ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Aikin marking takardun dalibai ya kacame mata, ta yi dai-dai da takardu a tsakiyar falon sanye cikin riga da wandon da basu kama jikinta ba, kanta babu kallabi, tufkar gashinta a tsakiyar kanta. Fatar nan ta kara zama fresh ta nuna mace danya sharaf, mai wadatar jini a jika, ta yadda ba za ka yi tunanin ta taba haihuwa ba.
Sassanyan kamshin ‘miyaki’ da ta dade da sani ne ya bakunci hancinta. A razane ta cira kai. Ta sake yin arba, da dan Abdurrahaman Gaya. Rungume da ‘yan biyunshi masu tsananin kama dashi.
Sai dai wannan AMIRUN ya sha banban da wanda ta bari shekaru uku a baya. Ya sirance, ya bar lallausar kasumba ta bata kyawun shi da tsarin shi, duk da haka yana nan a Amirun sa, dan gaye, mai kyau, kuma mai sanyi, wanda idaniya ba za ta taba gajiyawa da kallon shi ba.
Mikewa ta yi tsaye kamar an umarce ta da yin hakan, alama ce ta girmamawa a wajen bature. Ta rasa cikin yanayin da ta tsinci kanta tsakanin rudewa da gigicewa. Sannan wani sanyi ya tsirga a zuciyarta, ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar shi din ne, ba mai kama da shi ba.
Kafin ta yi wani action ya daga dogayen kafafunshi da sassarfa ya isa gareta, ya hada ta ita da yaran ya rungume, jikinshi in ban da kyarma ba abinda yake. Ya kankame ta ita da yaran hawayenshi na sauka a gadon bayansu. Ya ce,
“Mairo kin yi min alkawari…….. ba za ki taba barina ba, kin yi min alkawari…… we are meant for each other. Me yasa kika karya?
Kin riga kin sani kowanne numfashina yana fita ne tare da sunanki. Me yasa kika amsawa Uncle Junaidu, kika kasa jirana mu maida auren mu? Kika kasa yi min uziri? Uzurin da zan yiwa Daddy biyayya, kada ya ga rashin juriyata?
Ya ya zamu yi da ’ya’yan da Allah ya bamu bayan fidda rai da samun su? Baki yi sha’awar ki rayu tare da su ba? Ki basu tarbiyya irin taki? Jarrabawa ce Allah ya yi mana, kuma mun cinye ta da ikonsa, yanzu ne ya kamata mu karbi sakamakon mu.
Zan nemi Uncle Junaid in roke shi alfarmar ya bar min ke, ko da hakan na nufin zan durkusa masa akan gwiwoyina, don na fishi bukatarki, ‘ya’yanmu sun fishi bukatarki.
Kalle ni. Am all alone Mairo, leading a shattered life………!!!
Dukkansu basu ankara da wanzuwar mutum a falon ba, tsayin lokacin da suke rungume da juna suna kuka dukkaninsu, su suna yi ‘ya’yan na yi. Sai jin karar rufe kofa da aka yi a hankali, suka juyo dukkanninsu, babu kowa!
Amma kamshin ‘Irresistible Givenchy’ da Mairo ta ji, ya tabbatar mata da ko wane ne ya shigo, ya kuma fita, ba tare da ya yi wani motsi da zai katse su daga kololuwar duniyar shaukin soyayyar juna da kewar juna da suka fada ciki ba.
Hankalin Mairo ya tashi, ta tabbatar Uncle Junaidu ya ga Amiru, cikin halin da ita kanta ba ta san wanne ne ba. Ta zame da karfi, da gudu ta biyo bayan shi amma sai kurar motarshi da hasken fitilar motar shi ta gani.
Ta rasa ina za ta sa kanta, sai ta kifa kai cikin tafukanta ta soma kuka. La shakka maza biyu take so, ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.
Lallashi na duniya, ban baki na duniya Amiru ya yi amma Mairo ta ki ce da shi komai. Ransa ya fara baci, amma ya danne fushinsa, tunda mai nema…..baya fushi. Ya ce,
“Shi ke nan na tafi Mairo, na ba ki daga yau zuwa gobe ki yi tunani, zan je wajen Baffa daga nan zan wuce inda na yi masauki, sai gobe insha Allahu”.
Ya dauki Amir ya kama hannun Habib za su fita, ta taso da gudu ta rike rigar shi ta baya cikin kuka ta ce,
“Ina za ka kai su?”
Ya harare ta ya ce, “Gidan ubansu, tunda bakya son ubansu to suma bakya son su”.
Ta ce, “Ni na ce hakan?”
Ya yi mata kallon rahma, sannan ya ce, “Za su taya ni kwana ne”.
Ba ta yi magana ba, ta shige daki ta hado musu duk abin da za su bukata cikin karamar jaka ta ba shi. Suka ce, “Mummy bye-bye”. Ita ma ta daga hannun tana yi musu bye-bye din har suka fice daga falon.
Cikin hanzari ta dauki waya ta soma kiran nambar V.C Junaidu, bugu daya ya amsa, babu komi cikin muryarshi sai kulawa ya ce,
“Ya aka yi MARYAMA?”
Ta shafe hawaye ta ce,
“Ka fasa zuwa yin ‘dinner’ din?”
Ya yi murmushi ya runtse idonsa, tsigar jikinsa na wani irin tashi saboda KISHI. Idanunshi na tariyo mishi hoton abin da ya gani, wani image da bai taba ganin mafi muninsa a rayuwarsa ba, cikin sanyin murya ya ce,
“Na zo na tarar kina da bako, don haka na tafi”.
A raunane ta ce,
“Ba bako bane Baban su Amir ne ya zo ganin su”.
A ranshi ya ce,
“Ka ji rainin hankali irin na ‘ya’ya mata….”. Amma a zahiri ya ce,
“Ki saurare ni, idan na gama da Baffa zan kira ki”. Ya kashe layin.
Damuwar duniya ta ishe ta, ta kuma rasa abin yi, ta shiga halin rudani. Wadannan dakarun maza, jaruman soyayya sun sanya ta a kwana. Tana neman Dina, tana neman Nabilah….. don neman shawara, tunda an ce “Aikin mai shawara baya baci”.
Ta kira wayar Nabila, ta ce, “In kina gari zan zo gobe around 11”. Ta ce,
“Ina nan amaryar uncle sai kin zo”.
8/9/21, 9:04 PM – Kawata: 87
Junaid na yin parking a harabar gidan Baffa, shima Amiru na sawo kai, suka yiwa juna kallon-kallo, bayan kowanne ya fito daga motarsa. Kwayar idon Amiru har girgiza take saboda KISHI, akwai wani feeling na kishi iri daya a zuciyar kowannen su, sai dai babu wanda ya bari nashi ya fito fili.
Da sauri Amir da dan uwansa suka balle kofa suka nufi Uncle Junaid suka rungume kafafun shi, ya russuna ya kama kowannen su da hannu daya ya dauke su, suna ta zuba mishi surutu wai Mummy tana kuka, don Abban Abuja ya taho dasu. Ya yi murmushi ya ce,
“Zamu je mu lallashi Mummy ta daina kuka”.
An ce “mai Da, wawa….. sai Amiru ya karaso a hankali, ya mikawa V.C hannu, suka yi musabaha, aka rasa wanda zai fara janye hannunsa. Dai-dai sanda Baffa ya fito, ya yi musu jagora zuwa falon ganawa da bakinsa.
Kallo daya zaka yiwa Alh. Abbas, ka san cewa shima a rikice yake, ya debo gorar ruwa da tambulan cikin firij ya baiwa kowannen su. Aka rasa mai fara sha, aka rasa mai fara magana. Har shi kansa Baffan kuwa, kafin Junaid ya yi gyaran murya cike da tausayin Baban Amir da Habib da ya ke ratsa zuciyarsa. Da ganin wannan ‘giant’ kaga wanda ke fama da dingimemiyar soyayya, wadda ta rasa madafa. Yaran sun baibaye Uncle Junaidu sun kwanta a jikinsa.
Ya ce,
“Baffa na janye niyyata ta auren Maryama! Na hakura har ga Allah na barwa Baban Amir da Habib, ina bayan Maryama ta koma dakin mijinta uban ‘ya’yanta, don samun kwanciyar hankalin kowannen mu.
Ba lallai sai na auri Mairo ba shi ne zan nuna ina kaunar ta, a’a, ni da Mairo mun wuce haka, Yaya ne da kanwarsa, alakarmu hadi ne daga Allah, ba don mu yi aure ba.
Ina son ‘yan biyu su tashi gaban uwa da ubansu……kamar yadda Maryama ta tashi gaban Innarta da Babanta, ta san dadin iyaye, tasan amfanin su. Nikuma ina bukatar addu’arku Baffa, da fatan dorewar zumunci na har abada a tsakanin mu”.
Baffa ya ce,
“Allahu Akbar! Allahu akbar!! Wannan shi ne halin GIRMA, halin ‘yan aljannah!! Da gaske ne kai da Mairo kun fi karfin soyayyah!!! Sai ‘yan uwantaka, mun gode da wannan karamci Junaidu, Allah ya biya maka bukatunka na duniya da lahira, ya kara maka daukaka, ya baka duk abinda kakeso a duniya da lahira……”.
Amiru ya cira kai ya tsura ma Junaid ido ya ce, “In aka yi hakan, ni kuma na so kaina…….”.
Junaidu ya ce,
“Ni kuma ba zan auri Mairo alhalin zuciyarta na ga tsohon mijinta ba”.
Amiru yace
“nayi rantsuwa da Allah! Mairo tayi maka son da ni bata yimin ba, na aure ta ba da son ranta ba, sai a hankali na koya mata soyayyata. Uncle Junaidu kana da matsayi mai girma a gun Mairo, wanda ni bani da shi…..”
Junaid ya rausayar da kai cikin jin wani irin frin ciki a zuciyarsa, koda wannan ya tsira ya tabbata ya isheshi rayuwar duniya, yayi murmushi ya ce,
“Kauna ce tsakanina da Mairo Amiru ba soyayyar aure ba tun daga ranar dana fara ganinta, a halin yanzu jin nauyin junanmu ya fi yawa, wanda da kyar za mu iya sakin jiki da juna mu yi rayuwar aure yadda ya kamata. Ka yarda ko kada ka yarda, kai Mairo take yiwa soyayyar aure….!”