibu.
Ya ce “A rana in ba a kawo min kararta sau hudu ba, a kawo sau shida. Malaminsu ya gaji da sulalewar da ta ke yi, ya ce ta yi zamanta gida. Ni al’amarin Mairo ai sai addu’a. Kuma duk Hure ce ta jawo”.
Habibu ya yi kankan da murya ya ce “A gaskiya Baba kai ma da naka laifin. Mai yasa idan Innar ta yi hukunci akan Mairon ba ka ketarewa? Yanzu sabida Allah kamar Mairo ace har yanzu ba ta shiga makarantar boko ba, sai yaushe? Sai karatun ya wuce lokacinta? Fisabilillahi ina matukar takaicin rayuwar Mairo. Ina tausaya mata, domin dai ita ‘ya mace ce, gidan wasu zata je ba da jimawa ba.
Babu mijin da zai iya zama da ita da wannan rashin tarbiyyar wadda ni ba haka aka yi mun ba”.
Ya yi shiru kamar zai yi kuka, zuciyarshi na matukar kuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button