ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

“My life has no meaning……idan ba tareda ke ba”.
Habibu ya watsa mata takardun neman aiki, a manyan jami’o’inmu, tun daga Ile-Ife, Ahmadu Bello, Nsukka, Bayero, Lasu da sauransu, ba don neman kudi ba, sai don al’ummar Najeriya su amfana da ilimin da ta wanzar da rayuwarta tana nema, don su amfana.
Ba da jimawa ba jami’o’i har biyar suka dauke ta, ciki kuwa har da jami’ar Abuja, wadanda ta bari a baya. Amma ta zabi BAYERO domin a ganinta al’ummar Kano su ne al’ummarta.
Habibu bai takura mata da zancen aure ba, ko tayin ta koma gidan Amiru. Sai dai shima yana ganin lokacin yayi daya kamata a maidawa Amiru matarsa sabida yadda zawarawa manya-manyan kusoshi ke yi mishi rubdugu, a gida ne ko ofis. Alh. Abdurrahman ya fara tsawatar mata da cewa, ba zata koma Kano ba har sai ta fidda miji ta yi aure.
Sai ta sa musu kuka tana rokonsu, kada su kara yi mata zancen aure, idan ba so suke ita ma CIWON ZUCIYAr ya kamata ba. Me zata yi da wani da namiji ba Amiru ba? Me zata nema a jikin wani namiji bayan Amiru? Amiru yasa ta raina sauran maza, ta yadda har basa burgeta, duk ilminsu da mukamin su kuwa.
Gashi da alama Daddy baya son komen nasu. Tunda koda wasa bai taba furtawa ba. Ya kama Mairo da Habibu ya rungume kamar shi ya haife su, ya jibanci dukkan al’amuransu, amma baya ko son kallon Mairo da sunan matar Amiru. Itama kuma tunda hakane bazata taba nuna tana son komawar ba, koda hakan na nufin ta auri wani ne ba shi ba!
Alh. Abdurrahman ya ce,
“Aure ya zama dole Mairo, domin shi ne cikar kima, mutumci da darajar diya mace. Duka wadannan kwalayen naki aikin banza ne idan babu aure”.
Ta yi masa alkawarin su barta ta fara aikinta, a hankali za ta zabi wanda hankalinta ya kwanta da shi. Ya so ya karbe yaran, amma ta roke shi ya bar mata, zuwa wani dan lokaci kalilan, don suna debe mata kewa.
Gida guda suka bata cikin ‘new site’, suka tare ita da ‘ya’yanta da mai rainonsu, mai suna Lami. A lokacin Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa suna karatu a Bayeron, sai suma suka dawo gidan suna zaune a baskwata.
Baffa yana zuwa duba su akai-akai, su ma suna zuwa idan sun sami lokaci. Mairo ta fara ‘lecturing’ a ‘department of sociology’ cikin nasara da sanin makamar aiki. Ta sanya yaranta a ‘staff-school’ kullum su Lawan suna kaisu su dauko su, da yamma kuma su kaisu islamiyya da ke nan cikin ‘New-site’.
Ta dade da fara rubuce-rubuce tun tana Malaya akan fannin da ta ke karantarwa, wanda ya kaita ga matakin zama ‘proffessor’ cikin dan lokaci kalilan.
Kyawunta, zurfin iliminta, sakin fuskarta da yawan taimakonta ga dalibanta, ya sanya ta zamo abar so ga dalibanta. Sai dai fa kowa yana bin kwakkwafi ya yi mamaki idan aka ce ba ta da aure. Sukan ce kyakkyawar mace kamar wannan ace ba ta da aure, ai abin mamaki ne sosai. Sannan kallo daya zaka yi mata ka tabbatar ba da wannan aikin ta ke cin abinci ba. Tana dai yi ne don ra’ayi, amma ba don neman wani abu wai shi ‘kudi’ ba.
Proffessor Maryam Muhammad Bedi, ta zamo daya daga cikin malaman da ake ji da su a jami’ar Bayero, ko sabida karyayyen harshenta na Turawan America zallah. Don haka da yawa suke bin kwakkwafi akan rayuwarta, har su san inda ta samo wannan ‘background’ din. Wani dalibinta ya soma rubutu a kanta, sai dai duk yadda ya so ya ji tana da aure ko ba ta da shi, ba ta bada wannan damar ba.
Dr. Mairo ta shiryawa dalibanta masu fita a wannan shekarar ‘conference’ mai taken, “YADDA ZA A GYARA AL’ADA TA YI DAI-DAI DA ADDINI” Wanda take so Mai girma sabon V.C ya halarta. Don haka ta je ta nemi ‘appointment’ na ganin V.C a ofishinsa. Aka sanya ta cikin jerin wadanda za su ga V.C a safiyar washegari.
Da ta dawo gida ta tarar Lawan ya dawo da su Habib, Amir yana kwance shiru cikin kujera ba kamar yadda ya ke ba. Ta dora hannu a kanshi, zafi rau, Lawan ya ce.
“Amir ba ya jin dadi tunda safe”.
Ta ce
“Za mu je asibiti da safe, idan na ba shi ‘paracetamol’ zazzabin bai sauka ba”.
Ta dauko ‘paracetamol’ cikin ‘first-aid box’ dinta ta ba shi da dan kankanin cokali. Har zuwa washegari zazzabin bai sauka ba. Ga shi kuma tana da ‘appointment’ na ganin V.C, don haka ta sa yaran a bayan mota suka nufi cikin makaranta da zummar idan ta ga V.C sai ta wuce da su asibiti, don mawuyaci ne daya ya yi ciwo dan uwansa bai kama ba.
Ba ta barsu a mota ba, sanya su ta yi a gaba suka soma taka matattakala wadda zata sada su da ofishin V.C.
Mutum biyu ne a gabanta, sai da ta jira suka fito, sannan ta kama hannun Habib da Amir suka sanya kai cikin ofishin, bakinta yana mai furta sassanyar sallama.
Ya juya baya yana zakulo wasu takardu cikin loka. Idanunshi saye cikin farin gilashi, sanye cikin farar shadda ‘excelsior’ dinkin Muhammed Abacha. Hular kanshi na aje bisa teburinshi.
Gaban Mairo ya yi wani irin mugun faduwa, takardun da ke hannunta suka kwace suka watse a kasa. Amir ya tsugunna yana tsince mata. Shi kuwa Habib tattakawa yakeyi da cambos dinsa.
Ko mutuwa ta yi ta dawo, ba zata mance surar UNCLE JUNAID ba, wanda ke tsaye nan a gabanta. Sai dai wannan Junaidun, ya sha ban-ban da wanda ta sani shekaru goma sha biyu a baya. Wannan cikakken magidanci ne, da yasha gwagwarmayar rayuwar neman ilmi cikin fanninnika daban-daban, ba dan saurayi Junaid Galadanci ba.
Duk da alamun shekaru da suka hau kansa, har yanzu yana nan a Junaidunsa da ta sani, ma’abocin zati da kamala, gami da kwarjini bayyananne daga Sarkin halitta. Ta rasa cikin halin da ta samu kanta, rudewa ce ko gigicewa ce? A’a, ko kuwa gaba daya makuwa zata ce ta yi?
Ta juya da baya–da-baya zata bar ofishin, ya juyo a hankali ya dubi mai shigowa.
“Mariama!”
Maironshi da a kullum ta ke zuwa a farke, ko cikin mafarkinshi. Mairon da dai-dai da rana daya cikin shekaru goma sha shidda, zuciya ba ta taba hutawa da kaunarta ba. Ruhi bai bar mafarkinta ba, haka tunani bai taba kuskuren manta ta ba.
Ya dago Habib ya dauke shi tare da kama hannun Amir ya zauna a kujerar da mutane suke zama don ganawa da shi. Cikin wata irin kassararriyar murya, ya ce.
“Ya ya za ki koma? Ko ba ke ce ‘Proffessor Maryam Bedin ba?”
Ta ja tunga a jikin kofa, ba tare da ta juyo ba. Ita bata fita ba, ita bata juyo ba. Hannunta jikin marikin kofa, ta ce
“Ni ce”.
Ya ce
“To mene ne ajandar?”
Ta ce
“Na zo neman alfarmar V.C ya samu halartar ‘conference’ dina ne”.
Ya yi murmushi yana dauke da Amir ya tako har inda ta ke tsaye. Wani irin sassanyan kamshi da ba zata ce ko na wanne turare ne ba a duk iya sanin da ta yi wa turare ya kassara mata gabbai.
“Na kasance ma’abocin son ‘twins’ Dr. Mairo, ko za ki bani aronsu? Na dawo miki da su bayan awanni goma sha biyu?”
Wannan karon ne ta juyo ta dube shi, wasu kibbau na tsohuwar soyayya suka soki idanun kowannensu. Tsohon tsimi ya tashi, wanda ya yi sanadin tashin tsigogin jikin kowannensu. Da kyar ba tare da ta sake yarda sun hada ido ba, ta ce.
“Idan iyalinka suka tambaye ka ina ka samo su mai girma V.C me zaka ce musu?”
Babu bata lokaci, ya ce da ita.
“Ya’yana ne, wadanda Mairon Gurin-Gawa ta haifa mini……………”
Kuka ya kece mata, don haka da gudu ta fice daga ofishin tana ji a ranta, ta fasa yin ‘conference’ din, tunda shi ne ya yi sanadin da ya taso da tsohon gyambon da ya dade da warkewa a zuciyarta.
Gidan Baffa ta wuce kai tsaye, ta nufi dakin Habiba ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Ta yi juyi a lallausan gadon Habiba tana tariyo abinda ya faru cikin ‘yan mintina kalilan.
Baffa ya shigo dakin ya zauna a kujera yana fuskantarta, ta goge hawayenta, ya ce.
“Me ya faru? Ke dai har gobe abun kuka ba shi da wuya a wurinki?
Yanzun nan Habiba ta yi min waya ta ce, kin shigo da gudu kina kuka. Idan ka girma sai kasan ka girma, ka koyi dauriya da juriya irin ta manya. Ba akan kowanne kankanin abu ka bare baki ka yi ta kuka a gaban mutane ba”.
Ta yi murmushi tana goge hawayen idanunta, ta ce.
“Baffa, Uncle Junaidu na gani, bayan wucewar shekaru goma sha biyu. Ya tuna min da abubuwa da dama da suka faru cikin rayuwata, shine dalilin kukana, domin na tuna abubuwa da dama da yanayin shekaru da cigaban rayuwa ba su sani na manta ba”.
Ya ce,
“kwanannan naji a labarai anyi ‘appointing’ din shi matsayin shugaban jami’ar Bayero ai. Har yau har gobe kuma bai fasa zuwa gidan nan yana gaishe ni ba, bai fasa yi min manya-manyan alhairori ba. Sannan son ki har yau bai barshi ba.
Ban taba ganin ‘SOYAYYAH’ irin ta Junaidu ba. Don haka ni ma har gobe ban fasa yi mishi addu’ar budi da nasarar rayuwa ba”.
Mairo ta cika da mamakin jin cewa Uncle Junaidu na zuwa wajen Baffa har yau. Amma koda wasa Baffan bai taba gaya mata ba. Ba ta gama mamakinta ba su Habib suka shigo suna ta tsalle, kowannensu rike da kit-kit da leda fal ‘choculates’ suka fada jikinta.
“Mummy mun dawo… Daddy yana gaishe ki”.
Sai Baffa ya tashi ya fita, ya tarbi Junaid a dakin bakinshi.
Habiba ta shigo dauke da kulolin abinci. Su Amir suka makale ta suna ta ba ta labarin inda Daddy ya kai su.
Ta ce,
“Wai wane ne wannan Daddyn?”
Amir ya ce
“Daddyn Mummy ne”.
Mairo ta ce
“Rabu da shirmen su Mama, shugaban jami’armu ne”.
Habiba ta yi murmushi ta ce.
“To ko da shi za a yi ne?”
Ta yi shiru ta daure fuska bata bata amsa ba. Don ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata zancen aure.
Baffa ya dawo dakin yana murmushi, ya same ta tana cin abinci.