ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

“Idan kin kare sai ki je ku gaisa da Alhaji Junaidun. Daga nan ya ce yana so zai kai Amir asibiti, don ya ga alamun ba shi da lafiya”.
Matsayin Uncle Junaidun da kimarshi da ke zuciyarta, ya fi gaban ta ce ba zata je ba. Baffa ya ci gaba da yi mata nasiha mai sanyaya zuciya da sanya imani, akan lokaci ya yi da ya kamata ta tsaida hankalinta wuri guda ta yi aure, domin cikar mutuncinta a duniya da lahira. Tunda Amiru da Daddynshi basa bukatar komen.
Ta yi sallama a kofar dakin, yana zaune cikin kujerun (leather) da suka yi wa dakin kawanya, Habib da Amir akan cinyoyinsa, yana ta haba-haba da su kamar ya maishe su cikinsa. Ya dago idanunshi da suka yi fari sol, yana dubanta.
A zahiri Maironshi ce, sai dai fa wannan Mairon babbar mace ce ‘yar shekaru talatin da doriya, wadda kuma a idanunka da kiyasinka ba zata fi shekaru ashirin da biyar ba.
Wannan bakauyar da aka kawo mishi kafafuwanta jawur cikin lalle tsohuwa ta fada kwata, fatar kamar shuni, yau idan ka dube ta, tsammani zaka yi Balarabiyar Omman ce, ba wai ‘yar asalin kauyen Gurin-Gawa ba.
Kallonta ya ke, kallon da ke nufin al’amura da dama. Ita ma kallonshi ta ke, kallon da ke tuna mata da al’amura da dama. Da gaske Uncle Junaidunta ne, sai dai wannan ya kara yi mata GiRMA. Ta TUNA BAYA… ta tuno ALHERInsa gare ta, ta tuno SIRADIN RAYUWArta, ta yi ALKAWARI ko BAYAN RANTA matsayinshi ba zai taba canjawa daga zuciyarta ba. Cikin muryar GIRMA ya ce.
“Mairo, ina Amiru Abdurrahman?”
Ta kai gefen mayafin abayarta ta dauke wasu siraran hawaye da suka kawo mata zarya. A hankali tace.
“Mun rabu!”
Duk suka yi shiru na ‘yan dakikai. Can kuma ta kawar da shirun da cewa.
“How comes kai ne sabon V.C dinmu, amma ban taba sani ba?”
Shi ma ya yi murmushi ya ce.
“Ni nasan kina cikin ‘proffessors’ saidai ban tabbatar ba, sannan ban taba tunanin ba kya tare da maigidanki ba, a wane dalili zan nemeki? Sannan bani da tabbacin ke din ce ko ‘namesake’ dinki ce, na dai ga sunan da ya tsayamin arai ‘among the proffessors’,
Sannan ai ban dade ba ai, banyi dadewar da zaki san ina cikin makarantar ba” tace “haka ne”. Ta sunkuyar da kai kafin ta dago ta sake cewa
“Ikon Allah kawai”.
“Ni ma sai ki dauke shi a hakan, wato kudurar Allah, ta fi ga haka”.
Ta jinjina kai, ta ce
“Kwarai kuwa”.
Suka maida idanunsu akan Habib da Amir, wadanda ke ta dabdalarsu cikin dakin, dukkaninsu sai suka yi murmushi, yaran suka burge su.
“Kuruciyarsu na da ban sha’awa”.
Ya fada a zuci, bai san cewa a fili yake fadi ba.
“Kamar kuruciyar Mairo, Mairon Baba da Inna, Mairon Kausar da Nabilah……..”
Ta yi dariya ta juyar da kanta. Wani ala’amari mai girma na cin zuciyarta. Sai dai ba irin wanda take ji a tsohon mijin ta ba. Ya kura mata ido, zuciyarshi na harbawa.
“Ina labarin Nabilah da Yaya Habibu?”
“Nabilah tana nan Kano, ‘ya’yanta biyar. Yaya Habibu yana Abuja”.
“Nima na yi aure Mairo. A lokacinda na riga na sallamawa zuciyata cewa na rasa ki, bazan same ki ba, kin riga kin yimin nisa, kin zama matar wani na. Wanin da nake da tabbacin ko mutuwa yayi bazai tafi ba tareda igiyoyin aurenki ba.
A halin yanzu Ina da ‘ya’ya biyu, tareda ‘yar uwata Ikhlas. Sai dai har wannan lokacin da tunanin Mairo nake kwana nake tashi. Sannan dashi nake ‘functioning, will you believe it?”
Ta dago fararen idanunta ta haske shi da su. Tace “sabida me Uncle?”
Babu jinkiri, babu inda-inda ya rausayar da kai ya ce
“sabida Soyayyarki Mairo!
Soyayyar da na ke yi miki a wancan lokacin Mairo, ta zarta hankali, ta zarta duk wani kokarin hankali na ya fassarata. Mahaukaciyar soyayya ce Mairo, wadda ta makantar da ni daga daga ido na dubi sauran mata. Ta dakusar da hasken mata ta Ikhlas daga cikin idanuna.
Na tabbatar tunda na rasa Mairo, to bazan samu makwafinta ba. Don haka ne Hajiya tasha wuya da fari kamin inyi aure. Don nasan ko na yi, to bazan baiwa matar hakkokin da addini ya ce na ba ta ba. Ba zan iya sallama mata zuciya da gangar jikina ba”.
Ya taso ya tsugunna a gabanta, yana so su hada ido, amma ta ki hakan. Ya dora hannunshi akan tafin kafarta. Ta lumshe ido a hankali ta bude su akan yatsun hannunshi da ke bisa tafin kafarta. Ya dauke hannunshi ya zauna sosai a gabanta, ya ci gaba da cewa.
“Hajiyata ta shiga tashin hankali mai yawa, ta yi kuka, ta yi rokon duniya akan na yi aure, na kasa Mairo.
Daga baya sai malamai ta sa suke yi min rokon Allah, sun tabbatar mata da zan yi aure, sai dai da sauran LOKACI, tunda zuwa yake. Daga baya sai ta koma nasiha, amma zuciyata ta riga ta bushe. Na tabbatar mata idan dai ba so ta ke na auri matar na dinga daukan alhakinta ba, to ta kyale ni.
Haka ta hakura ta zuba min ido, amma ta ce ba ta fasa yi min addu’a ba. A yau ina da yakinin Allah Ya amsa addu’arta. For the first time da na ke ji a jikina LOKACI ya zo da zan yi AURE ba irin na Ikhlas da ya zamto hadin iyayen mu ba. Wanda akayi ba tareda anyi shawara dani ko neman yarda ta ba.
8/9/21, 12:19 PM – Kawata: 66
khlas diyar kanin mahaifina ce da Hajiya ta nema min aure bayan na kammala phD dina. A yanzu haka muna da Maryam (namesake) dinki da Sabir.
Yau ne na ji wani ‘feeling’ a zuciya ta mai tuna min da cewa nima namiji ne KAMAR SAURAN MAZA. Wadanda ke da buri a rayuwa, da kuma ‘hope’ (fatan) cikar burin nasu. Shin za ki tallafe ni Mairo? Ki auri tsoho in his fourteeth?”
Hawaye na gudu a kundukukinta, ta ce.
“Uncle Junaidu idan ka kira kanka ‘tsoho’ ni kuma na kira kaina me? Tsohuwa?? (second hand)? Ka bazawara…???”
Ya yi saurin kai hannu ya toshe mata baki ba tareda yayi niyyar hakan ba. Da sauri kuma ya dauke hannunsa…
“Ni har gobe a Maironki na sanki, koda kuwa ace ke kika haife B.U.K baki dayanta……”
“Idan haka ne, ni ma har gobe a Uncle Junaidu na sanka, bana son kara jin wannan kalmar ta fito daga bakinka ‘tsoho’.
Ya yi murmushi, ya ce.
“Da dai ana sakewa tuwo suna ne Mairo…”
Ta ce
“Ni ma ban ce a sake masa ba, a barshi a tuwonsa, don haka zauna a Uncle Junaidunka ba V.C Junaid ba, na zauna a Mairona…….”.
Suka bi junansu da kallo, kallon yarda, so da kauna da aminci. Gaskiyar masu iya magana da suka ce, ‘Soyayya ba ta tsufa, sai dai msoyan su tsufa’. Don haka sai mu bi JUNAID da MAIRO da fatan ALHERI.
Alhaji Abdurarhaman ne ke zarya tsakanin falonshi da falon Haj. Aisha yana duba agogon hannunshi, yana kuma azalzalarta kan ta yi sauri ta shirya jirgi ya kusa tashi, wanda zai tashi dasu zuwa Kano a sanyin safiyar ta ranar litinin.
Amiru baya nan ya je China, don shigo da wasu kwanfutoci sabon shigowa, Zuwa wannan lokacin ya yarda da nadamar ‘ya’yan nasa, da cikar YAKANAH da jarumtakar Amiru. Shekaru uku kenan da rabuwar shi da Mairo ba tare da ya kara sanya ta a idanunshi ba.
Ya tattara karfin zuciyarshi ya karbi rayuwa ba Mairo, yana ganin lokaci ya yi da ya kamata yai surprising din sa, da abin da zuciyarshi ke ciwo dominta. Da abinda rayuwarshi ke muradi……… Duk wasu experiments………. da ya dora shi a kansu…… bai fadi ko daya ba!!!.
Sannan Mairo ta kammala karatunta cikin kwanciyar hankali, duk wasu burirrikan rayuwarta ta cika su, kamar yadda dan uwanta ke so. Ya kira Habibu a waya ya ce su hadu a Kanon gidan Baffa suma za su taho yanzu.
Amina ta fito daga daki cikin shiri itama ta ce,
“Daddy don Allah zan biku Kanon, ina son ganin Amir da Habib”. Ya ce “Wuce muje Amina ‘yar albarka”. (Amina mijinta ya rasu ne, a yanzu haka zaune take a gida).
Hajiya ta fito cikin shirinta, suka nufi cikin chevrolet din Daddy zuwa filin jirgi, inda suka tarar jirgin ya kusa cika, don haka suna shiga ana rufe jirgin. Ba da jimawa ba ya soma keta hazo ya lula cikin sararin samaniya.