ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya yarda wayar ya fice, yana share hawayen da suka cika mishi ido.
Wasa-wasa sai da Mairo ta kwashe watanni uku cur cikin wannan halin, a lokacin cikin jikinta ya fito sosai, domin ya shiga cikin watanni na biyar.
Rannan daga ita sai Hajiyar Dutsinma a dakin, ta farka daga barci, ta kurawa silin ido, al’amuran suka soma dawo mata tar-tar.
Ta tuna wai Amiru ya sake ta, ba tareda ta yi mishi laifin komi ba, alhalin suna tsaka da son junansu. Bayan ta mallaka mishi duk wata soyayyarta.
Sannan ya auro Hanan, ba ta fita daga wannan bacin ran ba, ya dankara mata saki, ta tabbatar bisa tursasawar Hajiya ne, amma Amirun ba zai taba yi mata haka akan-kanshi ba, ko giyar wake ya sha.
Tana mai sa ran bada jimawa ba za su dai-daita da mijinta ya maida ita ta zauna lafiya da Hajiya Aisha, tunda abin da Hajiyar ta kwallafa rai, har ta tsane ta a kanshi, ga shi Allah Ya bayar.
Sai kuma ta tuno wai an fada mata ya kara kamuwa da ciwon zuciya irin wanda yayi a baya, aka samu rayuwarshi da kyar da taimakon ta. Gashi yanzu basa tare. Kai ita ji tayi ma kamar ance ya rasu! Daga bakin Hajiyar Dina da ba zai taba yi mata karya, ko zolaya ba.
Ta soma kuka a hankali, kukan sabo, soyayya, kauna da kewa. A tsayin zamansu na shekaru takwas, bai taba bata mata ba, sai bisa kuskure. Soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata, wani abu ne da ba zai taba kankaruwa daga zuciyarta ba.
Tunda ya aure ta ya haramtawa kanshi sauran mata. Bai kara hada jiki da wata diya mace ba, bayan ita, har inda yau ke motsi. Har kuwa wadda ya aura da auren sunnah. Taji wannan a bakin Hanan ba a bakinsa ba. Duk da matakin rayuwa irin nashi, wannan bai shagaltar da shi daga rudin duniya ba.
Ta tabbata ta yi babban rashin da har abada ba zata mayar da makwafinsa ba.
Ta mika hannu ta shafi kasan mararta, inda babynshi ke kwance, yana wutsil-wutsil cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido a hankali, hawaye masu dumi suna zirara ta gefen idonta suna shiga cikin kunnuwanta. Ba ta damu da ta share ba, haka zuciyarta ba ta daina kokawa ba.
A wannan halin Habibu ya tarar da ita. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta. Ya ce.
“Mairo, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu…”
Ga mamakinshi sai ta fado jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya. Ta ce.
“Yaya Habibu da gaske mun rasa AMEERU?”
Ya ce
“Mun rasa auren shi dai Mairo, da gaske mun rasa auren mai kaunarmu da gaskiya da amana. Amma Ameeru yana nan a raye.
Duk wanda yace dake ya rasu, ya fada miki ne kawai don ya tayar da hankalinki. Ko kuma baki tsaya kin saurara dai-dai ba. Amma yana gida, kwance a dakin ki. Akan gadon ki.
Kwanciyar shi ciwo da rabuwar auren ku ya barni da kewa, da katoton gibi a zuciyata. Wanda mayar da shi wani abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. Don haka ki dage da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa.
To lose a friend like him, will be the GREATEST lose of all losses. To lose a husband like him, is another GREAT loss. (rasa aboki kamar sa, ba karamar asara ba ce daga manyan asarori, kuma rasa miji kamar sa, shima babbar asara ce.) Sai dai mu cigaba da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya.
Wannan ne kadai babbar sakayyar da zamu yi wa masoyi irinshi. Amma ba da son ranshi ya sake ki ba.
A matsayinmu na musulmi, ma’abota imani da yarda da kaddara, muna da tabbacin cewa, duk abinda ya faru damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka muna da kyakkyawan zaton Zai tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa.
Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce.
“Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da muka rasa auren Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har mu cinye jarrabawarmu.
Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da ‘yan uwanshi suka yi, kan halinda yake ciki. Kuma Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti.
Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi gafarar ki sun rasa. Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana.
Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a gabana don na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi mana, yayi mamaki nima nayi mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun soma gani tun a duniya, tunda Amirun na neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko kofar gida Amiru bai kara takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki.
Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya rage ya saketa saida nasa baki tukunna ya hakura.
Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki shikuma ya gaya musu.
Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari ne ga mai juna biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa ki………bani da Uwa, bani da Uba, sai ke da abinda zaki haifa….”
Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa.
Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce.
“Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye”.
Ya ce,
“To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz… Mairona!”.
Ta ce
“To ba ni in ci”.
Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman kaji ya yi lugub. Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika mata. Ta karba ta soma ci sosai har tana taune harshenta sabida yunwa.
Dina ta shigo rike da kwandon kayan abinci, suka zauna akan kilishi suna ci ita da Habibu. Mairo na kallonsu tana raya abubuwa a ranta, wato ranar da aka kaita gidan Amiru ya takura mata sai ta ci abinci akan idonsa.
Ta kai hannu da sauri ta goge hawayen da suka kara shimfido mata, don ba ta son Yaya Habibu ya gani, ranshi ya baci. Amma ta riga ta san kuka ta dinga yinshi kenan, har karshen rayuwarta. Tunda yanzu itada Amiru sai dai a TUNA BAYA……Yaya zatayi da dimbin soyayyar shi data kankanewa zuciyarta????
An sallami Mairo ranar wata asabar bayan likitocinta sun tabbatar komi nata ya koma dai-dai. A lokacin cikinta ya cika watanni shidda cif, wanda ya yi dai-dai da cikar Amiru watanni hudu yana jinya.
Suka dawo gidan su Dina, inda a washegari Habibu da Dina suka yi shirin tahowa gida Najeriya. Gidan ya rage daga Mairon sai Hajiya da masu aiki, don Abban Dina bai cika zama ba sai a weekend, kullum yana ofis.
Bata tashi daga inda ta yi sallolin farilla guda biyar, ba tareda ta yiwa Amiru addu’ar neman lafiya daga Ubangiji ba.
Hajiyar Dina na kula da ita yadda ya kamata, ko Innarta iyakacin kulawar da zata yi mata kenan.
Watan Hajiyar Dutsinma biyu tare da su jikinta ya yi kyau ta koma gida.
Kwanaki na mirginawa su zama watanni, har watan Aprilu ya kama, wanda shi ne EDD dinta. Sai dai Mairo ba ta yarda anyi mata ‘scan’ ba. Ranar wata alhamis nakuda ta tashi cikin dare, haihuwa gadan-gadan. Don haka ba da bata lokaci ba Hajiya ta tuka su da kanta suka nufi asibitin da ta ke awo, nan da nan aka karbe ta a (labour ward), nakuda ta tsayin awanni uku cur, kan Hassan ya bullo, kamin likitocin su yi wani yunkuri, shi ma Hussaini ya biyo dan uwansa.
Aka turota dakin hutu, Hajiya na rungume da jariran tana yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, sabida kamar Amiru ya yi kaki ya tofar. Sannan ‘identical twins’ irin wadanda banbacesu zai yi wuya.
Sai dai da alama Hassan kalar Babanshi ne, wato (choculate), yayin da Hussaini ya debo hasken fatar Mairo.
A take Hajiya ta yi waya ta sanar da Habibu, ya yi hamdala ya kuma nemi wayar Alh. Abdurrahman ya sanar da shi, don haka a karshen satin suka dungumo har Hajiyar Amiru dasu Sabah suka iso Malaysia.
Farin ciki a wajen Hajiya Aisha da Alh. Abdurrahman abin ba’a cewa komi. Hajiya har da kukanta na nadama, ga dai ‘ya’ya ba daya ba har biyu Mairo ta Haifa, duk kunyar Mairon ta isheta, ta kama ‘yan jikokin ta rungume tana yi musu addu’a, ji take kamar Amirun ne ta rungume a ranar data haifeshi, sai dai dukkaninsu babu mai ra’ayin a yi wani taro sai addu’a da kowa yake yi wa mahaifinsu, wanda har zuwa lokacin ke kwance cikin halin jinya.
Yara sun ci sunan Habib da Amir, babu kuma wanda ya yarda da a sakaya. Ana kiransu da sunansu abinsu.
Bayan su Hajiya sun koma Mairo ta ci gaba da rainon ‘yan biyunta cikin koshin lafiya da taimakon (Nanny) Bamaleshiya da Hajiya ta daukar mata.
Kamin watanni hudu sun cika sun yi kiba, sun yi bul kamar ‘yan watanni goma sabida samun kulawa da ruwan nono isasshe. A lokacin ne kuma ‘addmission’ dinta na yin PhD ya fito a ‘university of Malaya’.
A satin da zata fara karatu, Yaya Habibu ya zo Malaysia. Yace tayi shiri suje Najeriya ta kaiwa Amiru ‘ya’yan shi ya gansu. Don ya samu sauki har ya soma zuwa ofis. Daddy ya samo mishi aiki a CBN. Don shi Habibun bai yarda su sake yin hadin gwiwar ba kamar yadda Daddy da Amirun suka bukata, yace saboda halin rai. Ya kuma ce da Daddy akwai kudurin da yake dashi a kan bankin nan bada jimawa ba. Amma ba wai don yayi fushi da abinda Hajiya tayi ba.
Mairo bata son wannan tafiyar sai don Yaya Habibu ya matsa mata. Amirun ne bata son gani, don bata son duk wani abu da zai taba zuciyar ta a halin yanzu. Ta riga ta sanyawa zuciyarta YAKANAH (sunan littafin Takori mai zuwa). Ta koya mata dangana, ta koya mata rayuwa ba AMIRU. Karatun ta kawai tasa a gaba, da rainon ‘ya’yan da Allah ya bata.
Lokacin da Daddy ya gayawa Amiru mairo ta haihu har ‘ya’ya biyu, bai nuna wani farin-ciki ba, don yana kullace da Mairo, da bata taba zuwa ta dubashi ba har yayi ciwon sa da jinyarsa ya gama ya gaji ya mike. Bashi da wani sauran buri a rayuwa, tunda ya rasa Mairo.
Sannan Daddy yace babu maganar biko, ba zancen kome, don bai yarda sun gama horuwa ba, Amirun yayi ta zama a gwauro, ko su aura masa mai haihuwa. Ya kuma ce da Amiru in zai mike ya fuskanci sabuwar rayuwa to ya mike, in bazai mike ba, yayi ta kwanciya soyayya ta kassara shi. Don shima yana da nasa laifin. Na kin gaya masa duk abinda ke faruwa saboda tsoro da son Hajiyarsa. Har saida komai ya lalace. Daddy yace
“ita tana son ka ta lalata maka rayuwa?”