ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

A fannin ita Hajiya, zaman Amirun haka babu iyali ya fara damun ta. Tana so tayi zancen biko a maida aure tunda saki daya ne, babu fuska daga Habibu da Daddy. Don haka tasa ido, don ganin hukuncin da suke nufi.
8/9/21, 12:13 PM – Kawata: 33
Saidaifa rayuwar Amiru ta canza sosai. Ya zama babu murmushi babu far’a sai ‘dark-spaces’ kusan koyaushe make a fuskarsa. Sai ayyukan dake gabansa. Ya kudire a ransa idan ba Daddy ne da kansa ya bude baki yace ya maida Mairo ba da bakinsa, to ya hakura da ita har karshen rayuwarsa.
Yamma lis, suka iso filin jirgin saman Abuja. Dina dasu Muhammad sukaje tareda direba filin jirgin suka dauko su. Suna zuwa gida Dina ta karbi yaran tayi musu wanka ta shiryasu da kaya na alfarma. Habibu ya dura su a mota tareda su Muhamnmad da mai rainon su Esta da suka taho da ita daga Malaysia sai Asokoro.
Kasancewar ranar Lahadi ce, Daddy yana gida shida Amiru a karamin falonsa, suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Habibu ya yi sallama rike da mai sunan sa yayinda Muhammad ya biyo bayansa dauke da Amir. Ya saki takardun hannunsa ya bisu da kallo. Ba zaka iya karantar halin da zuciyarshi ke ciki ba.
Suka yiwa kansu mazauni a falon Esta tana waje, Daddy sai murmushi yake yayinda Amiru ya zamo mutummutumi, tsigar jikin shi na tashi cikin kauna da shauki. Ya matso ga Habib dake zaune a cinyar Habibu, ya durkusa a gabansa ya mika mishi hannu, siraran lebbansa dauke da wani irin ni’imtaccen murmushi, da bai taba yi a rayuwarsa ba.
Wata irin kauna ta da da mahaifi ke fizgar zuciyar shi. Amma sai Habib ya noke a kafadar Yaya Habibu wato, bai san shi ba.
Yaji ba dadi, ya koma ga Amir yana karkada mishi ‘ya’yan mukullai, da wayo da dabara ya samu ya yarda ya dauke shi. Ya rungumeshi sosai a kirjinshi yana sunsunar shi. Yana shakar kamshin turaren Mairo (Fahrenheit) daya kama jikin yaron. Ganin dan uwanshi a hannun shi sai shima Habib ya miko hannu, ya hadasu su duka biyun a kirjinsa, sai yaji kamar Mairo ce ya rungume. Amma don mazantaka, bai yarda ya zudda hawayen da suke son bashi kunya ba.
Daddy da Habibu suka bisu da kallo cikin tausayi. Daddy yace “saukar yaushe?” Yace “dazunnan muka iso”.
Dai-dai lokacinda Hajiya ta shigo falon cikin kwalliya ta alfarma. Bakinta ya fadada da far’a da murmushi. Tace
“A’ah! Sababbin masu gidan sun zo, tsofaffi sai su zo su fice…” tana kallon Daddy tana dariya. Ya harareta don yasan dashi take, yace “da tsohuwar zuma ake magani. In dai wadannan ne da ba mazauna ba ai gaki gasu, da sun tafi zaki dawo min ne kina rara-gefe”.
Ba yadda bata yi ba don ta dauke su amma sun like jikin Ubansu. Ta fita ta kawo ‘teddy’ na ‘ya’yan Nina da suka zo hutu sannan suka yarda da ita. Daddy yana son ya tambayi Habibu mai yasa Mairo bata zo ba? Yaga babu dalilin da zai yi masa wannan tambayar sai yayi shiru. Shikuwa Amiru Allah kadai yasan abinda ke cin zuciyar shi. Mairo ta daina son sa……! Mairo bata son ganin sa…..!!
Har goma na dare suna can, yaran suka soma rigima, duk da an basu madara. Uwarsu suke so haikan. Amma Amiru ya kasa bada su. Saida Habibu yayi mishi alkawarin kafin su tafi gobe zai kai mishi su ofis sannan ya dauko su har motar Habibu, bayan Hajiya ta cika su da toshi. Daddy ma ya bada check na kudi masu yawa yace a dinka jamfa, baya son ganin su da daura ‘suit’ irinna Ubansu.
Mairo tayi shirin barci a dakinta dake gidan Yaya Habibu. Ta sanya yaranta a gabanta tana kallon su da fuskar mahaifinsu. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ wanda ya tuna mata da ‘those precious moments’ da suka shude a baya. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ da suka kwaso, wanda ya dawo da so da kaunar mijinta sabo fil a zuciyar ta.
Ta shiga tsakanin su ta rungume kowanne a jikinta. Ta soma sheshshekar kuka a hankali, na tashin tsohon mikin daya jima da samun sauki. Shiyasa bata so zuwa ba, amma Habibu ya takurata. Ta fadi a ranta Amiru ya daina son ta…….! Tunda har bai damu daya ganta ba. A karshe ta hakura ta sanyawa ranta salama. Tunda ance komai yayi farko, to inshallahu yana da karshe WATARANA!
Washegari Habibu ya cika alkawari, ya sake diban Amir da Habib da Esta ya zuba su a mota zai fita da niyyar kaisu office din Amiru suyi sallama kamar yadda yayi alkawari. Yana kokarin tada mota Amiru na sanyo hancin motarsa ‘camero’ cikin get din Habibun. Don haka Habibun ya dakata har ya bude motar ya fito.
Ya karbi ‘ya’yansa ya soma ‘kissing’ kamar bazai bari ba.
Daga can saman bene Mairo ta yaye labulen dakinta don iska ta shigo. Nan ta hango su. Ta kurawa Amir ido. Bayan muguwar ramar da yayi, ya bar lallausar kasumba mara tsari ta cika fuskarshi, abinki da mai yawan gargasa. Sannan ya saya kwayar idon shi cikin ‘dark-spaces’ wanda ya hana mata gano halin da kwayar idanun shi ke ciki.
Karan hancin ya kara fitowa, zirit, kamar karas. Wani irin so na fizgarta. Ta saki labulen a hankali ta koma da baya ta fada a gadonta. Tana mai fidda numfashi da sauri-da-sauri. INAMA ACE…….hannun agogo zai dawo baya???
Washegari suka koma Malaysia. Mairo ta fara karatunta cikin nasara, tana barin yaran a gida wurin mai rainonsu da yake an fara ba su madara. Kafin su cika watanni tara suna gudunsu ko’ina, musamman Alh. Abdurrahman ya bude mata ‘account’ a nan ‘Kuala-Lampur’ duk wata yana sako mata makudan kudi na fita hankali, don lalurorinta da kula da ‘yan jikokinsa.
Bayan kuma ba abin da Ambassada ya rage su da shi, ga na Yaya Habibu. Gaba da baya gata ya lullube Mairo da ‘ya’yanta, abin sai godiyar Allah.
Shekaru ukku cif, wadanda suka yi dai-dai da cikarta shekaru talatin a duniya, da kwalin digiri, master, da digiri na kololuwa.
Dr. Maryam Muhammad Bedi, ta tattaro ta dawo gida Najeriya a garin Abuja, zuwa lokacin Habibu ya yi ficce, bankin ‘Habib Bank’ ya samu habaka zuwa ‘branches’ a dukkan ‘thirty six states’ da muke da su a gida Najeriya, kamar yadda Amiru Abdurrahman ya yi fata. Yau ga ci gaban ya samu, ba tare da Amiru ba.
A wannan ranar da ake (ten-year anniversary) na cikar bankin shekaru goma da kafuwa, Habibu kuka yake, maimakon ya yi farin ciki.
A yayin da al’ummar taron suka dauka kukan farin ciki yake yi, amma shi kadai yasan dalilin kukansa, wanda bai wuce na alhinin samuwar cigaban shikadai, ba tare da Amiru ba.
A kalaminshi na karshe, bayan ya yiwa mahalarta taron godiya mara iyaka. Ya ce,
“Ya tafi ya bar bankin da kewa, bayan shi ya kirkireshi. Ya bar bankin da babban gibin da har gobe bai cike ba. Na kuma tabbata har abada ba zai cike ba. Sakamakon dumbin ALHERINSA gare ni. A yau na tashi daga mamallakin ‘Habib Bank’, na kyautar da shi ga ‘ya’yan AMEERU ABDURRAHMAN GAYA”.
Amiru ya daga ido yana kallon shi, extremely puzzled! To haka Alh. Abdurrahman. Ashe wannan shine kudurin da Habibu yace yana dashi kenan akan bankin, ya ki yarda amaida hannun jarin Amiru cikin bankin?
Ya sanya hannu cikin takardu, lauyoyi suka diba, su ma suka rattaba hannu. Sannan ya ce,
“as a servant, zan ci gaba da juya musu dukiyarsu har zuwa girmansu”.
Hajiya ma ta dauko duk takardun dukiyar Amiru dake tare da ita, ta danka mishi. Ya hada dana wajen Habibu ya adana a bankin. A wannan ranar Habibu yayi kuka, kawai sabida tausayin AMEERU. Don gabadaya rayuwarshi ta canza ‘completely’ ta zama ‘no meaning…’ kamar yadda ya fadawa Mairo a baya.